← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 38 OF 60

Sashe 38

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 7 min read

Mimi da tsayuwa gurin ta gagare ta saboda jiri ta bude motar da sauri ta shiga, kallon ta. Nayi ina girgiza kaina, saboda kar ya fuskanci wani Abu yasa na bude motar na shiga na zauna kusa da ita yaja motar muka tafi

Rambo da doh da suke tsaye suna kallon duk abunda yake faruwa suka koma gurin zaman su, dama sun taso ne saboda su cika umarnin ogan su.

Rambo ya dauki wayarsa ya fara Neman numbar ogan shi. Bugu guda ya dauka, inda yake akwai hayaniyar mutane yasa yace da Rambo ya kashe wayar zai kira shi anjima Rambo ya kashe wayar kamar yanda ya fad'a, doh yace." Tunda ka kira zaka yi masa bayani ya kawo uziri shikkenan nasan ko kayi masa baya ni daga baya zai gamsu, Rambo yace." Ni tsoron fad'an mutumin nake ji, akwai abunda na fuskanta game dashi da yarinyar nan." Doh yace." Nima haka Asma'u yana masifar sonta, Allah bai kaddara matar shi bace." Rambo da doh-doh suka dinga gulmar ogan nasu.

Asibitin nasarawa muka nufa, ba tare da b'ata lokoci ba, Mujahid ya sanya nurse ta dauki fitsarin Mimi a wata 'yar kwalba domin auna shi, muna zaune a ofis din sa, Sam yak'i duba marasa Lafiya wai lallai sai ya sallame mu, Kusan mintuna talatin sai gata ta shigo fuskarta a sake tace." Dr sakamako ya nuna positive tana dauke da ciki na sati biyu." Dr Mujahid ya saki murmushi yace." Alhmdullahi dama abunda nake tsammani kenan. "
Nurse ta futa tana 'yar dariya, ni da Mimi kuwa kallon juna muke yi, nace "Mimi Allah ya sauke ki lafiya."
Gani nayi idonta yayi rau-rau za ta fara kuka, saurin dauke kaina nayi daga kanta.

Mujahid kuwa dariya yake mata yana tsokanar ta, wai ko ta soma tunanin ranar haihuwa ne, ita dai bata ce komai ba.
Wayarsa ya dauka yana fadin"Ni zan fara yiwa mutumina albishir sai ya fara kiran wayar Amjadu, gabana ne ya fad'i nasan wata masifar ce,tunda mutumin nan yace babu ruwan sa, dani kar in kara shiga harkar shi, ya nuna baya so Dr ya duba mishi mata. Shuru dai nayi kawai INA l sauraron abunda zai biyo baya.

Mujahid da dariyar sa suka gaisa dashi, naji yana tambayar sa gida da sauran mak'otan sa, yace kowa Lafiya Lou sannan yace." Dama na kira ne ka bani gurin albishir. " yana dariya ya fad'i. Maganar. Sam bai kawo komai cikin ransa ba, kuma bai taba tsammanin za su bujurewa umarnin sa ba yace." Kome kake so zan baka."
Yace." Madam na dauke da ciki insha Allah ka kusa zama dady yanzu na sanya aka duba ta." Wani irin nauyi yaji a kansa, lokacin da Mujahid yake wannan maganar, Mimi na dauke da cikinsa, har yaushe daran yayi balle gari ya waye, dududu sau nawa ya kwanta da ita har ta dauki cikinsa. ? Shuru yayi Mujahid yace." Kayi shiru ko baka murna ne."

Da sauri yace." Wane ni, kawai ina mamakin hukuncin Allah ne, nagode K'warai Aboki bani Madam din." Mujahid yace." Babu godiya a tsakaninmu domun mun zama daya dakai ina fatan alkarmu dakai ta dore har a bada."

Mimi ya mik'awa wayar yana fadin "Ga mijin ki za kuyi magana dashi Mimi ta karb'i wayar jikinta a mace tunda akace tana da ciki tayi lak'was.
Muryarsa sama-sama naji yana fadin"Ya jikin naki."?
"Bakinta na rawa tace" Da sauk'i. "
"OK Allah ya sawake ki kula da kanki." Abunda yace kenan ya kashe wayar sa. Mimi ta mik'awa Dr wayar jikinta duk babu k'wari na dauka ma zai yi mata masifa sai naga a kasin haka, ni kaina banji dadin yanda ya ki nuna kulawar shi kan Mimi ba, ko wane namiji akai mishi albishir da matar shi na da ciki yana sakewa yayi ta murna, amma shi magana a cunkushe, Itama na lura bata ji dadin abunda yayi ba.

Dr Mujahid shine ya mai damu gida yana bayan ya hadawa Mimi magunguna dole yace ta zauna ta samu Hutu cikin ya danyi k'wari sannan.

