Sashe 42
Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 8 min read
Tsanin azabar da Mimi ta sha a wannan daran ya d'agawa Amjadu hankali domin kuwa a zaune suka kwana Mimi rungume a jikinsa, kamar ranta zai futa rik'on shi kawai take ya YAFE mata. Saboda tausayin ta bai San sanda ya fara zurarar da hawaye ba, rungume ta yayi tsam!! A jikinsa yana tofa mata addu'oi. Sai daf da asubahi bacci ya dauke ta, shi kuwa dungurgur ya kwana a zaune yana kallonta sai da yaji kiran sallahr sannan ya mike toilet ya shiga yayi Wanka ya futo tsaf shirin massalaci yayi yazo ya tsaya kanta, bacci yaga tanayi sosai, cike da tausayi yake kallon fuskarta inda idonuwan ta suka zurma cuki
[11/22, 8:02 AM] BintuUmarAbbale: Ko da ya dawo daga massalaci Mimi bata tashi ba, bai tashe taba sai ya zauna kusa da ita hade da rik'o hannunta ya rike tam! Ya k'urawa fuskar ta ido, Cikin zuciyar sa ya jinjinawa mata da irin wahalar da suke sha yayi d'aukar ciki da haihuwa.
Ya minti talatin a zaune a gurun yana sakawa da kwancewa, kana ya mike ya dauko wayar sa yana kunnawa sakkoni suka dinga shigo wa Sam bai bi takan su ba, numbar Mujahid ya kira. Mujahid yace." Gashinan zuwa gidan.
Kashe wayar sa yayi ya futo parlor lokacin granny ta futo tana kicin tana hada musu kalaci zama yayi a cikin kujera cike da damuwa.
Jahid yana shigowa ya ganshi a hargitse zama yayi kusa dashi ya bashi hannu suka gaisa, yace."yana ga duk ka wani furgice ne."?
Ajiyar zuciya Amjad ya sauke yace." Jahid yanzu haka Momy take shan wahala jiya kwanan zaune muka yi na tausaya mata wallahi."
Jahid yace." Dole kam abun tausayi CE, dama abunda ya kama ta ayi mata kenan." Ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu yace." Da har na fara tunanin futa da ita waje a duba ta."
Murmushi Jahid yayi yace." Kar ka damu Aboki duk abunda kake tsammanin za'ayi mata k'asar waje insha Allahu zamu yi mata zan tsaya tsayin daka kan almarin ta kasan sai asibitin mu muna da likitoci k'wararru so kar ka damu."
Gyada kansa yayi yace." Yaushe za'ayi aikin." ? Jahid yace." Insha Allah ranar Monday za'ayi." Saura kwana uku kenan."? Jahid yace." Eh saura kwana uku. " OK Allah ya kaimu nagode K'warai. "
Nan granny ta futo daga kicin ta same su, suka gaisa da Mujahid cikin barkwanci sannan ya bar gidan
Amjad din ta kalla a nutse tace" Aishatu ta tashi ne."? Girgiza kansa yayi kamar wani maraya.
Granny tace"Sai hakuri ka kwantar da hankalin ka naga kamar ka tada hankalin ka, insha Allah komai me wuce wa ne." Shiru yayi mata kawai. Ita kuma ta wuce daining domin shirya kayan breakfast.
*******
A gajiye na dawo daga makaranta na zube rumfar Umma cikin gajiya da ishirwa nace"Wallahi Umma da nasan zan sha wahala haka da ban dauki azimin nan ba, kinga yau juma'a anyi rana mutuka ."
Tace"Hakane ai zaki samu lada sosai. " lumshe idona nayi kawai ishirwa Duk ta dame ni, so nake a idar da sallahr la'asar nayi wanka ko zanji dadin jikina.
*********
Tunda motar shi ta shiga prison din, masu gadi da ma'aikatan gurin suke murna da zuwansa dama duk karshen wata yake ziyartar su, irin wannan ranar ta juma'a bayan sakkowa daga sallahr juma'a.
Daurarru dake kulle suna hangoshi ta tagogin dakunan su. Murna da farin ciki ya ishe su. Bayan motar shi wasu manya manyan motoci ne na company *Dangote* suka dinga shigowa cikin prison din, dukaninsu suna dauke da kayayyakin abunci na'ui ka daban-daban.
Ba tare da b'ata lokaci ba, 'yan jarida dake gefe guda suka mike domin fara'a aikunsu, dama duk wannan ranar sukan kasance a gurin da suka San yana zuwa kai ziyara, matasa majiya k'arfi ne suka fara sauke kaya suna ajewa inda aka tana da
Yana cikin mota Duk yana kallon abunda yake faruwa da irin hayaniyar da ake a gurin. Sai da suka gama kwashe kayan tsaf, sannan ya futo daga motar Aikuwa 'yan jarida suka yi caaaa! A kansa basu nemi suyi magana dashi ba, amma sun baibaye shi suna d'aukar hotonsa hade da vidio duk wani motsi NASA sai sun dauka duk inda ya sanya kafa sai sun bishi.
Ofis din shugaban gurin ya nufa.
Suka bishi a baya sai da suka ga ya shiga ofis din sannan suka dakata, Rambo da doh-doh suka tsaye bakin kofar suna zare ido.
Hamshakin mutum ne zaune kan kujerar sa sai juyi yake, kana kallonsa zaka San bashi da imani fuskarsa a murtuke take leb'anshi baki kirin kana gani kasan yana shan taba da abunda ba'a rasa ba, yana da manya manyan idanu,hanci sa yana da fad'i amma ba sosai ba, sannan yana da kiba dai-dai misali. Duk wani Abu da yake faruwa ya na gani ta CCTV Duk ta hasko masa komai da zuwan Amjadu gurin da yanda mutane suke ihu da yanda 'yan jarida suke turereniya akan sa, duk ya ga komai.
