Sashe 49
Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 8 min read
Babu kuzari a jikina na futo daga dakin Mimi hannuna rike da k'aramin hoton mu, kusa da Umma na zaune a hankali nace"Umma zaman me muke yi a gidan nan? Wallahi nagaji gani nake kamar Mimi zata dawo gwara mu tafi." Umma tace"Eh dama yau kam zamu tafi tunda an share makoki, muna jira maigidan ya futo ne zamu je duba baby insha Allah daga asibitin sai mu wuce gida." Granny tace"Habadai Ku kuwa ai sai kace Wanda ake kora kwabari kuyi sati biyu mana in baza Ku bari ayi ar'bain ba, har yanzu fa ana zuwa gaisuwa." Umma tace"Tafiyar tamu ta dole CE Hajiya ni kaina a takure nake a gidanan wallahi, kiyi hakuri duk Wanda zai mun gaisuwa ya same ni a gida." Granny tace"To Allah dai ya gafartawa wannan yarinya.
Tsaf ya futo Cikin dogayen kaya,na lura tunda akayi mutuwar nan bai sanya k'ananun kaya ba, k'amshin sa ne ya cika parlor ya tsaya bakin kofar shi yana gyara links dinshi, saurin kauda kaina nayi daga kanshi ina jan tsaki kasa-kasa wallahi wani mugun haushin sa nake ji. Umma tace"Ka futo kenan."? A hankali yace." Eh Umma Ku tashi muje yanzu, amma naji kuna wata magana ko." ? Umma tace"Eh kam yau zamu tafi gida." Yace." Umma kuyi hakuri ayi sadakar ar'abain mana." Umma tace"Bazai yiwu ba, INA da uziri Asma'u kuma makaranta zamana a gidanan bashi zai dawo da Mimi ba." Yace." Hakane Umma shikkenan Allah yasa ka da alkairi. " mik'e wa Nayi da sauri na bar gurin, hijab dina na dauko dama tunda nazo kayan Mimi nake amfani dasu, Umma ko granny ce ta dauko mata wasu sabbin atampopi super take sanya wa yanzu daya daga cikinsu a jikin ta, Granny ta mike tana fadin "Baza Ku barni a baya ba, muje inga 'yar yarinya cikin kwalba."
Aikuwa ko da sukaje Asibitin fafur likitoci suka hana su shiga ganin baby Aisha yarinyar da Ubanta yayi mata huduba da sunan mahaifiyar ta, shi kam ai dactors din sun San shi farin sani dolen su suke kyaleshi ya shiga yaga babynshi kullum baya iya bacci sai yaje ya ganta haka kazalika kullum kara kaunar yarinyar yake Cikin zuciyar sa, yarinyar kamar su daya da uwarta sai dai ta kwaso hasken fatar shi, fara ce sosai, Amjad kam yafi Mimi haske nesa ba kusa ba, Alhmdullahi tana samun kulawa sosai daga gurin dactors ta fara k'wari da girma jikinta ya fara murjewa tana rayuwa cikin kwalba cikin hukunci ubangji.
Babu yanda muka iya haka muka hakura amma naji babu dad'i a zuciya ta domin naso inga baby nan wallahi ga yanda naji ubanta na fadin kamar si daya da Mimi, Jahid nayi ta kira a waya yak'i dauka saboda yasan zancan dokar asibitin CE, yana ganin kan Asma'u ba zai sanya ya karya ba.
Amjad har gida ya kaimu Cikin motarsa, zuciya babu dad'i na futo daga motar ba tare da na jira su Umma da aunt Hauwa ba, barin su nayi tare dashi suna sallama, Ya Aminu ne kawai a gidan dama yasan da dawowar mu tunda aunt Hauwa tayi masa waya tsaf muka tadda gidan, rumfa na zube kan leda na fara kuka.
