← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 8 OF 60

Sashe 8

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 8 min read

"Ke Mimi tashe ta kuzo rumfar Umma ina Neman Ku." Yafad'a cikin daga murya. Futa yayi ita kuma tafara tashi na, tsaki ns buga ina kara gyara kwanciya ta, tace"Nasan dai kina ji tom Ya Aminu ne kin san dai halinsa.
Nace"Kije ke ni kam babu inda zani." Mik'ewa tayi tana fadin "Taurin kanki ne yake jawo miki komai.

Ina jinta ta futa, minti biyu na mike nima domin tsoro ne ya shige nasan halin Ya Aminu bai k'i ya shigo ya dake ni da sanyi safiyar nan ba.

Ina shiga dakin Umma na yadda Aunt Hauwa har tazo suna ta mai da magana, zama nayi gefan ta muka gaisa hannun Islam na jawo INA fadin " Baki je makaranta ba yau."? Aunt ta kalle ni tana nazari tace"Ke kuma waye ya fasa miki gefan fuska." Kwallah ce ta taru a idona nayi shiru hade da sunkuyar da kaina.

Yaya Aminu yace." Nine nan! Na fasa mata idan kuma tayi min gaddams kan abunda zan tambaye ta yanzu to bakinta zan fasa mata har sai hakori ya futa." Kallonsa nayi cike da rashin tsoro, cikin tsawa yace." Ki fada min a ina kika samo wannan tafkekiyar wayar me uban tsada kin San kuwa kud'inta,? Nasan wayar taki ce, Mimi ta rufa miki asiri ne kawai kamar yanda ta saba." Mimi na kalla dake wasa da hannunwan ta nace"Abunda kike zo kika CE musu kenan."? Da Jan ido ta kalle ni, nace"Kiji tsoron Allah Mimi." Murya na rawa tace"Umma me nace tunda Nazo gurin nan." Umma tace"Baki ce komai ba zargi take." Ya Aminu na kalla fuska a hade nace" Waya ta Mimi ce don haka ita zaka tuhuma bani ba, yanda ka ganta nima haka na ganta. "

*4/November/2019*
[11/4, 5:49 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*Mallakar_BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*

*40*

Yaya Aminu ya kalli Mimi cike da mamaki domin bai tab'a tsammanin faruwan hakan daga gurin ta ba, a nutse yace." Hakane Mimi."? Gyda kanta tayi tana k'ara sunkuyar da kai kasa, aunt Hauwa tayi karaf tana fad'in"dama baku San da wayar a hannunta ba."? Umma tace"Bamu sani ba Wallahi sai yau" aunt tace"To ai ko lokacin da suka je gidana da wayar a hannunta yau kwanansu Uku kenan." Umma ts tsare Mimi da kallon tuhuma tana fad'in" Ki fada min gaskiya Mimi wannan wayar ta wacece tsakanin ke da Asma'u. "Mimi tace" Wallahi Umma tawa Ce." Tace" waye ya baki ita." Shiru tayi, da k'arfi Ya Aminu yace." Ba tambayar ki ake ba."

Cikin inda-inda tace"Amjadu ne." Dukaninsu jikinsu yayi sanyi Mussaman Aminu Umma tace"Kina nufin yaron nan mai company ko me."? Aunt tace"K'warai kuwa Umma wai sonta yake yi shine ya bata waya." Umma tace" Ni abunda na kasa fahimta a nan shine, shin da ke da ita Asma'u wa yake so a cikin Ku? Ke ya baki waya mai tsada ita kuma ya bata KUDI da kaya dukanin Ku akwai alamun tambaya a tare daku."

Aunt tace"Shine maganar wallahi nima kaina ya kulle sosai." Hannu Ya Aminu ya mik'a tare da fad'in"Bani wayar." Mimi ta mik'a masa wayar jikinta a sanyaye . tashi yayi ya futa ranshi a mugun b'ace!

*********
Yinin ranan haka yayi shi babu dad'i ko da suka futa da Anthony ma shi kad'ai ya dinga zurga-zurgar sa, sai sa komai ya kammala sannan suka dawo gida.

Wanka kwai yayi ya futo parlor inda Anthony yake zaune yana aiki da loptol firji ya nufa ya dauko ruwa na gora ma sanyi tsiya yazo ya zauna kan kujera hade da bud'e ruwan ya fara tuttulawa cikinsa.
[11/4, 5:34 PM] .: Ko da wasa bai kara kallon pictures din nan ba, yana ganin idan ya k'ara kallonsu zai iya had'iyar zuciya ya mutu. Wayar shi ya bude hade da bude data ya shiga whatsp yana dubawa, Alina ya ga ta turo masa da pictures, domin kwana biyu baya d'aukar wayarta ko ta kira, ko wancan karon ma da yaje birthday din ta cin sa'a tayi.
Yana bude wa gaban shi Yayi wani irin bugawa ganin da yayi Asma'u tsakiyar 'yan iskan abokan Alina sunyi hoto*innalillahi wa'inna ilahi rajun* shine abunda ya furta ya mik'a zaune sosai zufa!! Na keto masa hotonan yake dubawa sosai lallai yarinyar tayi nisa, shi a ganinshi kamar jarabar ta ce ta sanya take shiga cikin maza ko zata rage wa kanta damuwa amma idan ba haka ba mace d'iyar Hausa Fulani tayi irin wannan d'inki Wanda dashi babu maraba da tsirara ta dinga keta maza, lokaci guda yaji zuciyarsa tana wani zafi tare da muguwar tsanar yarinyar, gani yake shine ya cuci kansa kwanaki baya da ta kawo masa kanta har gida, da ya sani ya biyawa kansa bukata tunda ita bata tausayin kanta.