Wani irin b'acin rai da kyashi duk suka dame shi, mugun haushin yaron yake ji saboda ya zame su kadangaran bakin tulu.
Abun mamaki suna hada ido da Amjadu din yaji gabansa ya fad'i, Yaron yana da kwarjini da haiba, take ya gyara zama yana masa barka da zuwa
Kafin ya zauna hannu ya fara mik'a masa suka gaisa a muntunce.
Sannan Amjadu yace." Fatan duk na same Ku lafiya."?
Alhaji Gali yace." Lafiya lou Alhmdullahi Ashe ka dawo gari. "
Babu walwala a fuskarsa yace." K'warai kuwa jiya na dawo insha Allah."
Kamar gaske Alhaji Gali yace." Ka cika Dan halak me son talakawa abunda gomnati ya dace tayi bata yi kai gashi kayi mungode K'warai ubangiji Allah ya kara k'arfin a arziki. "
Amjadu ya bashi hannu suka gaisa, yace." Naga muna daf da shiga wata me albarka ga kayan abunci nan insha Allah daf da sallah zan turo musu kayan sawa." Alhaji Godiya yake kamar gaske.
Amjadu ya Mike hade da yi masa sallama ya futa.
Yana futa Aljani Gali ya dauki wayarsa ya fara kiran me girma governor, sai da ya kira sau kusan uku sannan aka dauka, da sauri Alhaji Gali yace." Allah ya tai make ka?" Governor ya gyara zama kan kujrrarsa Cikin ginshera yace." Tare da kai mutumin." Gali yace." Yaron nan fa ya dawo wane shiri zamu yi a kanshi."?
Governor yace." Na sani ai duk wani Abu da ya faru a gidan yarin gashi a gabana ina gani, akwai shirin da muke masa ni da su Alhaji Hashimu insha Allahu sai mun rusa shi.
Alhaji Gali yace." Yana da kyau hakan , gaya nan ya kawo uban kayan abunci ." dariya governor yayi yace."ka d'ibi iya yanda kake so ka bawa Wanda kake so sauran a zubah a store na gidan, kar ka sake ka sakar mu, ka cuzguna musu abunci sau d'aya nake so a dunga basu haka ruwa ma sau d'aya zasu sha a rana."
Alhaji Gali ya saki dariya tare da fadin"Yallab'ai ai ba sai ka fad'a ba, haka ce zata kasance insha Allah. "
Dariya suka kyalkyale da ita sannan suka kashe wayoyin su, dukanin su suna cike da farin ciki da annushuwa.
Amjadu kuwa bayan futar sa daga gidan prison din kai tsaye gidan marayu suka nufa. Nan ma duk wani Abu da ya sauke gudin prison din haka ya sauke musu, marayu da marasa galihu ranar murna da dad'i duk ya ishe su, sosai kuma yayi Rabon kudi, musaman mata masu raino rainon yara k'anano sosai suka samu kud'in a gurun shi.
Sai daf da magariba ya koma gida. Granny da Mimi na zaune a parlor duk suna kallon abunda ya faru a TV.
Granny ta hau share hawaye tana tuno iyayen sa , addu'a take masa Allah ya kare shi daga sharrin magauta tabbas idan ya zama shugaba a garin kano za'a huta dashi.
Amma Sam bata yi masa sha'awar mulki.
*********
K'arfe bakwai ta ranar lititin dai-dai tayi mana a babban hospital din Nasarawa dake jahar kano.
Ranar ina da makaranta amma haka Na kashe ta saboda nasan ko naje babu abunda zan iya yi tun jiya nake Cikin halin damuwa INA wa Mimi addu'a Allah yasa ayi lafiya,
Umma kuwa kwanan zaune tayi da carbi a hannu, a subar fari aunt hauwa ta iso gida saboda haka gari na waye wa muka nufi asibiti kowanne bakin shi da dauke da addu'a.
Muna zaune suka shigo a sibitin Amjadu da granny sai Mimi dake rungume a jikinsa, ta kara yin haske sosai. Tana ganin Umma ta rugu da gudu ta rungume ta hade da fashewa da kuka, Umma ta fara rarrashin ta tana fadin"Mimi kina dauke da da lalura kina gudu, ki daina kuka kinji ko." Cikin kuka Mimi tace"Umma ki YAFE min ko da Zan mutu."
Naji gabana ya fad'i jin abunda tace
Kallonta nayi nace"Don Allah ki daina mana wannan maganar Mimi."
Shiru tayi min ta k'araso gurin aunt Hauwa dake share hawaye rungume ta tayi tana kuka, aunt rarrashin ta take da kalamai masu sanyi.
Hada ido muka yi dashi yana yana tsaye jikin kofa Yana kallonmu jikin sa sanye da shadda fara tas! K'afafun shi sanye da takalman me gidan ya tsaya baki , yayi kyau sosai da sosai,
Idan ba idona ne yayi kin gizo ba sai naga ya fad'a idanunsa sun zurma ciki, a hankali ya k'araso kusa da Umma hade da Dan risanawa yana gaishe ta.
Granny ma k'araso wa tayi tana tsokan Mimi alhalin itama Cikin zuciyar ta daurewa kawai take, tun kafin Suzo take share hawaye: Cikin k'arfin hali aunt Hauwa take rarrashin Mimi hade da karfafa mata gwiwa, shi kam Amjadu suna gama gaisawa da Umma bar gurin.
Motar sa ya nufa, ya zauna bayan ya kunna karatun alk'urani, me girma yana saurara
Muna zaune aka zo a tafi da Mimi.
Duk muka bita da addu'ar samun nasara.