Suka shigo suka same ni a haka aunt tace"Wannan wane irin shirme ne." ? Cikin kuka nace"Aunt don baki San yanda nake ji bane a zuciya wallahi Ashe duk gujewa mutuwa da muke yi akan Mimi tana jika aunt Mimi tasha wahala a rayuwar ta wallahi" aunt tace"Sai hakuri dukanin mai rai mamaci ne addu'a kawai zamu yi mata."
Ya Aminu ya shigo dakin yana fadin"Wannan kukan da kike yi kina kara mata azaba ne idan ta fado miki a rai kiyi mata addu'a. " shiru kawai nayi musu.
Ko da na koma makaranta ba wani sake ba, kullum muna tare da Munnu muna zancan Mimi da halayen ta na hakuri da ban dariyar ta da saurin kukan ta wani lokacin idan na tuno hae sai na share hawaye sai kawai inyi mata addu'a samun rahamar Allah.
Kullum kuwa sai na damu Umma da zancan babyn Mimi nace ta nemi alfarma gurin Amjad ta dauko ta ta raine ta kamar yanda ta raini Mimi, Umma tace wannan kuma nice zanyi hidima tunda nice mamanta a yanzu, nan na dauki a niyar fad'awa Mujahid kudirina kan Baby Aisha, yarinyar da ta zama cikkakiyar mutum domin yanzu tayi k'wari sosai ta cika wataninta na haihuwa, Jahid yace." Zai fad'awa mahaifin ta ko zai amunce, dama ya karb'i babyn sa, yau kwana uku kenan, jin abunda Jahid din yace sai ya d'aga min hankali Ashe har sun bashi baby babu labari mu gamu a zaune kullum muna kwadayin ganinta, to yanzu da ya karb'a wa ya kaiwa? Ni kadai nake tambayar kaina, ina dawowa daga makaranta na fad'awa Umma halin da ake ciki, tace "Aikuwa bai kyauta mana ba, muma ai muna da hakki a kanta, gashi kwana biyu ya daina kiran Aminu a waya balle kusan halin da ake ciki." Nace"Umma to yanzu wa zai kaiwa babyn ma." Umma tace "Kakarshi mana." Shiru na minti biyu nace "Umma kakarshi bata da k'wari don Allah ki amunce a dauko ta." Umma tace"Ai dama bani naki amincewa mutukar zai bamu muna so hakkin sa ne." Nace "Nayiwa Jahid magana zai nemi alfarma a gurin shi." """"
Rayuwa kenan duniya babu tabbas yau kwanan Mimi Hamsin da bakwai a karkashin kasa komai yayi farko yana da k'arshe Amjad ya sake ya barwa Allah komai ya tabbatar dukanin Abunda ya same shi daga Allah ne.
A halin yanzu ya maida hankalin sa ne gurin k'ara bunk'asa harkokinsa na waje, a cewar sa mu'amula da turawa yanzu ya fara saboda wasun su sun fi muslumin mu amana da tausayi, tunda gashi da Dan uwanshi musulmi aka hada baki dashi gurin cutar shi da izgilanci ga Allah ga manzon sa, yana nan ya sanya matakan tsaro ko ta ina yayi lamfu bunkice yake sosai aka mutanan da suka kulla masa sharri, maganar company kuma tunda sun rusa shi babu wasu kudinsa da zai futo dasu ya saka tada wani, suje kawai Wanda bai ji bari ba zai ji hoho.. Loptop ce a kan cinyar shi yana duba sakkonin da Anthony ya turo mishi tsawon lokuta dama wasu ya bashi amsa wasu bai bashi ba, ya bari ne in yaje can sai suyi maganar. Granny CE ta futo daga dakin ta ta zauna kusa dashi.. Hankalinsa na kan Loptop din bai dago ba yace." Ina Sweetheart yau banji motsin ta ba." Granny tace"Tana gurun Iyami tun safe da tayi mata wanka take bacci." Dariya yayi yace." Wannan Aishar ai rigamammiya ce tafi uwarta fitina." Granny tace"Mai suna Aisha kuka ne da ita ai." Yace." Granny ina tunanin cikin satin nan Zan tafi Chana kuma zan kai wata uku a can insha Allah, amma ina tunanin tafiya in barku fa."
