← Book details Bangon Duniya 1 To Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 20

Sashe 11

Bangon Duniya 1 To Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

#BANGON DUNIYA PART #3A Lokacinda yaro Kairuf yatsinci kansa atsakiyar makamakan dodanninnan sai yakwarara ihu yakama jada baya Sai shugaban wayannan dodannin yaceda Kairuf yakai Kairuf kakwantarda hankalinka lallai mubaxa mucutarda kaiba kawai xaka xaunane ataredamu domin baka kariya kada Axxaluman duniya sucutarda kai, Kairuf yace aa lallai bani kukesoba so kuke kukarbe Sarkan dake wuyata kuma baxan bakuba Dodo yafusata yadakama Kairuf tsawa yace tokuwa xaka mutu domin duk duniya babu wanda ya isa yadakatardamu ga Karban Sarkan Ajali agareka Dodo yadakama wani dodo tsaya yace kai Sairud maxa kasa takobi kasare kan yaronnan kadaukomin Sarkan Ajali Dodo yaxare takobi yadaga daniyyar Sarekan Yaro kairuf saura kiriss takobin yasauka awuyan Yaro Kairuf, Sai wata Kibiya tafasa kirjin Dodon tsananin Karfin sukan Kibiyar saida Dodan yai Sama sannan ya fado matacce koshurawa baiyiba dankari Dodannin sukakwarara ihu sukama waige waige amma basuga kowaba Kwatsam sai akwarara ihu saiga Tawagar dakarun xumunci sugoma Shabiyu a sukwane akan dawakai afusace Dodannin suka tunkaresusuna ihu, Dakarun xumunci Suka xare takubba akafara dauki badadi kayya fashi bannan,aiki kowa yagajji bai sababa domin haka dakarun xumunci ke sassabe kawunan dodanninnan kamar karya Jaruma Miraa tarika gunji tana Farke cikin dodannin gamida datse kawunanansu Sadauki marwan ya addabi dodannin da sara da Suka kamar marnan iska haka Dakarun Xumunci suke kashe Dodannin Inda Gimbiya Ela tarika xarya tana tsagesu gamida datse kafafuwansu dodannin sukarika kaisara dasuka afusace amma sai yakasance abanxa Domin akowani lokaci su,ake kashhewa Inda Boka Barnuhu yakafa yatsare awajdaya yana yakar Dodannin dakofofin tsafi inda yarika babbakesu da wata koriyar wuta maitsananin kuna dakarun xumunci sutakura dodanninn sukuntatasu suka toshemusu duk wata kofa tatsira surika turasu kiyama bashiri,ai kafin kace haka sunkarar dasu bakidaya Yaro Kairuf yakarema Dakarun xumunci kallo sai yayunkura xai futa aguje tuni Dakarun xumunci sukewayeshi suka rika xagayeshi da dokunansu Kairuf yakwala ihu yacekai kusuwaye kuntaimakeni yanxukuma kuna niyyar cutardani Boka Barnuhu yace kai yaro kanatsu mune Dakarun xumunci masu burin Samama Duniya Sauki Kairuf yace kenan Kune xakuimin rakiya xuwa bangon Duniya boka Barnuhu yace mune Kairuf yace gaku manya sannan kunkware afilin daga meyasa baxaku karbi Sarkan ajali kukaita Bangon duniyaba dakanku, Boka Barnuhuyace domin sarkan ahannunkane kawai xata xauna lafiya amma duk wanda yarike Sarkan sabanin kai to baxaiyi kwana biyu arayaba domin Masuson mallakan Sarkan sune ajalinsa Yaro Kairuf yace tome yasa Sainine Sarkan xata xauna ahannuna Boka Barnuhu yace Wannan kaddarace daga ubangijinka Kairuf yabude baki xaikara tambaya Boka Barnuhu yadakama Kairuf tsawa yace Kai yaro babu