Sashe 15
Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 8 min read
Nace "Umma kina da ta cewa mana don Allah ki sanya Ya Aminu ya janye magana.....kafin in karasa naji saukar Mari a kuncina Ya Aminu ne tsaye a kaina yana wani irin huci! Yace." Kina so naci ubanki Asma'u, wato kina zu ga Umma kina zuga Mimi kan su bujirewa Bukatata ko me? Ni kinsan halin da Zan shiga idan na rasa ta, ko kinsan irin son da nake mata, mutukar ina Raye a duniyar nan bani da mata sai Mimi, dake da ita kuje kuyi abunda zakuyi akin gama ya Riga ya gama."
Yana gama maganar shi ya fuce daga gidan a fusace!
Umma barin gurin tayi ni da Mimi mukayi shuru muna sak'e-sak'e
A hankali naji tace"Asma'u don Allah kar ki kara wata magana kan al'amarin nan, kinji tunda dai kince zaki taya ni addu'a tom na gode miki.".
Murya na rawa take maganar
Nima naji zuciyata ta karye nace"Mimi sai dai idan gani nayi am d'aura muku aure da Aminu shine zan daina magana domin nasan ki nayi a banza ne, bakin alkami ya bushe, amma magana kan al'amarin yanzu na fara."
Shiru tayi tans kallona.
Mik'ewa nayi na futa daga dakin zuciya nayi min zafi!
*RANA BATA KARYA*
Manyan attajirai da manya manyan 'yan boko 'yan siyasa masu mak'ami daban-daban Sarkin Kano sarkin Zazzau Sarki Katsina Jama'ar gari tsakunsu da kwarkatar su, sun hallara a wannan guri.
Hayaniya ce ta tsananta tare Da jiniya wannan ya tabbatar min da cewa me girma governor ne ya iso bani kadai ba, duk wani Wanda yasan da akwai dabi tsakanin *Amjadu* da me girma *Governor* sai da yayi mamaki, tuni jama'ar gari suka fara ihu!! Suna fadin abunda ransu yake so ga me girma governor.
Ko kunya babu me girma governor ya futo daga mota tare da jamarsa ya dinga ratsa jama'a Yana daga musu hannu hade da washe musu baki wai shi lallai ga governor tsagerun matasa masu goyon bayan Amjadu suka sanya ihu!! Da dariya suna fadin abun da yayi musu kan governor din, wasu na fadin"Ba mayi!!!! Sai da 'yan sanda suka tsawa tar sannan hayaniyar ta lafafa, can gurin da aka tanadar wa manyan baki governor ya nufa, police na biye dashi a baya domin sun tsorata da irin ihun da jama'ar gari sukeyi,
Sai da suka ga ya zauna sannan suka koma gefe suka tsaya da bundigun su a hannu.
Can na hango Mai citta shida abokanan shi, sai zare ido suke.
Limamin babban massalacin jama'a na garin kano ne ya tashi ya bude taro da addu'a yayi karatun alkur'ani me girma sannan daya baya daya manya baki suka fara jawabi kowa yana yaba kwazo da jajircewa irin ta Amajdu
'Yan jarida a gurin baza su kirgu ba, domin wasu jamar gari na gida kowa na gaban TV Wanda bashi dashi kuma kunne shi mak'ale da waya ko redio yana saurara.
Lokacin da Amjadu ya futo zai yi Jawabi Ihu!! Jama'ar gari suka sanya tare da fadin"Sai kayi fari me farar aniya ka iya ka huta *AmjaduAbulAbas* muna biye da kai insha Allahu *2004* taka ce sai ka zama shugabanmu." Ihu! Kawai suke, sun hana aji bayanin da yake, da kyar jami'an tsaro suka shawo Kansu suka yi shiru.
*Amjadu* yayi jawabi me gamsarwa jawabin da ya ratsa zukatan al'umma Su Kansu manyan gurin sun jinjina masa kuma sunyi masa fatan alkairi.mai Martaba Sarki yaji dad'i sosai da samun hazikin Yaro a garin shi yana mutukar alfahiri da shi.
K'arfe goma sha biyu da rabi taro ya watse saboda ranar juma'a ce za'a tafi massalaci, nan Amjadu ya bada sanarwar cewa jamar gari suje massalaci su dawo bayan an idar da sallahr za'a bude company daga nan har zuwa goma na dare.
Haka akayi kuwa bayan an sakko jama'a sukayi ta tururwa company suna kwasar garabasa.Sai k'arfe daya na dare sannan aka samu saukin Jama'a.
*****
Duk abunda yake faruwa a gari muna da labarin shi munji a redio Kuma mun gani a TV dake ranar sun bar mana wuta, abun mamaki Mimi yini tayi tana farin ciki.
Amjadu ya sha addu'a gurin Umma, aunty Hauwa ma ba abar ta a baya ba, kusan a dai-dai ta sahu guda tayo da kayan da bata koma gidan ta ba sai bayan sallahr Isha'i.
Ni ko tunda nayi masa kallon farko a TV ban sake kallonsa ba daga k'arshe ma tashi nayi na bar gurin naje na tsiri ninkin kaya ina tunin yanda Allah ya dauka kashi a duniya 'yan da yake da kyauta da son talaka da yanda yake da farin jinin jama'a, yanda yake da ibada, amma yana aikata sabon Allah domin zina mugun aikine Wanda Allah ya hana shi, kawai sai na tsinci kaina da yi masa addu'ar shiriya naji wani irin tausayin shi, babu uwa babu uba ga makiya da d'umbun masoya gaba da baya, Allah ne kadai yasan abunda zai zama nan gaba, a fili nace"Ubangiji Allah ya kare ka daga sharrin ma su sharri Allah ya shirye ka shirin addinin musulunci yasa ka daina aikata zina."