Granny tace"Allah ya taimaka ni kam babu wata chana da zan biki to kaji."!! Dariya yayi yace." Shikkenan zamu je da sweetheart d'ina OK." Hararshi tayi tace"Kaje ka bawa wa ita wannan garin ai ku da ku ga zaku iya zuwa." Murmushi yayi kawai ya cigaba da duba lptop d'insa.
A hankali tace"Ni ko nace dama akwai wata magana da na yanke a kanka." Gyada kansa yayi tare da fadin"Ina sauraren ki." Tace"Mai zai hana ka nemi auran Hafsatu. Da zan ce ko yarinyar nan Asma'u to amma naga wannan yaron Dan albarka Mujahid yana nemanta ana barin halas Dan kunya ko ba haka ba ne."? Bata fuska yayi had'e da ya mutse ta yace."granny ki k'yaleni in huta tukkuna ni kam yanzu babu maganar aure a gurina sai an kwana biyu sannan. " Tace"Aikuwa dole kayi aure domin shine cikar mutum ka kai munzali kace baza kayi aure ba, baka Isa ba."
'Yar dariya yayi yace." Granny nayi aure har na samu riba mutuwa ta rabani da mata ta, ki k'yale ni na huta tukkuna zanyi amma ba yanzu ba." Tace." Ni kam bazan ta kallon ka a haka ba dole ni nayi maka aure. " dariya yake yana mamakin rigimar ta, yace." Ok kiyi min aure sai in barki da matar wallahi inyi tafiya ta tunda bani na saki ba." Granny ta hau zuba masa masifa, dafe kansa yayi yace." Ina aiki kin hani oh my god."!!! Iyami ce ta shigo da Baby Aisha a goye a bayanta tana motsi, alamun ta tashi. Granny tace" Ta tashi ne."? Iyami tace"Gashinan fa da alama Dadynta take so." Rufe loptp din yayi yana kokarin karb'a baby daga hannun granny sai murmushi yake, yarinya tayi mulmul da ita tayi wata irin kib'a hasken fatarta ya kara futowa Iyami ta iya raino gaskiya sai wani kamshi take yi, tana cikin kayansu na jira jira abun gwanin sha'awa, leb'anshi ya manna a kumcinta yana sakin ajiyar zuciya yace." Momyna 'yar rigima hummmm! Yau ba kuka kenan. "? Kamar yana da magana da babban mutum haka yake yin magana da baby Aisha.
Granny tace"Aiki ya same ka kana magana kamar kana magana da babban mutum." Dariya yayi hade da kamo bakin baby yana Dan tsotsa yarinyar ta fara mamular leb'an shi da sauri.
'Yar dariya yayi ya cire bakinsa ya kalli Iyami dake zaune kusa da granny yace." Allah Iyami zanci tarar ki sweet heart dina yunwa take ji ga alamu nan na gani." Iyami tace"Afuwa Uban gida dama yanzu nake so in dama mata madarar ta, kaga ai bacci take kuma sweeh Hart din naka ci ne da ita Wallahi ." Dariya ya kyalkyale dashi jin yanda Iyami take fadi wai sweeh hart. Yace." Ungo ta ki bata bana so tayi kuka yanzu dai kin San halinta." Iyami ta karb'e ta da sauri ta futa...... Wayar shi tayi k'ara yana dubawa yaga Jahid ne, murmushi yayi hade da daga wayar sallama yayi Jahid yace." Kana gida ne." ?
"Eh ina Gida yanzu amma k'arfe biyar dai-dai zanje government house." Jahid yace." OK ganinan zuwa nima ina Gida kasan yau Sunday muna Hutu. " Amjad yace." OK sai ka shigo din." Kashe wayar yayi ya cigaba da abunda yake yi.