lokacin tambaya kuma babu lokacin amsata maxa kakama Hanyarka natafiya Bangun Duniya atsorace yaron yakama tafiya da kafarsa gunin ban tausayi Gimbiya Eela tadubi boka Barnuhu tace meyasa baxamutafi tareda yaro Kairuf ba Boka yace aa dole shikadaine xaitafi mukawai xamu kasancenne masu kubutardashi aduk lokacinda axxalumai sukamashi, Sarki Lukman yace to menene illar tafiya taredashi Boka yace mutukar muna taredashi tafiyar baxatai sauriba domin Axxaluman sarakuna daga jinsin mutun da aljan xasu matsamana damiyagun hare hare wanda hakann xai sa nubata lokaci wajen maida musu da martani amma shi yaro kairuf yakasancene maitsanain Sa,a,da shashatau aduk lokacinda wata halitta tatsareshi daniyyar cutardashi to wata halittarce xataxo tataimakeshi daganan Dakarun Xumunci suka tsunduma cikintaya subi bayan Kairu asukwane koda sukai tafiya mainisa Sai mamaki yakamasu domin axatonsu xasu riski Kairuf ahanya domin shi yana tafene akasa Sukuma suna bisa Dawakai amma sai suga bashi ba,alamansa Sarauniya Atine yarmama Kura mai ajalin Garke tadubi Boka barnuhu tace yakai babban Boka ya,akai bamuga yaroKairuf ba alhali akasa yake tafe Kodajin wannan tambaya sai Barnuhu ya bushedadariya yace lallaikisani mutukar Sarkan Ajali natareda Kairuf to tafiyarsa ta uni daya yanadaidaine da tafiyar ingarman doki na tsawon kwanaki uku kuma baxai taba gajiyaba abu ukune xasu rika tsaidashi Yunwa barci Sai bayan gida dankari aisai Sukaci gabada Tafiya ,acan kuma kauyan su kairuf bayan Sarki Kaushatu da jama,arsa summa kauyan dirar mikiya Suka binkice kauya cikinsa da bayansa basuga Kairufba Sai Sarki Kaushatu yakwarara Ihu yadauko wani madubin tsafi yakama ambaton kalaman Surkulle gamida tsatsuba yashafi Madubin Tsafin aisai Ga Kairuf natafiya adokardaji shikadai Sarki Kaushatu yakwarma,ihu yace maxaje mushirya, yaro yatunkari bakar Sahara lallai muhanxarta kada mubarshi yakai ga bakar Sahara domin akwai Bakar aljana da rundunanta Sunuyi kwanto suna jiransa yakariso garesu sukameshi aiSai runduna tai kudu asukwane yawansu yawuce irga kai inka gansu Saika dauka Dakarun Duniyane mutane da aljannu Sukaiyo ayari DANKARI NIKAM NAYI RUMFARRRRR ;;#BANGON;;#DUNIYA;;#3B Kairuf yarika ketagudu asararin Sahara dukda baisan abinda xaitarar agababa kwatakwata bayajin tsoron komai saida yakwashe Samada Makwanni uku yanaratsa Saharannan batareda yaga iyakantaba watarana daga cikin ranekun tafiyarsa sai yaunwa takamashi kishin ruwa ya addabeshi yafara tagayyara neman ruwa yake ido rufe tsananin jinkishida Kairuf yakeyi har gixo,ruwa yakemasa kawai saiyarika ganin korama agabansa sai yanufi gurin Sai yaga tarin yashine ahakadai yaci gabada tafiya kwatsam sai yaga watarijiya maidan karan kyau abin mamaki ga mutane abakin rijiyar sunata diban ruwa yawan jama,andake gurin tamkar anacin kasuwa kawai Sai Kairuf yanufi gurin domin yasha ruwa kaisai wani tunani yafado aransa yace kai nifa nakasance abin Farautane ga Mutaneda,aljannu kadafa mutanennan yaxamanto tarko sukadana