Sashe 10
Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 5 min read
Shi kuwa bayan shigewar ta dariya ya kama yana mamaki wai shi Granny zata bawa maganin k'arfi hummm! Yana zaune ta futo dashi cikin Leda viva sabuwa dal, dauru kusan ashirin ya karb'a yana dubawa, dauri daya ya dauko yana sansanawa, cikin haushi da takaici tace"Meye haka kuma zaka haramtashi fa." Cikin dariya yace." In na haramanta ma ai ni nawa ne kuma ni zan sha." Tace" To fasa dauri daya kasha a gabana." Aikuwa ya fasa hade da zukewa yace." Idan cikina yayi ciwo kece kin yadda." Tace"Na yarda wannan maganin bazai saka ciwon ciki ba sai dai ma ya gyara ka." Yace." Naji to zauna muyi magana dake."
Granny ta zauna kusa dashi.
Yace." Neman aure zanje fa."
Granny tace." Alhamdullahi yau Allah ya kawo ni wannan lokacin. "
Gyad'a kansa yayi yace." Mata biyu zan aura ya kika gani. "
Shiru tayi tana nazari daga bisani tace"Ai Matsalar Ka ce abun ji." Murmushi yayi yace." Kar kiji komai duk zan iya dasu.
B'ata fuska tayi tace"to naji amma dai ta biyun Hafsa ce ko."?
Yace."Wacece Hafsa kuma."? Tsaki taja tace"Kamanta kenan kana so ka hadani da Innar ka kenan? Dama suna cewa sai abunda nace dakai kake yi baka zumunci dasu dukiyarka baka Mora musu sai dai su ji a gari."
Shiru yayi kawai domin shi kanshi ya San baya kyautawa Sam baya ziyartar dangin mahaifiyar sa, sun gani da korafin sun hak'ura dole yanzu ya gyara ko don kada duniya ta zage shi, Granny ya kalla yace." Yanzu yaya kike so ayi. "? Zama ta gyara tare da fadin" Kaje ka nemi auran Hafsa yarinyar na da kirki kuma tana sonka." Ya mutsa fuskar sa yayi wannan bukatar ta granny baza ta yi wu ba, yace." Kiyi hakuri Granny bana so ayi Abu daga baya azo ana da an sani kin fi kowa sanin halina bana rufa-rufa yarinyar bata yi min ba, zan dai yi kokari gurin ganin naje mun gaisa dasu kuma zanyi musu alkairi sosai."
Ajiyar zuciya ta sauke tare da fadin "Shikkenan to Ubangiji Allah yayi maka zab'i na alkairi "
"Ameen yace yana kallon agogon dake daure a hannunsa.
Mik'ewa yayi yace." Insha Allahu komai ya dai-dai ta zamu je ki ga kawayen naki ko kuma in ce kishiyoyin naki." Tace",Allah ya kaimu yanzu ma ace dasu ina gaishe su."
Har ya futa ta bishi a bays hannuta rike da ledar magani tace." Ka manta kuma." Shiru yayi yana nazari,hannu ya mik'a ya karb'a sukayi sallama ta koma gida
Mota ya bude ya zura ledar maganin kusa dashi ya zauna sosai hade da kunna motar mai gadi ne ya mik'e da sauri ya bude masa Gate ya futa daga gidan.
Kai tsaye,....... Gidansu Asma'u ya nufa.
*5/November/2019*
[11/6, 5:13 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*Mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*
*42*
Yana tafe cikin mota yana sauraron wak'ar Joy mutumin shi, gyada kansa yake da alamun Yana jin dadin wak'ar, sai da ya kusa shiga unguwar tasu ne ya kira Mimi a waya, lokacin muna zaune a tsakar gida bayan mun gama cin abunci muna ta fama da wasu shegun cinna ku da suka addabe mu, dama duk lokacin damuna haka suke futowa a gidan ta cikin ramuka suyi ta cizon mu. Wani ne ya cije ni a hannuna ina ta faman sosawa hade da haska gurin da toch din wayar Mimi neman sa nake in kashe, kira naga ya shigo wayar *Heartbeat* abunda na gani kenan, siririn tsaki naja hade da mik'a mata wayar ta karba hade da tashi daga gurin, Umma ta bita da kallo tana girgiza kanta. Minti uku sai ga ta ta futo da wayar a hannu tana sink'e kai Umma tace "Waye ya kira ki harda barin gurin."?
A hankali tace" Amajad ne, yazo Umma." Sakin fuska tayi tace" To masha Allahu, alamu sun nuna ke yake so, tunda gashi ya kira ki a waya yazo zance maza je ki shirya Ubangiji Allah ya sanya alkairi." Umma ta k'arashe maganar cike da murna da farin ciki.
Mimi ko kunya ta shiga dakinmu da sauri, sai abun ya bani mamaki ganin d'azu take kuka tana cewa ta hak'ura dashi ta barmin amma dubi yanda take rawar kafa saboda zuwan sa. Ni dai shiru nayi kawai, har ta futo Cikin shiri sai zabga kamshi take. Tace"Umma sai na dawo." Umma tace." Ki gaishe shi da kyau kuma ki iya ladabi da biyyaya." Tace"To tana k'okarin futa sai farin ciki take.
Hira muke da Umma sama-sama nake jin ta domin a lokacin bana cikin hayyacina wani irin lami bakina yayi sai kace mace mai yaron ciki haka nake jin wata irin kasala da sagewar gwiwa jiki babu k'wari na shige dakinmu hade da fadawa kan katifa ruf da ciki rumtse idona nayi sam zuciya ta babu dad'i ni kadai nasan abunda yake damuna.
Parking yayi bakin hanya hade da kunna Fitilar wayar sa, unguwar duhu dumd'um!! Sai hasken masu ababen siyarwa dake kan hanya, masu charge masu wanki da guga, masu provision da sauran su, yaji dadin haka domin baya son ya futo har jama'a suka gane shi, wayar Mimi ya kira hade da fada mata gashinan ya iso. Lokacin tana kan hanya. Inda ya Saba parking ta nufa cikin yanayin tafiyar ta tsallaka titi tayi ta isa kusa da motar hade da d'an kwankwasa wa, a hankali ya bude motar tare da haske fuskar ta da wayar hannunshi, sakin Fuska yayi yace." Momy na tafi ta kowa." Mimi tayi wani fari da ido. Yace." Shigo ciki mana." Cike da kunya ta shiga motar ya mai da murfin ya rufe. Kashe ta yake da kallonsa na goggun 'yan duniya, sunkuyar da kanta take tana fadin"Sonka zai iya kashe ni." Cikin zuciyar ta tayi maganar
Yace." Bamu gaisa ba Momyna kunyar ki na bani mamaki tana d'aya daga cikin abunda yasa naji kin kwanta min a raina"
Mimi tayi murmushi yace." Ok ni ne yafi kamata na gaishe ki tunda nine danki. Kinga kuwa dole in nemi albarka." 'Yar dariya tayi sai kace sokuwa, tace"Ina wuni"?
Cikin sangarta yace." Umum!! Nine zan fara gaishe ki." Mimi taji kamar tana yawo kan gaji mare don shauki gaskiya guy nan ya iya love.