******
Yau sati guda kenan da faruwar al'amarin Wanda yayi dai-dai da kwanaki goma da afkuwar al'amarin Auran mu komai ya dai-dai ta, tun ranar da ya kira wayar Mimi na kashe ban kara kunnawa ba sai yau, sun kawo wuta na jona ta a chaji.
Mimi ta shigo dakin jikinta babu k'wari ta zube kan katifa.
Binta nayi da kallo. Nace"Mimi kinga yanda kika rame kuwa."?
Shuru tayi min
Nace"Wallahi Ki yiwa kanki fada ni yanzu kin daina bani tausayi haushi kike bani wallahi, wai Amjadu shi kadai ne namiji a duniyar nan."
Shiru dai tayi min bata ce min komai ba.
Tsaki naja na futa daga dakin.
***
Tun lokacin da ya kira wayar yaji an kashe bai Kara kira ba yasan Mimi baza ta kashe masa waya ba.
Tabbas Asma'u ce shiyasa bai kara kira ba.
Yana zaune gefan bed da wayar a hannunsa numbar ya kira sai yaji ta shiga har ta katse ba a dauka ba, kira ya kara yi a karo na biyu nan ma ta katse ba a dauka ba, a je wayar yayi hade da Jan tsaki a fili yace." Mata masu aji kenan." Mik'ewa yayi ya futa parlor.
Mimi na kwance a dakin lokacin da yake kiran wayar tarin da take ne ya hanata d'aukar wayar har ta katse.
Cikin wani irin mugun tari da galabaita ta mike zaune hade da dafe k'irjinta tana cigaba da tarin sosai wa
[11/8, 6:21 PM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*
*Mallakar_BINTA UMAR*
*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*
*45*
Ni da Umma muka shigo dakin da sauri!
Mimi na durkushe ta rike k'irjinta tana ta tari.
Da sauri Umma taje ta rike ta ni kuma ns dauko ruwa hade da fasawa na dago kanta ina bata, k'arfin tarin ya hanata ta karb'i ruwan.
Umma tace"Maza kije ki dauko gishiri a kicin.
Cikin tashin hankali na nufi kicin din na dauko ledar gishiri
Umma ta dangwala a hannuta ta sanyawa Mimi a baki tana Dan bubbuga bayanta hade da yi mata sannu.
Mimi idonta ya rufe sosai take tari! Da haki tare da hawaye.
Ni da Umma duk mun shiga tashin hankali.
Nace"Wallahi Umma jiya da daddare haka ta dinga yi da kyar tayi bacci."
Umma tace"Ikon Allah watak'ila busawar sanyin nan ne,.
Nace"Ina jin hakane " cikin ikon Allah tarin ya lafa sai dai haki da take yi.
Umma ta rungume ta a jikinta tana yi mata sannu
Ya Aminu ne ya shigo dakin ya tsaya bakin kofa fuskarsa s daure yake tambayar menene?
Umma tace"Mimi ce babu Lafiya in anjima ka siyo mata maganin tare saboda dare."
Wani irin kallo yake wa Mimi daga bisani kuma ya tab'e bakinsa Yace. " Umma ki rabu dasu duk karya ne,nasan wannan'yar iskar ce take zugata."
Umma ta bata fuska tare da fadin"bana son wannan halin naka Aminu ina ruwan Asma'u anan.?
Futa yayi daga dakin ransa a bace.
Nace"Umma shifa bazai taba ganewa ba tunda ya samu ya kubuta Mimi CE abun tausayi.'
Shiru Umma tayi min, sai da taga Mimi tayi bacci sannan ta gyara mata kwanciya ta futa daga dakin jikinta duk babu k'wari.
Kallon Mimi nake gwanin tausayi duk ta rame tayi Dan wuya k'irjinta sai sama yake yana kasa alamun tana jin jiki.
Jikina babu k'wari na kwanta kusa da ita ina tunani
Ringing din wayar naji wacce take jone a chaji na mike da sauri hade da dauka
Babu sauk'i a murya ta nayi sallama
Ajiyar zuciyarsa naji a hankali yace." Ya kike mata masu aji."!! Sama nayi da murya ta nace." Ina nan kallo kamar tsumma a randa, amma kasan da cewar zuciyar da ka yaudara da sunan so kake azabtar da ita tana cikin gararin rayuwa tana cikin halin ha'ulai kullum bata da sukun hawayen idonta ya kasa daina zuba....... Katse ni yayi kafin in karasa magana ta yace." Wannan wace irin banzar magana kike min kina yi kina daga murya kamar kina yi da sa'an ki, kiyi min magana yanda zan fahimci me kike nufi ."
Haushi maganar shi ta bani saboda haka nace "Da Hausa nake maka magana ba da harshe nasara ba, nace" D'aya zuciyar daka yaudara tana cikin halin ha'ulai da damuwa saboda haka in ta shiga mugun hali to kai ne sila."
Lokaci guda ya fahimci inda maganar ta ta dosa.
Babu ya bo babu fallasa yace." Bani Momyna mu gaisa. "
A hasale nace"Ya ina yi maka magana daban kana yi min wata maganar, Mimi dai na bacci Wanda muka samu ya dauke ta da kyar don haka bazan tashe ta."
Na k'arashe maganar tawa a kufule!
Wannan karon akwai sassauci a muryarsa yace." Nace kiyi min bayani dallah-dallah yanda zan fahimta ni har yanzu ban gane abunda kike nufi ba."