min sai yainaxarin jama,ar gurin yaga bakidaya jama,an dake bakin rijiyar Idansu na kansa Take Yaro Kairuf yatuna dakalaman mahaifinsa alokacinda yake koyamasa Karatu daga littafi Sarrafa rayuwa domin karekai daga abokan gaba mahaifinsa kecemasa kasani yakai dana samun ruwa asahara abune mai matukar wahala sannan idan kasamu to kainaxarin kafin katunkari ruwa domin xai iyakasancewa akwai makiya abaya domin gamawa da rayuwarka Sannan yace kasani yarona duk lokacinda kaga wata hallita ta yawaita kallonka tolallae kaikokarin nisanta daga gareka domin Xata,iya cutardakai ai Kairuf nagama wannan tunani sai yaji yakoshi kishin ruwanda yakeji yagushe yaji wani Sabon karfi yashigeshi dankari aisai yafuta agujee tamkar Futan kibiya wohoho aibakidaya jama,arda Bakin rijiyarnan sai sukai Girgixa suka rikida sukoma wasu bakaken aljannu masu tsananin muni sunada bindi kamar birai Sugaban aljannun Sarauniyar bakaken aljannu masubindi Za,uma takwarara ihu taceda jama,arta kai tsinannu abin harinmu yagane shirimmu kada kubari yakai Labari lallai kukamaminshi aisai aljannu sukabi Kairuf da masifan gudu nanfa sukasa tsere naban mamaki domin gudune maitaken gudun mutuwa aljannun sukurema Kairuf gudu sunaneman kamashi amma abin yagagara domin sai sunzo dafdadafamma sai yabace musu saidai suhangeshi candanisa yana tsallake duwatsuda koramu komai girman Rami indai Kairuf yadaka tsalle tofa sadai kahangeshi yakai daya ballin yada futa aguje suma aljannun babayaba domin sunkasancene suna gudu dafdadaf Koda Sarauniya Za,uma taga wankin hula xaikai jama,arta dare sai tadauki wani katon dutse ya seta bayan Kairuf tacilla dutsen aaune dutsen yaje yakifardashi Kairuf yakwalla kara yabaje a yashin Sahara Runudunan bakaken aljannu masu bindi sukai dafifi akansa alokacinne Sarauniya Za,uma tadiro daga sama takalli yaro kairuftakeceda dariya tace kai shu,umin yaro lallai yaxamamaka wajibi kaxauna taredani tsawo kwanaki talatiKairuf yamike yafara jada baya Sarauniya Xa,uma tamika hannu xatadamkeshe sai akwatsatsa wata tsawa mai raxanarwa tilas tafasa Shirinta takama xaxxare idanu itada Jama,arta dankari aisai gagayyan dakarun Sarki Kaushatu dankan,ana sundurfafo inda yaro Kairuf ketsaye Sarauniya xu,ma tai ihu dakarunta sukai Sahu inda suma Dakarun Sarki Kaushatu suka jadaga afara hararan juna can sai Sarki Kaushatu yabayyana yadakama Za,uma tsawa yace ke yarinya lallai kadaki kuskura kitabi yaronnan domin keda dakarunki xaku hallaka Sarauniya Xa,uma tabusheda dariya akarketadakama Sarki Kaushatu tsawa tace kai wawa lallai sharafar mutuwa nadibanka lallai kasani nina wuce Saninka kuma naxarce tunaninka lallai babu wani abuda xai hanani tafiya da yaro Kairuf ruwa da iska Mutun da aljan Koda yaro kairufyaji ana misayen yawu akansa sai yakwalla ihu yace kai bakaken Shaidanu badai nikukeso ku mallakabato nima nayarda xan xauna ahannun daya daga cikinku amma bayan kun gwabxa yaki atsakaninku domin asan waye xaiyi nasara kumawaye xaifadi Karuf yadaga murya yace