← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 56 OF 60

Sashe 56

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 5 min read

Take ya fahimci inda maganar take wato ruwan sama ne ya doki sweet heart dinsh, babu walwala a tare dashi yace." Jahid idan na fahimci maganar ka kana so kace min ruwan sama ya tab'a lafiyar baby Aysha hakane ko.'? Jahid yace." Eh mana ai na dauka ka sani kaima maganar zakai min." A kaurare yace." Inso in ce dakai ka sanya Asma'u ta mai damin yarinya gida sai naji wannan mummun labarin daga bakinka Asma'u taje ta dauko min yarinya ba tare da yadda ta ba shine dalilin kiran da nayi maka, gaskiyar magana Mujahid Dan dai Kaine ina ganin girman ka a idona amma da sai na dauki mataki kan Asma'u tunda abunda ta shirya min kenan kan wane dalili zata futa da k'aramar yarinya ruwa ya dake ta, kaga irin sakacin da nake fada maka ko, ita bata rike kanta ba taya ya zata iya rike wani."!! Ya k'arashe maganar tasa a zafafe! Jahid yace." Gaskiya bata kyauta ba gani bata gayamin haka ba, amma kayi hakuri don Allah komai ka gani tsautsayi ne amma tabbas bata kyauta ba. " Cike da takaici yace." Yau kwana biyu rabona da in ji sweetheart nayi kewayar jiya babu yanda banyi da yarinyar nan ba ta bani ita muyi hira ta kashe min waya, ni da yarinya ta." Jahid yayi murmushi tare da fadin"Sai kace Wanda zakayi hira da babban mutum ka kwantar da hankalin ka zaka dawo ka yadda sweetheart dinka cikin koshin lafiya." Ajiyar zuciya ya sauke yace." Insha Allah karshen watanan zan dawo zan je Umara insha Allah." Jahid yace." Alhmdullahi kayi mana addu'ar zaman lafiya ni da Asma'u da samun zuria mai kyau kasan karshen wayan aka sanya lokacin d'aurin auranmu." Amjad yaji wani irin fad'uwar gaba ta rikito masa zan can yazo masa a baza ta! Yace." Jahid yaushe aka sanya rana babu labari."! Jahid yac."Wallahi my friend abun yazo a bazata kuma a kurararn lokaci Dan har yanzu hankalina ba a kwance yake ba dalili Momyna bata kaunar auramu da Asma'u, shine nake cikin wani hali shaf na manta ban fada maka ba." Cikin dakiya da kokarin danne damuwa yace." Na tayaka murna Aboki amma INA baka sha'wara cewa ka bi umarnin iyaye domun Neman albarkar su, ina ganin tunda Momy tace bata so kayi hakuri mana ka bari."! Jahid yace." Wallahi nayi kokarin hakan na kasa INA yiwa Asma'u wani irin so Wanda nakasa gane irin shi ka tayani da addu'ar Neman zabin Allah." Girgiza kansa yayi yana jin wani daci Cikin zuciyar sa yace." Insha Allah zan sanya ka a addu'a. " Jahud yace." Nagode my Aboki. " Amjad yayi murmushi tare da fadin. " ka kula min da baby please kuma ka sanya ta ta Mai da ta gurin granny yau INA son muyi hira da ita please. " Jahid dariya kawai yake masa sukayi Sallama. "

***

Babu laifi Zazzab'i ya sauka daga kaina sai baby ce take fama sosai Jahid da yazo kafin ya tafi gurin aiki ya fada min duk yanda sukayi da Amjad din na dinga mamakin rashin kawaici irin nashi nace"Insha Allah Jahid ko baka fada bs yau din nan zan mai da masa yarinyar gida nagaji da wannan gorin wallahi,." Jahid yace." Baki fahimce shi bane shima yana da tasa manufar shiyasa ." nace "Jahid Dan dai abokin ka ne kake kareshi dariya yayi min tare da fad'in"Ya jikin baby dim nace DW sauki kam hancin ta ya daina yoyo sai dai zazzab'i"Yace shima zai sauka Insha Allah." Godiya nayi masa shi kuma ya tafi tare da jaddada min in mai da baby gida nace insha Allahu." Ko da na fadawa Umma abunda mahaifin. Baby yace a kanta sai tace aikuwa baza a maida ita gida tana cikin wannan yanayin ba, Sam baza a fita da ita ko ina ba kasamcewar akwai sanyi a gari har yanzu kuma da akwai sauran hadari, shuru kawai nayi ina jiran Abunda zai biyo baya.

****
Duk abunda yake yi k'arfin hali yake tunda yaji labarin d'aurin auran Jahid da Asma'u ya nemi nutsuwar sa ya rasa hak'ika al'amarin yazo masa a bazata! Kullum ta Allah kokarin sa ya yakice yarinyar daga rayuwar sa, abun ya fassakara duk abunda yake mata yana sane yake mata domin ya kuntata matane suyi fad'an da zai ji tafi ta a ranshi gaba daya amma dake yarinyar taurin rai ne da ita taki yadda suyi fada da ita sha fa yanzu gani yake babu yadda za'ayi ya auri Mimi daga baya kuma ya aure Asma'u a da dai yayi niyyar ya hadasu ya aura dalilin son da yakewa Asma'u, sai bayan ya auri Mimi ne ta koya masa sonta kyawawan haleyen ta suna burge shi, a wannan zamanin dai samun mace kamar Mimi sai an tona... Yini yayi yana tunanin Abu d'aya. K'arfe goma na dare dai-dai ya jira granny dake shirin kwanciya, ta dauka suka gaisa Yace. " Granny bani baby Aysha ko tayi bacci ki tashe ta kinji."" Cike da mamaki tace." Wai kai baka da lokacin kiran waya ne sai dare."? Yace." Time din nake da sukuni ki bani sweetheart please."Ya wani marairaice murya. Tsaki yaja tace." Wace baby kuma wacce take gidan kakaninta." Tashi yayi da sauri yace." Me kika CE Granny. "!? Cewa nayi baby na gidan kakanin ta, yo ko tans gurina kana tunanin zan tashe ta daga bacci saboda shirmen ka." Kashe wayar sa yayi ba tare da ya tsaya ya gama sauraron Abunda granny take fada ba.
Wayar Asma'u yake kira, busy yau ma tana waya da wani, zuciyar sa kamar tayi bundiga ya jefar da wayar kan bed d'in ya dafe kanshi da duk hannunwan shi biyu.

*29/11/2019*

*BABBAN YARO*

*MALLAKAR_BINTA UMAR*

*68*
Chapter 56 · 0% Book details