← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 20

Sashe 1

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

💔_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*SADAUKARWA*
*HAUWA,U DAHIRU TIJJANI SHATIMA YAKASAI*

*DOGIYA*

Dukkan godiya su tabbata ga shugaban halitta annabi Muhammad (S.A.W) wan da ya hallaccine ya hallicci dukkan abin dake cikin duniya ,Ina godiya ga Allah suba hanaw wata ala Wanda ya bani baiwa da ikon kawo muku tittattafai dadama ,to ayau ma Nasake samun wata damar da Zan kawo muku kayataccen littafina me suna 💔DÉPRESSION 💔(damuwa)

*KIRKIRA*
Littafin 💔DÉPRESSION 💔kirkirarene Kuma littafin 💔 DEPRESSION 💔 yafarune agaske ba hasashe bane Ina fatan ga duk wadda ta sani damar karanta littafin ta Yi amfani da abin da littafin ya fadakar akai.

*NOTE*

Littafin depression ya kunshi abubuwa da dama' kamar yadda yarinyar da ke cikin Book d'in ta kasance da ita da d'an uwanta 'yar uwa kada ki Bari abaki labarin wanan kayataccen littafin domin idan kika Bari Aka baki labari za a barki a baya .

*GARGAD'I*
Ban amince wani ko wata ya samu damar karanta min book ta hanyar yimin audio batare da neman amincewa ta ba ,dukkan Wanda ya karanta min shi audio batare da yasanar Dani ba zanyi Shari a dashi domin abimin hakkina.

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK one*

*Chapter 1*

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*✍️

A Guje ya Tura hancin motar cikin asbitin Har haki yake hajan bud'e motar da yake ciki, batare da ya kula da mutanen da ke zaune a gurin ba ya fito daga ciki ya bude gidan Bata ya sa kansa ciki, hannu n'a ga ya sa ya dakko wata kekkewar matashiya daga ita sai daurin kirji, gashin kan ta kuwa duk ya lullube Mata fuska baka iya tan tance ya yanayin kamannin ta duke.

A kafa d'arsa ya dorata yayi cikin asbitin da sauri ,Yana shiga ya shiga Kiran doctor's din asbitin "doctor! Doctor!! Likita ku taimake Ni" Bai karasa fad'ar abin da zai sake cewa ba sai ga likitocin sun fito cikin tashin hankali suka Kar'be ta tare da d'orata a kan gadon majina ta Tura ta suka shigayi juya dakin da zasu mar bi haihuwar ta,ina kafin su karasa Shiga da ita taruga da ta cika, allah ya karbi rayuwar ta, a tsora ce macen ta kalli doctor Tace "mun rasa ta ta cika doctor" "innalillahi wa'inna ilaihirraju un Kinga Kuma cikinta Yana motsi da alama yaron be mutu ba" "tabbas hakane doctor to yanzu ya za muyi?" "Dakko kayan aiki maza a shiga da ita d'akin tiyata" ba bu wani sauran Bata lokaci sukayi gaggawar Shiga da ita Aka Soma mata aiki ,cikin nasara da taima kon ubangiji sukayi sa,a yarinyar Bata mutu ba, Dan Haka suka dinke inda suka yanka sannan likitan ta dauki jaririyar domin ta gyra ta, shikuma likitan cike da rashin kwarin gywar Mai zai sanarwa wan da ya kawo ta ya fita harabar asbitin, anan ya same shi a tsaye ya Kai ya dawo ya Kai ya dawo duk ya fita a hayyacin sa saï gumi yake, hago fitowar doctor da yayi ne yasa ya karasa gurin da sauri yace "doctor ya jikin bata?" Shiru doctor yayi Yana kallon sa cike da tausa yawa yace "saï dai kayi hakuri amma munkasa cetar rayuwar ta, Wan da yayi sanadiyyar zuwan ta duniya ya karbi abarsa kayi hakuri" "hannu yasaka ya goge kwalla da tacika Masa Ido bakinsa harrawa yake wajen cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un! "Innalillahi wa'inna ilaihirraju un !! Doctor cikin dake jikina ta fa?" "Tun kafin ta harfeshi ta rasu sai dai munyi ko Karin yimata aiki mun Ciro yarinyar mace" idon sa ya runtse tare da sakin murmushin karfin hali yace "Allah Mai d'aukewa da bayarwa ,sai gashi ya dauke min fateema ya bani wata yarinyar duk a lokaci daya ,Allah yaraya ta yanzu doctor ya za ayi natafi gida da gawar?" Kar ka damu Bari mu salla meka amma kafin nan ka kirawo iyayen ta su zo Naga Kai daya baza ka iya ba ko" "a,a doctor fateema Bata da kowa anan Ni kadai ne gatan ta Haka nima bani da kowa a wannan garin sai dai ita uwar gidana abokiyar zaman fateema" "okay tom shikkenan Babu matsala zaka iya shiga sai mu taimaka maka zuwa gida" "tom shikkenan doctor na gode sosai".