Pictures da Mimi ta turo masa yake dubawa, du Rabin su ita da Asma'u ne sai wannan budurwar da ya tab'a ganinsu tare wato Munnu, kayansu iri d'aya haka ma Dinkin su iri daya to wai me yasa d'inki a jikin Asma'u yafi nuna tsaraci. Shi kadai yake WANNAN tunanin, wata zuciyar tace masa ai duk tafi su ciki ta ko wane fanni.. Fuskarta yake kallo kamar zai lashe ta, har kara zomming din pic din yayi dai-dai ita yana kare mata kallo, ajiyar zuciya ya sauke tare da fadin"Zaki gane Baki D's wayo yarinya, wani pic din ya bude ,sai da wayar ta kusa fad'uwa daga hannunsa, ganin guy nan shi da ita suna kallon juna kamar masu kallon love. Ji yayi duk duniyar tayi masa zafi, ya kalli Anthony da jan ido cikin turanci yace." Gobe zan wuce najeria Tunda komai ya kammala anan."
Anthony ya gyad'a kansa gami da cigaba da aikinsa

Mik'ewa yayi da sassarafa ya shige bedroom din, kan wata duguwar kujera ya zube hade da dafe kanshi, yana cije lips din sa tunani kawai yake wane irin hukunci ya kamata yayi wa yarinyar nan.
[11/4, 5:47 PM: *****
Kwanan bakin ciki da damuwa yayi a ranar, washe gari kuwa da wuri ya gama sallamar duk Wanda ya dace, ya bar amanar komai a hannun Anthony ya nufi k'asar sa ta gado wato Najeria.

Sha biyu dai-dai jirgin su ya sauka a filin jirgi na Malam Aminu kano, su Rambo na gefa suna ganin saukowar sa suka k'araso da sauri Rambo ya karb'i wayoyinsa shi kuma doh-doh ya karb'i 'yar jakar sa. Suka nufi mota.

Satar kallon fuskar sa suke ganin fuskar ogan nasu kamar Wanda aka aikowa masa da mutuwar iyayensa, Tunda ya shiga motar babu Wanda ya kula a cikinsu har suka isa gida. Get Man yana ta d'aga masa hannu tare da fatan alkairi ko kallonsa bai yi ba Doh-doh na gyara parking ya bude motar ya futo ba tare da ya jira rambo ya bude masa ba.

Kai tsaye ciki ya nufa suka rufa masa baya, nan parlor suka aje masa wayoyin shi hade da jakar shi, suka futa da sauri.
Yana shiga bedroom dinshi ya fada toilet Wanka yayi ya futo ko mai bai shafa ba, parlor ya futo masifa na cin sa, zama yayi hade da kiran Rambo a waya domin yaji meye labarin guy nan yana ganin ta kanshi zai fara.

*4/November/2019*
[11/5, 11:28 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*Mallakar_BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*

*41*

Rambo ya shigo cike da Ladabi yace. " Sir g... Gurin zama ya nuna masa Rambo ya zauna jikinsa a sanyaye saboda yanayin da ya ga ogan nasu ya bashi tsoro. Cikin dakakkiyar murya yace." Wannan guy ya bar garin nan ko kuwa."? Rambo yace." E to jiya da na ga gilmarsu a mota shida abokina sun wuce can Titin rimin gata, ina kyauta ta zaton can masaukin sa, yake." Mik'ewa tsaye yayi hade da goya hannunsa a baya, ya kalli Rbow da jajayen idonsa yace." Kaje kazo min dashi, nan." Rambo ya mik'e jiki na rawa ya futa daga d'akin. Shi kuma ya cigaba da kaiwa da kawo wa cikin parlor
Rambo da doh-doh sun jima a tsaye suna tattauna maganar kafin Rambo ya shiga mota ya tafi, yanda suka tsara shine baza su biyewa Ogansu ba, zasu yi masa dabara ne kawai saboda suna ganin a yanda yake kan dokin zuciya zai iya kashe guy nan kamar yanda ya fad'a.
*Amjad* yafi a wa guda a tsaye a parlor sai kace wani soja, bedroom dinshi ya nufa wayar shi ya dauko ya dawo parlor ya zauna numbar Mimi ya kira yaji wayar a kashe, ranshi a bace ya aje wayar yana tunanin ta yarda zaiyi ya gansu. Minti ashirin a tsakani ya k'ara kiran wayar kamar da wasa aka dauki wayar, Muryar Namiji yaji yana sallama.Amsawa yayi Tare da gyara zaman sa, Ya Aminu a nashi b'angaran ya gane muryar Amjadu da sauri ya gaishe shi, ya amsa babu yabo babu fallasa, yace." Yallab'ai Ashe dai yaran nan da gaske suke yi." Amjadu yace." Menene ? Aminu yayi masa bayanin yadda suka tada hankalinsu ganin wayar a hannunsu. Murmushi yayi yace." Nine na bata domin mu dunga gaisawa, Ya Aminu yace." Allah ya saka da alkairi gaskiya akwai alamun tambaya anan Yallab'ai idan banyi rashin kunya ina so in San cikinsu wacece tayi dace da samun gwarzo miji irin ka."
Kai tsaye yace." Dukaninsu nake so zan aura lokaci guda idan zaku bani." Aminu yaji gabansa ya fad'i yace." Yallab'ai a yi haka kuma."?
Murmushi yayi yace." Anyi an gama ni dai a gurina saboda haka ina so ka sanar da manya kafin in turo magaba tana a tsai da magana domin baza a ja lokaci me tsayi ba."

Yaya Aminu yace." Insha Allahu Yanda kace haka za'ayi mungode sosai da wannan karamcin." Sallama sukayi hade da kashe wayar.

********
Chapter 8 · 0% Book details