← Book details Babban Yaro Part 2 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 21 OF 60

Sashe 21

Babban Yaro Part 2 Complete Hausa · about 8 min read

Kai tsaye......Asibitin Zana ya nufa zuciyarsa kwata-kwata babu dad'i abun yana mutukar bashi mamaki shi dai yasan babu wata Kalmar so da ya tab'a fadawa Mimi wacce har suke zargin sa da ya yaudara ta, maganar auran ta kuwa ya fada ne saboda son da take masa gami da ganin yanda suka shak'u da Asma'u yana ganin ko ya aure su su biyu ba za a samu matsala ba, yanayin dabi'un Mimi da nutsuwar ta gami da kunyar ta suna bashi sha'awa amma zallah so gangariya babu Wanda yake wa sai Asma'u duk cikin 'yan matansa babu wacce ta samu wannan matsayin kamar ta hak'ika Asma tana da babban matsayi a zuciyarsa.

Da wannan tunane-tunanen ya Isa asubitin, Madi suka bude masa kofar ya shigo cikin sauri suka biyo motar da gudu yana parking suka bude masa kofa suna yi masa barka da zuwa.
Amsa musu yayi babu yabo babu fallasa, ya wuce ciki.
Suka tsaya suna binshi da kallo tare da tunani wane dalili ne ya kawo shi asibitin ? Suna zargin yau ya zagayo su ne duba marasa lafiya da. da bada tallafi kamar yanda ya saba, murna suke sosai yau zasu cika aljihunansu.

Wayarsa ya futo da ita yana laluben numbar da ta kira shi da ita yanzu....

*10/November/2019*
[11/11, 9:19 AM] BintuUmarAbbale: *BABBAN YARO*

*Mallakar_BINTA UMAR*

*LITTAFIN MALLAKI NA NE KUN BIYA KUD'IN KARATU NE KAWAI DUK WACCE TASAN ZATA FUTA DASHI WAJE DON GIRMAN ALLAH TAYI MIN MAGANA NA DAWO MATA DA KUDIN TA.*

*48*

Ringing d'in wayar ne ya dawo dani cikin hankalina wayar na duba sai naga numbar sa, da kamar kar in dauka wata zuciyar tace"Dauki kiji me zai ce miki.
Jin alamun ta daga wayar ne yasa yace." Gani cikin hospital din ki futo kiyi min jagora har inda kuke."
Bai saurari Abunda zata ce ba ya kashe wayar sa.
Futowa nayi daga gurin da nake.
Har yanzu suna tsaye kan Umma sun yi mata rumfa Aminu sai fiffita yake mata.
Aunt Hauwa ta kalle ni tare da fadin"Da ina kika shiga tun d'azu. "
Cikin wayan cewa nace"Futsari naje nayi."
Raba ido nake yi a gurin ko Allah zai sanya I n hango shi
Da yanayin tafiyar shi na gane shi.
Shiru nayi har ya k'araso gurin.
Cike da mamaki suke kallonsa.
Ya mik'awa Aminu Hannu su gaisa.
Da kyar ya mik'a masa nasa hannun kamar yanda yayi masa jiya.
Umma ya kalla yace." Umma Ashe bayan tafiya ta jiki ya rike CE."
Umma ta gyara zamanta hade da gyara mayafin ta tace"Wallahi kuwa aman jini take sosai."
Gaban shi ya fadin jin abunda Umma tace, Yace." Bari in ga dector babu matsala insha Allahu komai zai zo da sauki."
Binsa mukayi da kallo har ya shige ciki abun mamaki babu Wanda ya hana shi shiga cikin ma'aikatan sai ma da d'a gyara masa hanyar wuce da suka yi.

Kamar yanda dector ya yiwa Kawu Baya ni haka yayi Amjadu baya ni Wanda ya gamsar dashi kuma shima ya gane kan ciwon Mimi kamar yanda Asma'u take fada cewar ciwon sonsa ne yake damunta.

Yace." Doctor yanzu kun gama komai ko."? Gyada kai Dr yayi tare da fadin"Mun gama komai dasu domin har sunje sun karb'o magani a pharmacy kuma yanzu na sanya nurse ta bata maganin babu matsala insha Allahu mutukar an bi doka."

"Yanzu sauransu biyan kudi domin yanzu nake cewa Narse ta zo mik'a musu rasit." Yace." Kar ka damu insha Allah ka bani numbar accont din Ku na hospital din sai a turo maku hakkin Ku.

Da sauri Dr ya dauki 'yar k'aramar ta karfa da biro ya rubuta masa hade da mik'a masa, ya San ba iya kacin kud'in su zai tura musu ba Dole sai yayi musu kari, tunda dama ya saba kawo musu ziyara a sibitin.

Har ya mike zai futa sai kuma ya tsaya tare da fadin"Yanzu babu halin a ga yarinyar. " ? Dr ya mike da sauri yana fad'in"A'a Yallab'ai kai zaka iya shiga ka ganta."

Tare suka shiga room d'in da Mimi take kwance bacci take sosai sai dai har yanzu nuffashin ta bai gama dawo wa normal ba. Dr ya futa hade da jawo masa kofar , ido ya tsura mata sosai yake kallonta mace har mace tana Neman ta jefa rayuwar ta a wahala.

Domin shi a ganinshi wahala ce,kaso Wanda bai San kana yi ba, bai tab'a tunanin son da Mimi take masa ya kai haka a zuciyar ta, sai yaji zuciyar sa tana ce masa da ma wannan Soyayyar daga gurin Asma'u ka same ta daka ji dad'i. Amjad mutum ne mai mutukar son a dunga tattashin sa da rarrashin sa kulawa da soyayya, shiyasa yake addu'ar Allah ya bashi mace wacce take da wannan azanci domin matan ma suna suka tara.