Kamar yadda duniya take juya rayuwa take karewa lokaci yake Kara kurewa numfashin mu na dad'a karewa gudun zuciyar mu na sauri ,Haka itama fateema ta tsinci kanta a yau domin a yaune tayi fatan ta na karshe kafin ta bar duniya, alokacin da ciwan zuciyar ta ya tashi zainab ce zaune a gefan ta tana famar hura hanci tana kallonta ,cikin Ido da Ido fateema take kallon ta tana cewa "Zainab wannan ciwan nawa na fahimci ba na tashi bane sannan ga zaidu Nan ba shi da wani shekaru masu yawa balle ya iya kula da rayuwar abin da Zan Haifa ,bana da kowa a adamawa kowa nawa Yana kasar faransa bansan a duniyar da suke ba ayanzu da ace Ina da tabbacin zanyi tsawan Rai a duniya tabbas da na roki wata alfarma a gurin ki Amma Ina nasan hakan bazai yuwu ba, Zan fad'a Maki wani abu wan da Baki taba Sani ba a tattere Dani, Ni din tauraruwace a nahiyar mu sannan Ni ba talaka bace mahaifina hakshakin Mai kudi ne mahaifiyata kuma jinin sarautar jamani kaf family Dina suna zaunene a faransa dan Allah ki taimaka ko bayan Raina ki bawa yarana wannan a kwatin domin su nemi dangina"fateema ta d'akko wata 'yar k'aramar akwati Mai sanye da wani dutsuna guda goma Sha saya sai Kelli suke a kowanne dutse a kwai number guda daya, "to fateema wannan menake gani kamar gold?" "Ba tantama kike ba gold sai sai an yisu ne da numbobin mahaifina ta nanne kawai Zaki iya t'ai makawa su zaidu wajan Samo dangin mahaifiyar su, n'a rokeki ki taimaka ki rikesu kada ki Bari rayuwar su ta wula kanta" bakin zainab Har rawa yake wajen cewa "insha Allahu Zan rike muki amana" ta fad'a tana watsa mata harara ta gefan fuskar ta, wata uwar Kara fateema ta saka hakan yasa zainab tsorata ta kwallawa malan Kira da sauri ya karaso ya dauketa sai parking space ,a mota ta sata ya rufe sannan ya fita zuwa asbiti.

Wannan shine a bin da ya faru kafin zuwan su asbiti .

Tun da doctor ya taimaka Masa suka kawo gawar fateema gida zainab tashiga ihu da kururuwar karya har da Suma, Wai ita ala Dole asai tana sonta, shikuwa zaidu dayake a lokacin shekarar sa hudu bai San komai ba saï dai shima yasoma kuka ganin yadda yaga mahaifinsa na kuka" sumayya da munira wadan da suka kasance Sune manyan yaran malan suna zaune Suma sai kuka suke na karya Dan duk kansu mahaifiyar su ta koya musu bakin hali.

Abu kamar Wasa malan Yana ji Yana gani akayi wa fateema wanka Aka sallaceta sannan Aka huce da ita gidan ta n'a gaskiya,gidan da duk wani mumini da ma Wan da suka kasance ba musulmai ba suma sai sun jeshi Allah yasa mudace muyi kekkewan karshe Ameen.
Chapter 1 · 0% Book details