← Book details Banana Island Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 33

Sashe 3

Banana Island Complete Hausa Novel · about 5 min read

ba kuma,sake biyosa tayi da gudu saidai nunata kawai yayi da yatsa taja cakk ta tsaya,har ya wuce bata iya motsawa ba. Yina fitowa ofar falon jirgine ke tsaye an Rubuta ADNAN 3. Pilot in jirgin ,sojan samane ri e da bindiga ,yina ganin ya fito yayi maza ya kar i brief case in hannunsa yina gaishesa ,bai magana ba ya mi a masa hannu sukayi musabiha ya shige jirgin ,filfilan helicopter ta waina ta lula cikin gajimare.?? Mohammadul_Adnan kenan,Shahararren matu in jirgi na asa da asa ,sa annan kuma shugaban kamfanin era motoci da ananun helicopter na A&D. Matashin billoniya mai kimanin darajar ku i Dala tiriliyon bakwai . **** Uni lag. Female hostel Room 4 "Ifty 8 on dot" matashiyar da ke zaune gaban Laptop a falon ta walla kiran iftyn tana kallon wani ofa dake hagu da inda take zaune . "Wayyo gani nan sisto..." zazza ar murya ta bata amsa daga ciki.kafin ta falfalo da gudu rungume da file in takardu mai tsananin kyau sai wayoyin hannunta guda biyu duk kamfanin iPhone Wanda kowani aya zai kai ku i 700k Zuwa gefen kujeran da Aalima take tayi ta an ha e gefe da gefen kumatunsu ta sakin mata sautin kiss "Umuhhh...I'm going..."(Na tafi) Ta are maganar tana fashewa da dariya har saida kyawawan dimple dinta suka lollo a a gefen kuncinta . Subhanallh! tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya era kyakyawar halitta kamar Iftihal_khair. Kyakyawar dirarriyar bafullatana ce mai auke da kala mai tsada wato chocolate colour , sai yali fatar takeyi irin na hutu da jin da i ,saye cikin doguwar riga Maroon mai azaban kyau yasha adon duwatsu ba e don haka cover in takalminta ,agogon iWatch in ta suka kasance ba Aalima jinjina mata kai tayi "Ok ga car key ina ki je a ciki" ara daka tsalle tayi ta rungumeta "awwwwn kina sona fa da yawa li_li... Bye" auki makullin motar a kan table in karatunsu ta fice da sauri . A gaban premises in Hostel in motocin alibai ne reras kyawawan mata masu lekcan safe sai wucewa suke a kafa wanda ajujuwansu ke nesa da Hostel suna zaro motarsu a inda suka saba adanawa suna ficewa . Iftihal ma haka tabi sahun sauran aliban ta je ashin wata bishiyar dalbejiya ta fiddo motar Aalima in _Marcedes C320_ ba a wuluk tayi masa key ta fice da gudun gaske saboda har 8.15 am tayi Tazo giftawa ta wajen department in su wasu rukunin an mata su hudu na tsaye da lekcaransu Sir Dauda ,suna ganin ta dumfarosu suka bushe da dariya suna nuna motar da take ciki "Malam gafa mutuniyarka ko ina zata je oho " zarrr yabi motar da ido har saida yayi nasarar lalubo ganinta ta saukakken glass in motar . Sosai Iftihal ta tsargu don tasan gang in su Fari'at basu da Alkhairi ,bare taji labarin jiya malam Dauda yazo kiranta a aji bataje ba,don haka da sauri ta ara ma motar wuta fuuuu ta wuce. Wani sassanyar Ajiyar zuciyar sir. Dauda ya ajiye "Gaskiya yau tafi ko yaushe ha uwa " "Mtseww malam duk kayan Aro ne fa ,wallahi daidai da wayoyin da kake ganin tana fafa dasu na Aalima ce ka ganta ar matsiyata ne na gaske don inajin ana binta bashin kudin makaranta na shekaru uku kenan...yawwa misali baka ganta ba a ba ? Ka na ganin an masu kudi bakake ? Sai an wahalalu masu dambe da kwanon tuwo" Aikuwa suka doka shewa suka yace da dariya Dafe baki malam Dauda yayi "Aihooo ai na aza ar masu dashi ne ,ina binta tana Gara Ni ,Kinga da ta kwantar da hankali da ko kudin makarantar ne ban biya mata ba..."? Tsaki Salma tayi "Mtseww baka dandan ara mata carry over bane,Dama naga kanta na fizga ana kiranta da _brain box_ tana yinma mutane kallon hadarin kaji ...amma tana ganin ruwan carry over zata daina bin ta rich kids I bet u" Tunda Ifty ta isa maha an Victoria Island ba abunda kake iya hange sai Dogon ginin gilas da gilas in A&D group of companies ,shi ka ai kake hangowa wanda tsayinsa ya shiga har cikin jido, benene mai nisan gaske an lullu eshi gaba aya da gilasai masu ruwan sararin samaniya. A gaban kamfanin ta faka motarta da taga ya zama tsohon yayi cikin lafta laftan motocin da suke wajen. Fitowa tayi hannunta ri e da file tana arewa dogon ginin kallo amma ta kasa irga benen hawa nawane ma,sosai ta zama auye makuwa yina neman kamata,aro mazantaka tayi ta daidaita natsuwarta sannan ta iya shiga Companyn ,tasha tambayoyi da bincike kafin a barta ta isa floor in da ofishin ADNAN yake saida aka amshe komai na hannunta daga ita sai jotter da waya guda aya,sannan ta sadu da secrataries in sa su biyu Kince shine ya Baki verbal appointment yace kizo yau ko? jinjina masu kai tayi saboda tasan tana bu e baki za'a gane arya tayi,rubutu sukayi a jikin computocin gabansu suka tura masa sa on zuwan Ifty,da cewan da tayi shi yace tazo Mamakine ya kamasa don shi bai baiwa kowacce mace appointment din ganawa dashi yau ba. Da har zaice a koreta Kuma sai yace a barta ta shigo Na'uran tantance mutum aka auko aka kara mata a jiki ,da sauri ta daga hannunta sama baiyi ara ba wannan ya tabbatar masu da bata unso komai na sharri ba don haka ,PA insa wacce ta kasance baturiya ta tasa ta har gaban office in sa. Office ne sunan office ne amma ba'a yi shi da bulo koda guda aya ba,zallan frame work ne na gilasai a angarorin ginin guda hu u wanda na ciki yake ganin komai dake gudana amma shi ba'a ganinsa . Ifty ana bata izinin shiga kawai ta sa arfi ma ofar da nufin ta tura ta shiga,saidai naurane yayi magana da turanci wanda ya sata firgita ,kawai ofar ya bu e siyyyy .kamar wanda aka hanka o sai gata kif ta kife a asa. Adnan dake tsaye jikin window yina kallon yanda gajimare ke gudu a sararin samaniya har yana an dakan gilas in windown sa wani zubin ,hannunsa ri e da cup in coffee ,bazato yaji fa in wani abu mai nauyi gamida arar mace Cikin karsashi ya waigo ganin ta watse a asa yasa yayi saurin zuwa ya kamo hannunta ya mi ar da ita tsaye ,da wani kalar murya na kamilallun maza mai kama da ra a yace mata
Chapter 3 · 0% Book details