xankoma gefe inga yanda xata kaya tabbas wanda yainasara xantafi taredashi Aisai Sarki Kaushatu yabusheda dariya yace dakyau yaro inasom hatsabibin mutu tundaka hada bala,i maxa koma gefe guda kaikallo Kairuf yakoma gefe yahaye bisa wani tsohon kwaure yaxauna Sarauniya Xa,uma takalleshi tace dakyau yaro kajirani Ingamada tsinannun nan dake gabana taima jama,arta tsawa Sukai ruri sukaikan Dakarun Sarki Kaushatu sumasuka fasa kururu suka afkamusu take yaki yakullu masifa tawanxo wohoho ai sai Bakaken aljannu sukarika yagalgala Dakarun Sarki Kaushatu kamar baranan iska haka suke Fatalidasu suna turasu kiyama Kaiya Sarki Kaushatu yafusata yakwararaihu yabuso wata mahaukaciyar iska take iska tarika sunkutan bakaken aljannu tana juyi dasu asama tana kakkaryasu hankalin Xa,uma yatashi tasabi karonto wasu kalaman Surkulle take iskan taya cakJama,arta sudawo kasa amma dayawa sun mace ranta yabaci takwarma ihu sannan tafidda wani garin magani tawatsa sama gamida ambaton wasu kalaman surkulle garin maganin yaxama hayaki yaratsa Sansanin Sarki Kaushatu kayya tsafigaskiyar maishi asai ga jama,ar sarki Kaushatu na kumbura suna fashewa damm kamar tsiya haka sukarinka fashewa namfa afara asaran Maxaje mutane da aljannu Sarki kaushatu yakwarma ihu yasabi karanto dala musan tsafi take wata iska mai Sanyi yatsa sansanin Jama,arsa tuni sukadaina fashewa ammafa dakarunsa sunmace da yawa kamar igiya yamika ahannu xararara yadamko Xa,uma yadagata sama yamaka dakasa yadaga takobi xai Datse kanta saita bace bat Kawai sai yadamko acikin Iska take yashako Wuyanta tabayyana idanunta sunyi Jajaju saboda xafin Shaka Dakarunta sukwarma ihu sukayo Kan Sarki kaushatu yanunasu da yatsa ta ke suka kafe acikin Kasa TOFA#BANGON;;#DUNIYA;;PART (#3B) Lokacin da Sarki Kaushatu yashakeSarauniya Za,uma idanunta sukai Jajur nunfashinta yafara daukewa ai sai Dakarunta sukakwarma ihu suka Zare takubba suka tunkaro Sarki Kaushatu afusace Sai Sarki Kaushatu yanunasu da sandar tsafi tareda ambato wasu kalaman Surkulle take kasa taburma dasu tashanyesu iya Kugu Sarki Kaushatu yabusheda dariya yaceda Za,uma yanxunnan xan sanya wuta takone jama,arki agaban idanunki sai yadaki kasa dakafarsa take wata shu,umar wuta tabayyana tatunkari Dakarun Sarauniya Xa,uma wadanda suke kafe akasa nanfa sufara ihu dakururuwan neman ceto koda Sarauniya Za,uma tatabbatar intai sakaci jama,arta xasu hallaka sai taikururuwa taceda Sarki Kaushatu kai sarkin Sarakai natuba nabika lallai nida jama,ata xamu xamo bayinka nahar,abada Sarki Kaushatu yabushe dadariya yace wane yaro kuma wane uban yaro yanuna wutarnan da Sandar tsafinsa take wutartamutu kasar tasaki dakarun Za,uma bakidaya sukai mubaya,aga Sarki Kaushatu dankan,ana jikan Sarki Kurungu mugun kifi kada naganainka yakwanada yunwa koda Sarki Kaushatu yainasara akan Sarauniya Xa,uma da jama,arta sai yakalli yaro kairuf yace,To yaro nine nakasance mai gala saboda haka xaka xauna ahannu tsawon kwanaki talatin afadata
Chapter 11 · 0% Book details