← Book details Auren Dole Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 15

Sashe 9

Auren Dole Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Godiya sukayi masa dakin da Hudah take suka shiga Abbu kuwa tafiya yayi

Ummi da Dalhat kuwa mamaki ne ya cikasu Jiddah tace Ummi meyake damunta tun daxu bacci take haryanzu bata tashi ba

Ummi tace kada ki damu zazzabi ne kawai insha Allah zata samu sauki

Daga nan ta fita a dakin wayar hajiya ta kira ta fada mata wannan abin mamakin

Abin ya bata mamaki lallai akwai alamun tambaya koma dai menene in sun dawo gida dole zaayi bincike daga nan sukai sallama.....

🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:30 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰

Book 2

Page 91 - 95

Mufeedamuazuu.blogspot.com

STORY
And
WRITTEN
BY

*Mufeeda Muazu*

Jiddah tace yar uwa meya faru kike ta nemana haka Hudah ta numfasa ta fada mata duk abinda ya faru yau tsakaninta da Dalhat Jiddah tayi shewa tace dama ai na fada miki yaya Dalhat yana sonki kinki sakin jikinki da shine shiyasa ya kasa fada miki Hudah tace uhmm ni ba wannan ba yanzu meye shawara Jiddah tace shawara daya ce ki bada kai kawai bori ya hau Hudah tace haba ya zaayi kice haka bayan irin wahalar daya bani gsky nima sai na rama sannan kuma inja ajina

Jiddah tace nidai na baki shawara ta gsky kyaje garin jan aji yaje ya tsinke Hudah taja dogon numfashi tace naji zanyi shawara ni zan tafi sai nashigo anjima Jiddah tace ba sai kin shigo ba ki zauna Kusha soyayyarku Hudah ta harareta tace kyaji da shi ta bude kofa ita kuma Rufaida tazo kenan zata shigo bangajeta tayi zata wuce Hudah ta janyota tace wai ke wace irin karya ce ance ba ayi kin nace murmushin mugunta Rufaida tayi tace kin kusa barin gidan don dama yaya Dalhat ba saan aurenki bane nice na dace dashi bake ba tsaki Hudah tayi ta wuce abinta

Dalhat yana fita gidansu Hudah ya shiga ya gaishe dasu hajiya sun dan taba hira kadan ya dawo gida ya tarar da side din a rufe baiji mamaki ba don yasan tunda ya hana Jiddah zuwa ita sai taje mamakin kawancen su yake jininsu ya hadu sosai basa boyewa juna sirrinsu

A bude ta tarar da kofan tana shiga ta tarar dashi zaune a falo yana latse2 a wayarsa wuce shi tayi zata shiga daki Kiran sunanta ya kira bata amsa ba tsayawa tayi inda take yace ina kikaje ba izini banza tayi dashi saida ya sake maimaitawa sannan tace wurin Jiddah na shiga tunda kai ka hanata ta shigo wurina sbd wani tunani irin naka tana gama fadin haka ta shige daki abinta

Ajiyar zuciya yayi tunanin yanda zai shawo kanta yake don gsky Allah ya jarrabeshi da sonta gashi ita kuma bata sonsa abinda bai saniba shine itama tana shiga daki tunaninsa ne fal a cikin ranta sai dai gsky tana kokonton son da ya fada mata yanayi mata don haka bazata yi saurin amincewa shiba koma zata amince masa to gsky ba yanzu ba sai taja ajinta yadda ya kamata

Abinda basu sani ba shine Rufaida na biye da Hudah a baya saida ta tabbatar da babu kowa a falon sannan ta shiga ta boye bayan labule Dalhat yana shiga daki alola ya yo don an fara Kiran sallar magriba tunda ya tafi masallaci bai dawo ba saida akayi sallar issha

Sanda ya dawo a falo ya tarar da ita tana sallah wuri ya samu ya zauna har sai da ta idar tayi addua suka shafa a tare kallonta yayi cike da kulawa yace baby ki shirya mu dan fita cikin jindadi tace toh tare da nade abin sallar daki ta shiga cikin yan mintoci ta fito sanye da zumbulelen hijabinta sai kamshi take zubawa yaji dadin shigar da tayi

Murmushi yayi yace kinyi kyau taji dadi a ranta amma batace komi a tare suka fita saida sukayi nisa sannan ta kalleshi tace yaya ina zamuje dan kallonta yayi kadan sannan ya maida hankali ga tukinsa yace kisa ido zaki gani ba wanda ya kara magana cikinsu har yayi parking a gaban wani katon mall fita yayi yaga bata fito ba ta window ya leko yace madam ki fito mana ba musu ta fito yace muje ki zabi abinda kikeso siyayya sukayi sosai kananan kaya kuwa shiya zabar mata da kansa

Daga nan restaurant sukaje a can sukaci abinci sannan suka Kama hanyar gida zuciyarta cike da farin ciki dama tana son fita irin haka

Rufaida najin dawowar su tayi sauri ta koma bayan labule Dalhat ne ya shigo da kayan da suka siyo dakinsa ya wuce da shi itama daki ta shiga don yin shirin bacci Rufaida na ganin haka tayi sauri ta dauko ruwa da kofi ta tsiyaya ruwan a kofi ta aje tabs din FP a gefe tayi sauri ta fita a side din a kofar kitchen suka ci karo da Jiddah bata ce mata komi ba ta wuce zuciyarta cike da farin ciki

Fitan ta ba dadewa Dalhat ya fito daga daki kaman ance ya kalli gurin hango magani yayi a center table zuwa gurin yayi ya dauki maganin iri daya dana rannan ransa yayi matukar baci Wato har yanzu bata daina sha ba kenan sai tayi kamar ta bari kiranta ya farayi bataji ba sbd ta fara bacci saida ya kira sau 3 sannan taji da sauri ta sauko daga gado ta fito tana mitsike ido almamun mai bacci yana yin data ganshi ya bata tsoro tace lpy meya faru

Bata ankara ba sai jin Mari tayi dafe gurin tayi tana hawaye magana ya fara da kakkausar murya yace wato kin maidani banza kike tambayata abinda ya faru nuna mata maganin yayi yace Allah ya Kama ki kin dauko ruwanki zaki sha sai kika manta kuka take sosai tace Allah bani na ajeba ban san dashiba wani magigicin tsawa ya daka mata yace yi mun shiru daga ni sai ke a gidan nan kada ki raina mun hankali......

🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰

Book 2

Page 101

Mufeedamuazuu.blogspot.com

STORY
And
WRITTEN
BY

*Mufeeda Muazu*

Bismillahir rahmanir rahim

A hankali Hudah ta fara motsi da idonta tana budesu a hankali har ta bude su gaba daya Jiddah na ganin ta bude ido ta matso kusa da ita tace sannu ya jikin dai Hudah bata iya cewa komi ba sai hawaye dake bin fuskarta

Dalhat da Ummi suna waje suka ga Jiddah ta fito a rude Ummi ta tareta tace lpy Jiddah tace ta farka ta kasa magana sai kuka take shine zanje in kira doctor

Da sauri suka shiga dakin Jiddah kuma taje Kiran doctor Ummi ta zauna kusa da ita ta riko hannunta tana lallashinta yunkurawa tayi zata tashi Ummi tai sauri ta komar da ita tace kiyi hakuri kinga ruwa ake kara miki Dalhat na tsaye a gefe yana kallonta cike da kauna suna hada ido tai sauri ta runtse idonta ta mai jin zafin abinda yayi mata ya bude baki zaiyi magana kenan sai ga doctor ya shigo Jiddah na biye dashi a bayanta

Likita ya duddubata sannan yayi mata wasu yan tambayoyi da yadda takeji a jikinta ta bashi amsa yayi rubuce-rubucensa yaba Dalhat yace yaje pharmacy ya siyo

Jiddah tace sannu yar uwa tare da goge kwallar dake zubo mata tace yawwa ngd

Hudah tace Ummi wai me likita yace ke damuna zazzabin yayi mun sauki yanzu zuciyata ke tashi ga matsanancin ciwon cikin dake damuna

Ummi tace kiyi hakuri Hudah insha Allah zaki samu sauki yanzu zai kawo miki magani kinji

Tun daga nan Hudah bata kara cewa komi ba lumshe idonta tayi kamar mai bacci har Dalhat ya dawo tare da magunguna a hannunsa

Ya mikawa Ummi sannan yace bari yaje ya dawo Ummi tasa Jiddah ta hada tea mai kauri

Sannan tasa ta kawo mata babban roba ta kuskure baki rungumeta tayi tana bata a baki da kyar ta iya shan rabin kofi sannan ta sha maganin nan da nan bacci ya dauketa

Ummi tace jiddah ta kula da ita zataje gida ta dafa musu abinci zata turo Rufaida Jiddah ta bata rai jin an ambaci sunan Rufaida tace Ummi da kin kyaleta kawai ni zan iya kula da ita

Ummi tace aa hakan bazai yiwu ba sai na dau Allah ya kara sauki

Tafiyan Ummi ba dadewa Dalhat ya dawo hannunsa rike da leda kayan marmari ya siyo ajewa yayi akan drawer bude Jiddah ya tambaya ina Ummi tace masa ta tafi gida ta dawo

Ya kalli Hudah dake kwance idonta a lumshe kamar mai bacci Dalhat yana kula da ita ba baccin take ba kallon Jiddah yayi yace dan bamu guri

Tayi kamar bataji ba saida ya kara maimaitawa sannan tace yaya ai tana bacci yace ina ruwanki batace komi ba ta fita

Tana fita yasa ma kofar key ya dawo kusa da ita ya riko hannunta yana murzawa har lokacin taki bude ido murmushi yayi yace nasan idonki biyu nine dai bakya son gani sbd laifin dana aikata a gareki ba tare da nayi bincike akai ba ina mai baki hkr akan abinda ya faru don Allah kada kiga laifina idona ne ya rufe kiyi hkr kinji ita dai jinsa kawai take bata gane inda maganarta ya dosa ba

Hawayene ke zuba a idanunta ba tsayawa goge mata yakeyi yace Hudah bakice komi ba don Allah ki bude idonki kiyi mun magana kona samu sassauci a cikin zuciyata nan ma shiru

Sakin hannunta yayi tare da mikewa yace shikenan tunda bazakiyi hakuri ki yafe mun laifukana ba shikenan bkm ammah ina rokon alfarma a gurinki don Allah ki kula da kanki da kuma cikin dake jikinki jin ya ambaci tanada ciki tayi sauri ta bude ido tayi farin ciki da Allah ya fitar da ita da zargi a daya bangaren kuma tana tunani bazata iya barin cikin ba sbd ta gaji da wannan auren na yaya Dalhat

Kusa da ita ya dawo ya zauna yace banga kina farin ciki ba hararasa tayi ta kalleshi ido cikin ido tace bana farin ciki kuma ka daina wani rawar kafa don sai na zubar da cikin nan na fada maka bana sonka bana kaunarka ni ka kyaleni inyi rayuwata cikin farin ciki ka bani takardata ni bazan koma gidanka ba
Chapter 9 · 0% Book details