← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 45 OF 60

Sashe 45

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 8 min read

Yana futa ya hangosu sun samu nasarar shigowa, ciki dake akwai tazara mai mugun tsayi kafin su gurin shi, sai suka yanko da gudu suna ihu!
K'ik'am ya tsaya had'e da hard'e hannunsa a kirjin sa yana jiran k'arasowar su.
Mujahid Khalid da Su Rambo sun tsorata mutuka suka fara Jan rigar shi.
Fuzgewa yayi a zuciya! Yace. " Ku jira Ku ga abunda zai faru, wallahi duk Wanda yazo gurin nan to sai dai Uwarshi ta haifi wani."
Ja da baya suka yi cike da tsoro! Fito yayi sai ga DOG dinshi ya shek'o a guje! Yana wani irin haushi!!! Magana yayi masa da ido. Aikuwa sai ya buga wani uban tsalle ya tunkari su yana wani danbanzan zufa ya cafki k'afar daya daga cikinsu sai da ya huda ta tukkuna ya sake shi. Kafin kace kwabo ya fad'i a gurin yana nishi ga jini ya fara zuba.
Wani tsagera ne ya kawo sharb'eb'iyar wuk'ar zai dab'a masa, da sauri yayi sufa ya datsa masa hak'oran sa a fuskar sa, dai-dai hancin sa, ya yago Innalillahi sai ga rabin hancin sa da naman kumatun sa a bakin DOG din. Kwanciya yayi a gurin yana ihu! Shi kuwa Amjad nad'e hannun Riga yayi ya tunkare su, yana wani zare idonsa!
Tsoro ne ya shige su dukanin su ganin yanda dog din yake barna har ya jikkata mutum biyar gasu nan a kwance a gurun.
Take suka fara guduwa domin ceton ransu.
Amjad ya buga musu wata irin tsawa! Tare da fad'in"Ku tsaya mana ku kashe ni kamar yanda kuke bukata."!!! Ko juyo wa basu yi ba, gudu kawai suke su Isa bakin gate.
Daga murya yayi sosai Wanda sai da gurin ya amsa yana magana da masu gadi cewar maza su rufe gate din nan, kar su bar kowa ya futa."
Aikuwa suka mike da kuzari suka ja gate din da k'arfi suka datse
A nutse yake tafiya hannunshi goye a bayan shi, fuskar sa a murtuke ya k'araso gurin su: One by one yake kallonsu tsawon five minutes, murmushi yayi mai ciwo yayi gyaran murya gami da gyad'a kansa har sau biyu murya sama! Yace." Kun shigo da shirin aika ni barzahu ko."? Shiru su kayi suna muzurai! Gefe guda kuma ga *Tegar* na wani irin haushi!!!!! Shiru suka yi........ Ya cigaba da cewa"Zaku kashe ni kan abunda kuke zargina dashi, Wanda ni nasan ban aikata ba hakane ko ba haka bane."?
Sunkuyar da Kansu suka yi cikin mutuwar jiki. Girgiza kansa yayi cikin takaici da tsabar bakin ciki yace." Gani ga ban Ku Ku kashe ni, ni Ku kashe banza kamar yanda kuke fad'a. "! Tsit! Suka yi.
Yace." Duk Ku aje makaman hannun Ku."
Aikuwa suka aje da sauri!
Yace." Kuna so Ku kashe ni Wanda baku San in kuka aikata haka ba, to babu shakka hukuma zata dauki mataki akan Ku, tunda ba ita ta sanya Ku ba,hakane ko ba haka ba."
Duk suka ce "Hakane."! Yace." Duk abunda kuke zargina dashi ban aikata ba, sharri ne kawai, akai mun. "
Shiru suka yi ya cigaba da cewa"Kuma Ku zuba ido zaku ga irin hukunci da za'a dauka a kaina, tunda dai kun k'one company na kunji dad'i shikkenan, amma babu shakka sai na binciko Wanda aka had'a baki dasu aka kullamin wannan k'azafin." Duk sai suka ji jikin su ya mutu, take suka zube suna bashi hakuri.

