Sashe 46
Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 8 min read
Daya Dan jarida ne yace." Ranka ya Dade sai tambaya ta k'arshe kayi hakuri muna son muji me ya kawo ka asibiti gashi dai a zahiri jikinka babu ko kwarzane babu jini balle ace ko daga gurij mutanan da suka kai maka har....... Kafin ya karasa maganar shi ya katse shi ta hanyar fadin"My wife dina tana ciki cikin halin rai da rayuwa duk ta dalilin wannan ibtila'in babu abunda zan ce sai dai Allah Ubangji ya saka mata ga dukkanin mutanan da suka shirya faruwan hakan.""""""Yana gama maganar shi ya maida hannun sa fuskar sa ya rufe ruf! Yana kukan zuciya
Duk wani mai imani da tausayi a lokacin zai tausaya masa mata masu rauni tuni sun soma zubar da hawaye, jiki a sanyaye 'yan jaridar suka masa sallama suka futa.
Dukanin abunda yake faruwa bamu da labari mun dai ji labarin yanda mutanan gari suka k'one company ya Aminu ya kawo mana video mun gani a wayar abokinsa garba har yanzu Umma kuka take yi tana tunanin wane irin hali Mimi take ciki dashi kanshi Amjadu din, domin da har ta dauki mayafi zata futa Ya Aminu ya hanata da sauri yaje ya kulle kofar waje da kwado domin rigima muke da ita wai sai ta futa taje gurin su Mimi.
*****
Yana zaune a gurin shi kadai sai gilmawar nurses da d'aid'aikun marasa lafiya da suke shigowa asibitin.
A gogon hannunsa ya kalla K'arfe goma shaura, cikin tararrabi da tsinkewar zuciya ya mik'e tsaye yana kallon room din da aka shiga da Mimi ciki.
Kai tsaye ya durfafi d'akin baya ko kallon gabansa.
Karo suka buga da Jahid ya futo daga dakin hannunsa sanye sa safa, duk ta b'aci da jini.!! Wani kallo yayi masa yana bin hannunsa da kallo cikin fad'uwar gaba.!
Jahid ya gyara yanayin fuskar sa, cikin rashin kuzari yace.''tana bukatar jini cikin gaggawa."!! Amjad kokari yake ya bangaje Jahid ya shiga dakin.
Jahid ya tare hanya cikin sigar rarrashi yace." Colm down Aboki tsaya ka saurare ni tukkuna." Cikin damuwa da fargaba yace." Muje ka sanya mata nawa jinin kar Ku kashe min matana."!!! Muryar shi na kyarma ya k'arashe maganar tasa."
Jahid ya rike hannunsa ba tare da ya damu da jini da. Yake hannun nasa ba ya damk'e sosai yace." A halin yanzu bani da masoyi sama da ita bani da kowa sai ita da abunda yake Cikin ta sai granny su kadai suka rage min a duniya my friend bana so in rasa Momyna."!!!!! Tsabar tausayi ta hana Jahid cewa komai ya ja hannunsa suka shiga wani d'aki.
A gigice Ya Aminu ya shigo gidan Hannunsa rike da wayar Garba abokisa.
Kamar dai d'azu da ya shigo mana da ita, duk ya rasa inda zai tsoma ransa, ya mik'o min wayar bakinsa na kyarma yakasa cewa komai
Hannu na rawa na fara dubawa
Farko abunda na gani ya sani kurma wani ihu na jefar da wayar hanna hannu na d'ora aka ina fad'in "Innalila wa'ina ilahi raji'un, shikkenan sun kashe mana Mimi mu."!!!!!!
Umma ta dauki wayar da sauri tana dubawa, Mimi ce rungume a hannun Amjadu lokacin da suka shiga asibitin nasarawa abunka da mutumin da yayi suna a duniya aka samu wasu suka dauke su vedio a wayoyin su, a lokacin suka fara turawa Media hade da sharhi cewa jama'ar gari sun shiga har gidan *Young millionaire* sun Sassari matar shi mai dauke da ciki Dan wata shida gashinan tana halin rai da rayuwa.!
Abunda ya k'ara tayar mana da hankali shine yanda mu ga jikin Mimi dashi kansa Amjadu din duk ya b'aci da jini duk da cewar dare ne amma akwai hasken fitulu a ko ina na asibitin.
Umma ta mik'e tsaye cikin tawakkali ta kalli Ya Aminu da yayi tsaye a gurin duk ya rasa me zai yi tace" Muje mu gani Aminu Mimi tata kaddarar kenan, bawa baya wucewa kaddarar sa, muje idan ta mutu ne sai mu karbo gawar ta."
Hawaye Ya Aminu ya share ya futa daga gidan da sauri domin samo abun hawa.
Ni da Umma muka futa daga gidan kamar wasu zautattu! Shi kanshi hijab din dana sa a baibai na sanya shi, hawaye ne kawai yake zura ra a idona shikkenan Mimi sai ta Allah a yanda na ganta ina gani kamar kafin mu Isa a sibitin za'ace ta mutu.
*24/11/2019*
[11/25, 8:46 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*MALLAKAR_ BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*
*62*
Lokacin da muka Isa asibitin goma da rabi ta wuce, Dan dai ma daran azimi ne akwai jama'a a bakin asibitin suna siye da siyarwa, har ciki mai a dai-dai ta sahun ya shiga damu, Ya Aminu ya biyashi kud'in sa, ni kam tuni na Dade da futowa daga a dai-dai sahun sai kyarma jikina yake yi.
Ko da muka shiga ciki babu mutane sosai wasu kujera muka samu muka zauna. Ya Aminu ya nufi wani d'aki da sauri.