Granny na zaune ita kadai a parlor tana kallo muna shigowa tace "Naji dadin dawowar Ku da ina zaune ni kadai kamar wata mayya, Dariya nayi na zauna kusa da ita cikin gajiya tace." Ina fatan dai komai lafiya nasan dai ciki ne da ita."

'Yar Dariya nayi nace"Eh ciki gareta Dr ya bata magungunan Karin jini kuma ta kula sosai da jikinta."

Wani irin farin ciki naga granny tana yi sai washe baki take yi tana fadin"Allah na gode maka 'yar nan ubangji Allah ya sauke ki lafiya naji dadin wannan al'amari dole zama ya kama ni a gidan."

Tausayi tsohuwar ta bani ganin yanda take murna da farin ciki. Na kalli Mimi wacce take ta b'oye k'walla ko ta mecece oho mata.

Bayan sallah azhar nayi musu sallama babu yanda basu yi dani ba kan in zauna in ci abunci naki zama.
Ko da na koma gida Umma har ta sauke nata,zama nayi rumfar ta ina ci muna hira nan nake fada mata Mimi ciki gareta, itama murna take sosai har da 'yar kwallar ta.
Ni dai mamaki nake ko kwallar me suke yi oho.

**********

Kullum Mimi sai ta kirani a waya tana min magiya kan naje gidan ta wai na taya ta zama kafin ya dawo wataran sai na zage ta sannan muke dai-dai tawa da ita. Wataran ma kin d'aukar wayar nake yi.

*******

Yau watan Amjadu Uku a chana Wanda yayi dai-dai da watanin auran su da Mimi komai yayi masa yanda yake so, don haka sai ya fara shirye-shiryen dawowa gida.

Lokacin kuma Mimi tana fama da Matsalar ciwon ciki matsananci Dr Mujahid shine tsaye a kanta scanning anyi mata sau biyar kullum Abu guda yake nunawa Cikin Mimi na zaune a bayan mahaifa Mujahid ya tsorata mutuka duk scanning din da zai sanya ayi mata zai nuna masa twins amma ko gurin wanne kwanciyar daban, daya cikin mahaifa daya a waje Innalillahi wa'innailahi raji'un.

Duk wannan fad'in tashin da muke yi Sam bai sani ba domin Mujahid yace kar Wanda ya fada masa, Ni kad'ai ya fadawa abunda yake faruwa nima tare da gargadin kar in fadawa kowa saboda kwanciyar hankalin su duk da haka granny tayi mugun tada hankalin ta, saboda ta Dora wa cikin Mimi son duniya.

Tuni na tare a gidan Mimi kusan wata guda kenan muke cikin wannan tashin hankali Mimi ta fige tayi wata shegiyar rama sai uban haske gashi bata cin abunci sai nayi da gaske sannan take ciki ko kuma taga raina ya b'aci kullum da daddare ta dinga murkususu kenan Cikin ta, kuka nake yi sosai ina mata addu'a.

Ganin halin da take ciki yana kara yin gaba, ya sanya Dr tununin Sanar wa da Amjadu dole kome yake yi ya aje ya dawo gida domin duba halin da gidan yake ciki, Duk da cewa kullum yana kiran waya safe da dare amma kira da ban zuwa daban, Dr yana ganin dole ayi mata aiki shine za'a samu maslaha. To ko da ya kira Amjadu din a waya ya fad'a masa abunda yake faruwa bai wani nuna damuwar sa ba yace." Insha Allah yana kan hanya.

Zaman mu guri guda da Mujahid ya sanya wata matsananciyar soyayya ta shiga tsakanin mu, gani nake yanzu nake soyayya Mujahid ya cika mutum mai kyawun hali da tausayi tabbas duk macan da ta aure shi tayi dace da miji na saki jikina sosai dashi, domin shine yake kaini makaranta cikin motar shi kullum, siyayya kuwa babu irin wacce baya min, har yaron shi sai da ya kawo min ya yini a gurini
Grnay tayi ta tsokanar sa, sai dai yayi dariya kawai.

Ina dawo wa daga makaranta granny take fada min yau Mai gidan zai dawo domin yayi waya bayan futa ta yace." Yana jirgi, shikkenan na nemi nutsuwata na rasa domin Sam bana kaunar abunda zai sake hada ni dashi, tunanin hada kaya na nafara yi domun ina gudun cin mutumcin da zai yi min a gidan shi....

*20/11/2019*
[11/21, 10:38 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*MALLAKAR_ BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKINA NE KUN BIYA KUDIN KARATU NE KAWAI DUK WACCA TASAN ZATA CI MIN AMANA TA FUTAR MIN DA LITTAFINA TO TUN WURI TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA, GASKIYA DAYA CE, HAKA MA AMANA DAYA CE DUK WANDA YACI TA SAI TA CI SHI*

*58*
Chapter 38 · 0% Book details