Murmushi yayi yace." Ba wai na fad'a muku Wannan maganar ba ne domin Ku yarda da ita, A'a duk wani hukunci da zaku yanke kaina Ku yanke Ku kashe ni ku kashe banza."!
Ya fada da wani murmushi a fuskar sa, na tsantsar takaici.

Hakuri kawai suke bashi cikinsu kuwa har da masu kuka saboda tausayin sa. Yace." Mutukar nakama mutanan da aka hada baki dasu cikin ma'aikatana tom ni da kaina zan hukunata su da kaina in yaso nima a kashe ni saboda kishin Allah da manzon sa." Ya nagama maganar shi ya juya bayan ya bada umarnin a bude musu k'ofa su futa.
*Tega* ya bishi a baya Yana shinshina m asa jiki: Wani irin salati Granny take yi,lokaci kank'ani jikinta ya kama rawa ganin wani irin jini yana malalowa k'asa daga jikin Mimi.
Kuka ta fashe dashi tana salati ta janye Mimi daga jikinta
Ta mike Da sauri ta nufi kofar futa.
Karo suka buga dashi ya shigo.
Hannunsa ta rike takasa cewa dashi komai sai dai nuna masa gurin da Mimi take kwance take.
Da sauri ya kalli gurin, jini duk ya kwaranya kan tayal din gurin. Wani irin ihu! Ya kurma! Ya saki granny da gudu ya k'arasa gurin Mimi ya dauke ta kamar zautacce yake kiran sunan ta"Momy na."!!!!!!! Ina Mimi bata San wace duniyar take ciki ba, da gudu ya futa daga Palo, mota ya nufa da gudu su Rambo dake tsaye suka bishi, Mujahid ya bude motar da sauri ya shiga mazaunin dravar, jiki na rawa Rambo ya bude masa mota ya shiga rungume da Mimi a jikinsa jini duk ya b'ata shi har ila yau bai daina zuba ba.!!

Da gudu Jahid ya figi motar masu gadi suka bude gate din tun kafin motar ta karaso. Wani irin gudu Jahid yake yi kamar zasu tashi sama, Allah yasa titi akwai saukin motoci kasancewar kowa na gida an sha ruwa an gaji wasu kuma na massalaci suna sallahr tarawi.

Rungume da Mimi yake yana tofa mata duk addu'ar da tazo bakin sa, wasu zafaffan hawaye ne su ka fara zuba a kuncin sa Amjad jarumi ne da kafin kaga kukan sa a duniya sai ka manta ko da iyayansa suka mutu bai yi wani kuka ba, yanzu tsananin tausayin Mimi da irin azabar da take sha akan soyayyar sa yasa shi zubar da hawaye masu zafi, matseta yayi sosai a jikinsa yana tuno maganar ta ta d'azu lokacin da zai futa *"Kar ka futa su kashe ka."!!!!* Innalillahi wa'ina ilahi raji'un. "!!! Abunda ya fada a fili kenan hawaye na zubo mishi wato shi irin tashi kaddarar kenan.

Tun kafin su karasa hospital din Jahid ya kira waya cewar su futo da gado ga emergency nan, aikuwa suna shiga ciki da sauri wasu mata ma'aikata suka turo gado na d'aukar marasa lafiya, ya bude motar da sauri ya zagayo ya budewa Amjad din dake ruk'unk'ume da Mimi dake cikin halin rai da rayuwa.
Futowa yayi ko kallonsu bai yi balle ya saurari abunda suke CE masa, Mimi na rungume a jikinsa ya wuce su. Dr Jahid ya bishi a baya, suna nurses din suka rufa musu baya da sauri.

Likitoci kusan biyar kan Mimi ciki kuwa har da Jahid din sun dukufa domin ceto rayuwar ta.