Waya ta dake hannuna na kunna na fara Neman numbar Jahid, sai da na kira sau biyar a kashe, cikin mutuwar jiki na aje wayar a cinya ta, Ya Aminu ya futo daga dakin da ya shiga ya nufo mu, fuskar sa babu walwala
Gaban Umma ya tsaya yace. "Yanzu wata nurse take min bayani cewar Mimi tana ciki har yanzu ba'a futo da ita ba, kuma abun mamaki na dauka zamu samu mijin nata anan gurin bab........ Kafin Ya Aminu ya rufe bakin sa, Jahid da Amjadu sun futo daga wani d'aki. Da sauri Jahid ya k'araso gurin mu. Shi kam Amjad yana tsaye a gurin da yake.
Jahid ya kalli Umma tare da fadin" Ashe har kun samu labari."
Umma tace"Ba dole ba wannan tashin hankali dai Allah ya sawwake, mana shi, yanzu ya jikin Mimi yake. "!!?
Jahid yace." Jikinta Alhmdullahi Umma ku kwantar da hankalin Ku, jini ake bukata sosai za'a kara mata saboda ta zubar da jini sakomakon fad'uwar da tayi."
Mik'ewa nayi zumbur nace"Muje ka sa mata nawa jinin kaji Don Allah ka cece rayuwar ta." Murya ta na rawa na k'arashe maganar.
Jahid yace." Dole haka za'ayi muje a dauka a auna mu gani, idan yayi dai-dai sai a d'aura mata yanzu ma an d'ibi na Amjadu ne."
Kallon shi nayi dake tsaye kamar wani maraya sai ya bani tausayi mutuka wata zuciyar tace ba abun tausayi bane mutumin nan.
Wani daki muka shiga da Jahid ya dauki jinina ya duba yayi dai-dai Dana Mimi take ya umarce ni na kwanta kan wani gado domin ya dauki jinin.
Amjad kuwa jingina yayi jikin bango hade da lumshe idonsa Sam ya kasa zuwa ma ya gaishe da Umma saboda halin masifar da yake ciki.....Muryar Granny yaji ta shigo gurin cikin kuka take fadin"Sai da tace kar ka futa kar ka futa ka futa gashi da ka futa ka dawo sumul k'alau! Da kai ita kuma saboda tsananin son da take maka, ta fadi kan cikin ta."!
Komai a kunne magangan da granny take yi domin dakin da nake ciki a bude yake, Jahid na kalla Ina daga kwance nace "Nasan kasan dukanin abunda ya faru don Allah ka fad'a min komai."?
Ba tare da tunanin komai ba Jahid yace." Wallahi Asma'u tsautsayi ne ya afka kan Mimi lokacin da abun ya afku, tana hana Amjad din futa saboda jama'ar garin da suka kawo masa hari har gida, garin kokarin rik'o rigar sa, kawai santsi ya kwashe ta ta fad'i kan cikin ta to shine fa take ta zubda jini, amma insha Allahu zata dawo normal.
Murya ta a cunkushe nace"Kana nufin ya sane ya futa bayan tace masa kar ya futa yanzu me futar tashi ta jawo mana, ai dai gashinan da kunnen ka kaji Abunda kakar shi take fad'a ko." ? Jahid ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Tsautsayi fa baya wuce ranar sa, don Allah mu bar maganar bana so Ku Dora alhakin abun kan shi." Shiru nayi ganin ranshi ya b'aci Jahid yana da saukin kai da dad'in mu'amula amma baya son musu da taurin kai shiyasa nayi shiru kawai amma cikin zuciya ta nayi alk'awari sai na fad'awa guy nan magana a kan Mimi komai daran dad'ewa kawai don yaga tana da hakuri sai ya dunga gara ta kamar gare-gare kullum cikin damuwar sa, da bata mata rai.
Jini Leda biyu a kauda a jikina nan Jahid din yace min na kwanta kan gadon na huta mintuna talatin, INA kallon shi ya futa daga d'akin. Granny ce ta fad'o dakin tana kuka tana k'ara tisa maganar da abunda ya faru. Fad'i take "wannan yarinya Ubangiji Allah ya tashi kafad'unta amma babu shakka tana shan wahalar rayuwa. " Shiru nayi mata kawai ina bin ta da kallo.
Amjadu masjid ya nufa domin yin sallah istigufari kawai yake a fili da Cikin zuciyarsa. Ta shi nayi jikina babu kuzari na futo daga dakin, har yanzu su Umma na zaune cikin sauraron hukuncin Ubangiji, kusan awa guda da shigar Jahid dakin da Mimi take ya futo, kallon mu yayi ya kalli a gogon hannunsa sha biyu na dare saura minti ashirin, futa yayi ya nufi gurin Amjad dake cikin mota
Amjad yace." Ta farko ko."? Daga kai Jahid yayi a hankali yace "Alhmdullahi ta farko kuma munyi nasarar tsayar da jinin insha Allahu an sanya mata, shi gobe dole za'ayi scanning din cikin domin ganin wane hali yake ciki.
Sunkuyar da kansa yayi cikin tawakalli yace." Allah ya kaimu lafiya Jahid ina cikin halin damuwa ina bukatar rarrashin." Kafadunsa ya dafa yana rarrashin sa da kalamai masu sanyi.
Amjadu Rambo ya sanya ya je can *Mai takobi* ya karb'o nau'i kan abunci da abun sha, duk ya sanya ya shiga dasu gurin mu, tsabar damuwa da fargaba bata bari munci komai ba, ko da asubah ruwa kawai muka sha fafur abunci yak'i samun shiga a gurin mu, Ya Aminu dama ya tafi gida ni da Umma ne kawai sai granny