← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 57 OF 60

Sashe 57

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 5 min read

Yafi Rabin a wa a Zaune a gurin sannan ya mike Cikin mutuwar jiki ya shiga toilet alwala ya dauro ya fito yana hada hanya, dadduma ya shimfid'a ya fara sallahr nafila cike da Neman zabin Allah domin shu kanshi al'amarin sa tsoro yake bashi. Komai ya da gule masa lokaci guda, bayan yayi idar ya jima yana rokon Allah ya kawo masa dauki a rayuwar sa, yaji wani sanyi cikin zuciyar sa, kwanciya yayi kan daddumar bacci ya dauke shi mai nauyin gaske.
Ni kam bayan mun gama waya da Jahid tunani na fad'a mai tsayi zahiri dai gashi mahaifiyar shi ta nuna bata kaunata karara ko yanzu sai da ya kara fad'a min irin artabun da suke bugawa da ita kan Dole ya janye maganar saboda ta samu labarin kai kud'in da akayi a family lokacin da taje gidan buki suka dinga yi mata Allah ya sanya alkairi, sai abun yayi ta bata mamaki sai daga baya ta fahimta, shine tasa akai kiran sa, ta kare masa tanadi har tana ikirarin zata tsine masa in har bai janye maganar ba, duk yanda naso na fahimtar dashi ya kasa fahimta na lura Jahid idonshi ya rufe a kaina baya tsoron Abunda zai je ya dawo, dole in Sanar da Umma halin da ake ciki, yanzu jikina ya fara sanyi da al'amarin hak'ika ina son Jahid tsakani da Allah kuma bazan so ya fad'a cikin halaka ba, tunani na gwara ya hak'ura kawai domin ya samu albarka iyaye da wannan tunane-tunanen nayi bacci kwata-kwata na manta da Wani Amjad da damuwar shi. Da safe duk na warware wa Umma abunda yake faruwa tace"Asma'u dama ni tuntuni sai DW nace ki hak'ura da yaron nan tunda uwarsa bata so kika k'i, kuma kin san halin Kawun Ku ba kirki ne dashi Yanzu in wata magana ta sake faruwa zasu har gida su ci mun mutunci ne ki jawo tashin hankali ya kare a kaina da ban ji ba ban gani ba." Shiru nayi wasu zafafan hawaye na zubo min duk ja rasa wane tunani ma zanyi.. Karar waya ta naji a dakinmu da sauri naje na dauko ina duba baby dake bacci cikin kwanciyar hankali, INA dubawa naga jahid din ne ya kira sallama nayi ya amsa murya babu dad'i ya Dora da fadin"Asma'u duk abunda kike ki aje don Allah ki mai da wa da mutumin nan yarinyar shi, wallahi yai shi ya tashe ni daga bacci dama ga shi da kyar na samu ya dauke ina fama da damuwa."
Nima cikin damuwa nace"Jahid ka kwantar da hankalin ka dama yau nayi niyyar mai da ita saboda Umma tace a k'yaleta ne yasa saboda sanyi jiya amma insha Allahu yau zan mai da ita Nima na huta da jaraba." Kashe wayar nayi a fusace! Ban saurari maganar shi ba. Hakan ce ta kasance bayan sallahr la'asar Munnu tazo gidanmu nan muka tafi domin mai Da baby kamar yanda nayiwa Jahid din alk'awari munnu tq kalleni cikin damuwa tace"Asma'u fyskar ki ta nuna alamun damuwa tabbas da Abunda yake damun ki."! Girgiza kaina nayi nace"Tabbas Munnu abokin kuka shi ake gayawa mutuwa nan na kwashe duk abunda yake faruwa na fada mata har irin rashin kunyar da nayi Monye Jahid din sai da na fad'a mata. Munnu ta dinga mamaki daga bisani tace"Wallahi wasu masu kud'in haka d'abi'ar su take Sam basa son talaka kiri-kiri ta zo har gida ta ci muku mutumci saboda zubar da girma yanzu kuma idan mukayi aura kuka Tara zuria tace me? Da aure da mutuwa duk na Allah ne mutane ne basa ganewa wallahi." Nace"Ke wace shawara kike gani." Tace"Kawai ki cigaba da nan zabin Allah idan da Rabin auran Ku za'ayi dashi amma ko da wasa kar ki nuna masa kin karaya domun kinga shima yana daurewa gashi saboda ke ya bujerewa mahaifiyar sa." Da wannan zancan muka isa. Babu walwala a tare damu muka shiga, Iyami da Granny na zaune a parlor kamar ko da yaushe ta amsa mana sallama a sake Iyami kuwada saurin ta ta k'araso gurin mu tana fadin "Oyoyo baby kokarin daukar ta take yi nayi saurin kwantota ta dauke ta tana cilla ta sama, yarinyar ta gane ta sai ta fara yi mata dariya. Zama mukayi a nutse muka gaisa da granny dake tambayar mu Umma nace" Tanan k'alau tace ma a gaishe ki da kyau kafin tazo." Granny tace"Ina amsawa nima...Iyami kawo musu abunci." Tafad'a tana kallon Iyami dake wasa da baby Granny ta karb'i baby ta nufi kicin, cikin zuciya ta nace yau kam baza muci abincin gidannan ba wallahi Mik'ewa nayi Munnu ta mike granny ta bimu da kallo tana fad'in"Za'a kawo muku abunci kun mik'e." Nace"A koshe muke Wallahi." Cikin nazari tace" kamar akwai abunda yake samun Ku kun shigo babu walwala kinji sakewa Lamar yanda kuka saba, yake kawai nayi nace"granny kenan babu komai wallahi mu dai mun tafi sai mun sake zagayo wa." Hanyar futa muka nufa Abun kamaer almara babyta fashe da kuka tana d'ago hannun ta! Granny tace"To maza Ku dawo Ku tafi da ita gashinan tana kukan rabuwa da Ku
" gaba nayi cikin zuciyata nace yarinyar nan ko kukan me zata yi bai same ni ba wallah" Munnu CE ta koma da baya ni kuwa tuni na fuce da sauri, ina jiyo kukan ta har waje, ko da Munnu taje kin yarda tayi da ita sai kuka take yi Granny tace"Asma'u take nema ba ke ba. iyami ta kwalawa kira tana fadin "Bazan iya da wannan rigimar ba zo ki dauke ta yarinya k'arama da gane mutane." Iyami ta shigo da sauri ta dauke ta tana rarrashin ta, Munnu tace "Asma'u baby ta gane ki sosai wallahi har nayi sha" awar Dadyn ta ya Baki tunda kuna kusa in Allah yayi nufin auran ki da Mujahid." Murmushin takaici nayi nace"Munnu kenan, nasan ko mutuwa zanyi bazai bani ba, kar ki so kiji yanda nake jin zafi a zuciyata jin kukan da take yi." Munnu tace"Allah ya kyauta masa amma gaskiya na lura guy nan ya sanja hali da ba haka yake ba." "Hummm! Munnu kenan dole yayi abunda yake so tunda gonar sa a ka shiga kuma yana ganin ya wuce komai na rayuwa shiyasa." Munnu tace"Wallahi maganar ki gaskiya ce Allah ya kyauta." Nace "Ni Abunda yake damuna Abu daya ne aurana da Jahid wallahi yanzu abun tsoro yake bani ina jin tsoron abunda zanje in Tarar."! Insha Allahu alkairi zaki yadda ke dai ki cigaba da yin addu'a.'a" nace "Nagode Munnu." Da Wannan hirarar muka isa gida.
Chapter 57 · 0% Book details