Yana zaune a reception ya hade fuskarsa da tafukan hannayen sa, kwata-kwata baya so ya bude idonsa ganin irin kallon da jama'ar gurin suke masa, wato yanzu ya zama abun kallo kenan? Tsoron sa d'aya kada Allah ya kawo 'yan jarida gurin, yasan sai sun fed'e biri har hutsiyar ta.
Aikuwa Ko minti talatin bai yi da zama a gurin ba suka shiga su uku. Daya daga gidan redio daya daga gidan television daya kuma daga gidan jaridar Gaskiya dokin k'arfe
Kewaye shi sukayi suna gyara kayan aikin su, ya d'ago kanshi Yana kallon su da idanunsa wanda sukayi wani irin ja!! Babu fargaba a tare dasu tunda a kan aikin su suke .
Daya daga Cikin su yace." Ranka ya dad'e me zaka ce game da zargin da mutane suke maka."? Shiru yayi musu yana binsu da kallo
D'ayan yace." Kuma muna son karin baya ni daga bakin ka, shin zargin da ake maka cewar ka had'a baki da yahudawa domin Ku tuzarta Allah da manzon shin hakane."?
Amjadu yaji wani k'aton bakin ciki ya tokare masa a mak'ogwaro shiru yayi bai ce musu komai ba, kallonsu kawai yake kamar zautacce.! D'ayan da bai yi magana ba shine yace." Ranka ya dade jama'ar gari sun ci alwashin sai sun kashe ka kan abunda ka aikata sai sun k'one gidan ka sai sun k'one company ka, sai sun kona ka, yanzu dai sun samu nasarar k'one company ka kurmus! Ta inda babu wani Abu da zaka Mora a cikinsa, abun mamaki da daure kai kuma sunyi zanga-zanga sun je har inda kake sun kasa aikata Abunda suka yi niyya, gashi kuma yanzu mungan ka a hospital cikin halin damuwa da d'imuwa ran ka ya Dade muna bukatar garin haske a gurin ka.

A jiyar zuciya ya sauke ya mike tsaye da sauri! Suka fara kara masa lasifikar su a bakin sa,
Sunkuyar da kansa yayi kasa hade da soka hannunwan shi duk biyun cikin aljihun wandon dake jikinshi yace." Alhmdullahi Allah ne abun godiya a halin yanzu." Shiru ya rasa gurin, ga 'yan kallo duk sun nutsu
Ya cigaba da cewa"Ban yi niyyar magana daku ba amma dole tasa zan fad'i Abu guda akan wannan k'azafi da akai min, cewar ni *Amjadu Abul Abbas* zan tsaurara bunkice akan mutanan da suka shirya min wannan sharrin, mutukar na kama su, babu shakka dani dasu za muyi kare buri jini dasu, domin sai dai a dauki gawarsu ko a dauki tawa, ni *Amjadu* bana had'a Allah da ma'aiki da kowa, Wallahi wallahi sai dai idan na kashe su hukuma ta kashe ni, duk Wanda zai yi wasa da Allah da manzo to tabbata barin sa a ban duniya shirka CE,idan ban kashe su ba, I promise Sai na raunatasu! Sai na jikkatasu! Sai na sassab'a musu kamannii!!!!!, wannan shine magana ta."!!!
Ya fada yayin da yake wata irin zabura!!!!
Dan jarida d'aya yace." Ranka ya Dade shin baka jin ciwo da bakin ciki akan b'arnar da akai maka, gashi duka duka company ka ko shekara guda bai yi ba shin yake jin zuciyar ka a wannan lokacin."?

Girgiza kansa yayi ba tare da wata damuwa ba yace." Company na da suka k'ona bai min ciwo ba, da sun barshi ma ni da kaina zan zazzaga masa fetur in kona shi, saboda bashi da amfani a gurina, company da ya tara miyagu marasa tsoran Allah a ciki barinsa babban hadari ne, naji dad'i mutuka da suka kona shi. " ya k'arasa maganar sa yana futo da hankici daga aljihunsa ya goge fuskarsa.
Chapter 45 · 0% Book details