Yafi minti goma a tsaye a kanta yana kallonta, kokari yake yaji wani abu wanda ya shafi so ya darsu a zuciyarsa a game da ita, bai ji komai ba sai dai tausayin da taye mata da kuma kaunar da yake mata saboda sunan Maman shi, Wanda ba ita kadai yake wa wannan kulawar ba, mutukar A kace kina da suna Aisha to zaki samu kulawa sosai a gurin shi.

A gogon dake daure a hannunsa ya kalla hud'u shaura na Asubah. Gyad'a kansa yayi ya bude kofar dakin a hankali ya futa, har yanzu suna zaune a inda suke sai dai sun matso cikin wata rumfar kwano dake gurin saboda sanyin asubah. Sosai suka bashi tausayi mussaman Asma'u da ya ganta tayi wujuga-wujuga da ita ga idanunta sun kode. daga nesa ya tsaya tare da fadin "Umma ni zan wuce Allah ya bata lafiya."

Umma tace"Ameeen suma ameen mun Gode k'warai da kulawa." Kallona naga yayi a fakaice sai kuma ya kalli Aminu dake dauke dauken kai ya mik'a masa hannu domin suyi sallama.

Da kyar Aminu ya bashi hannunsa, Amjadu ya wuce yana mamakin abunda Aminu yake yi sai kace jahili in banda dalili ya kai dalili Aminu ya Isa yaga inuwar shi ma ballanta ya hada hannu dashi, duk sanadin Asma'u ne.

Sai da ya shiga motar sannan ya kira ta a waya, ina jin wayar na ringing naki dauka Munnu ta karba daga hannuna tana dubawa. Mik'a min tayi tare da fadin"Shine." Aunt Hauwa tace" Sai ki tashi kije mybe akwai abunda zai ce miki."

Kallon da Umma tayi min ne yasa na mike da sauri na bi hanyar da naga ya bi.Na gane motar shi tunda duk inda suke basa b'uya bayan haka kuma gurin da haske.

Kallonta yake yana daga cikin motar har ta k'araso. Ajiyar zuciya ya sauke babu wasa a tartare dashi ya bude motar tare da fadin"Shigo muyi magana dake ta fahimta."

K'in shiga nayi na tsaya ina kallonshi. Shima ya kalle ni babu fara'a yace." Time d'in sallah ya kusa ki shigo muyi abunda zamuyi in tafi gida Ok."

A hankali na shiga motar na zauna ina kauda fuskata. Ya kalle ni na minti uku, kana yace." Wannan kukan da kike yi Sam! Ba zai miki maganin komai ba sai dai ma ya kara sanya miki damuwa da ciwon kai, Yanzu shawara zamu yanke dake idan kin amince ni mai sauki ne."

Kallonshi nayi ina d'an ya mutsa fuskata nace"Ina jinka." Shiru na minti biyu bai ce komai ba yana kallona, na dago kaina hade da watsa masa harara nace"Kace lokacin sallah ya kusa amma kuma ka sanya ni a gaba kana kallo kamar tv."

Ajiyar zuciya ya sauke hade da lumshe idonsa, k'asa-k'asa naji yace." Asma'u Allah ne kadai yasan ita a dadin kaunar da nake miki a cikin wannan zuciyar tawa, tun da nake a rayuwata ban tab'a furta wa mace WANNAN Kalmar ba sai ke, duk da cewar nayi rayuwa da 'yan mata iri-iri masu kyau da kudi Asali nasaba da wayewa amma babu wacce ta samu wannan Kalmar sai ke."
Shiru nayi sauraron shi. Ya cigaba da cewa "Ina da kudi sosai Wanda ban San iya a dadin su ba kuma kullum karuwa suke yi ina zakka da duk wani Abu da Allah yace kayi da dukiyar da ya baka amana, Abu guda ya rage min mata, kuma na samu insha Allah." Shuru Yayi na minti biyu ya cigaba da cewa "Mimi ta bani tausayi mutuka nasan illar so, tabbas tana so na, Wanda naji a zuciyata dama kece kike min irin son da take min da babu namijin da ya kaini dacewa a duniyar nan."
Kallonshi nayi jin abunda yake fada.

Dauke kaina nayi hade da d'an ya mutse fuskata nace"Me yasa ka yaudari Mimi kasan baka son ta."

Shiru yayi yana nazarin magana ta can naji yace." Da farko da wasa nake yi, amma daga baya na d'aura niyyar auranku tare domin in cuzguna miki dalilin yin haka kuwa shine Rashin mutumcin da kika je kikayi gurin pary Ku ya bani haushi shiyasa na yanke wannan shawarar."

Murmushi nayi me ciwo nace"Idan domin ka bani haushi kace zaka auri Mimi a lokacin wallahi da baka wahalar da kanka,saboda kasan shi so sai ana kishin mutum ake yin sa, Mimi tana sonka tana kishin wani ya rab'e ka ciki kuwa har da ni, Mimi ita yafi da cewa ka aura bani ba."

Fuskarsa ya Dan hade yana kallona tare da k'ankantar da idanunsa yace." Gashi ni kuma ba Mimi nake so ba ke nake so, sai dai idan kin yarda in hada ku, Ku biyu in aura amma duk abunda ya biyo baya kar kiyi kuka dani."

Ba tare da tunanin komai ba nace"Ni dama akan wannan k'adami nake, Ya Aminu dole ya janye maganar auran Mimi idan yak'i janjewa nima nace bazan aure ka ba, sai dai duk mu hak'ura dama ni ban damu ba, itace abar damuwa."
Chapter 21 · 0% Book details