← Book details Auren Dole Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 15

Sashe 14

Auren Dole Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sumayya sai tsokanar Hudah takeyi a hanya wai Allah yasa yan biyu zata haifa tun tana kulata harta gaji ta kyaleta a daki suka sameta taci kukanta harta gode Allah Hudah na zuwa ta maka mata duka a baya da sauri ta tashi ganin Hudah ne yasa ta koma ta kwanta tana hararanta tace sai yanzu ne kikaga daman zuwa ai da kin sani bakizo ba Hudah tace ai yanxu ma bata baci ba sai in koma tunda baki bukatar ganina tashi tayi zata fita Jiddah tayi sauri ta riko hannunta tace haba yar uwa baki San wasa bane Sumayya tace kyaleta ta tafi mugani

Hudah tace ke kuma waya sakoki ciki zama sukayi a gefen gado Hudah tace kinsan da yaya na fito kuwa da kyar ya barni kuma yace kada magriba tayi mun a waje Jidda tace aiko bazai yiwu ba ace bazaki kai dare ba Hudah tace to yaya zanyi abinda yafi karfina dole sai hakuri Jidda ta dauko wayar ta dialing no Ummi tayi bugu daya ta dauka bayan sun gaisa Jidda tace Ummi don Allah kice yaya Dalhat ya bar Hudah sai dare sai yazo su tafi tare Ummi tace eh to bazan ce eh ko aa ba don bai kamata in shiga hurumin da ba nawa ba kuma idan nayi masa magana zai ga kaman itace ta fada mun kinga zasu iya samun matsala kuyi hakuri kawai

Sallama sukayi Jidda bata so haka ba hawayene ya gangaro mata a fuska Hudah ta goge mata tace kiyi hakuri nima ba haka naso ba ammah ba yadda muka iya Jidda tace shikenan yanxu zumuncin mu zai yanke

Hudah tace ki daina fadan haka xumuncinmu bazai taba yankewa ba har a bada kamar yadda muka taso mukaga iyayenmu nayi haka muma insha Allah mutuwa ce kawai zata raba mu Jiddah tace ba gashi ba yanzu yaya yana so ya yanke ba Hudah tace wane mutum ai bai isa ya yanke mana zumunci ba

Sumayya tace Allah sarki Allah ya bar zumunci dukkansu suka amsa da Ameen daga nan kuma sai hira ya tsinke

Wurin karfe 6:30pm sukayi shirin tafiya Jiddah kuwa kwalla ne ya cika mata ido Hudah tace hakuri zakiyi kowa da kika ganshi haka aka tafi aka barshi ina nan zuwa kada ki damu kinji yar uwa goge mata hawaye tayi rakosu tayi har wurin da sukayi parking din mota Hudah tace to amarya sai munzo gashi gone kallon Sumayya tayi tace ko ba haka ba
.
.

Sumayya tace kinji Jiddah kyaleta dadin abin ma baa kaiki kina guduwa ba wai ba kyaso sai kuma gaki da ciki ina kiyayyar take Hudah bata ce komi ba ta bude mota tayi shigewarta sannan tace kwaji dashi ke kuma Sumayya idan kin gama shirmen naki sai ki shigo mutafi sallama sukayi mata suka dauki hanyar gida Jiddah ta koma gida jikinta a sanyaye.......

Muffy😘
[4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰

Book 2

Page 115

🌐🔰 HAJOW 🌐

🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐

mufeedamuazu.blogspot.com

*STORY And WRITTEN*
*BY*

*MUFEEDA MUAZU*

Bismillahir rahmanir rahim

Bayan wata uku Hudah ce ta fito da tsohon cikinta tana kiran Dalhat shiru bataji motsinsa ba dukawa tayi sakamakon matsanancin ciwon mara tana cikin wannan hali Aunty Mufeeda ta shigo da sauri ta karisa wurinta tana tambayarta meyafaru kasa magana tayi sai ciki da take nuna mata kamota tayi a hankali suka fito a mota ta sata sannan ta zaga mazaunin direba ta shiga maigadi ya bude musu gate suka fita asibitin da take awo ta kaita don haka suna zuwa aka amsheta labour room suka shige da ita don suna ganinta suka gane haihuwa CE
Aunty Mufeeda fitowa waje tayi tana nema layin Dalhat

Koda Dalhat ya dawo yayi sallama yaji shiru ya duba ko ina bai ganta ba ya tafi side din Ummi nan ma shiru yaji ba kowa a falo dakin Ummi ya shiga ya tarar tana bacci wayarsa ne tayi kara Aunty Mufeeda ne karan wayar ne ya tashi Ummi daga bacci dauka yayi tare da yin sallama daga can Aunty Mufeeda ta amsa sannan suka gaisa anan ne ta fada masa suna tare da Hudah a hospital tana labour sannan tace masa ya duba dakinta ya dauko kayan da ta hada na haihuwa

Hankalinsa duk ya tashi ya fadawa Ummi da sauri ya fita Ummi kuwa toilet ta shiga tayi brush ta wanke idonta zani kawai ta daura ta dauki hijab dinta ta sauko kasa da sauri lokacin harya fito da mota shiga tayi sai asibiti

Tun safe har yamma bata haihu ba hankalin kowa duk ya tashi Doctor ne ya fito daga dakin duk yayi xufa yace Dalhat ya biyo shi office Ummi tace lpy kuwa Doctor baice komi ba Dalhat yabi bayansa

Doctor ne ya fara bayani kamar haka a gaskiya munyi iyaka kokarin mu ammah har yanxu d only solution kawai shine ayi mata C.S wani takarda ya dauko ya bawa Dalhat yace yasa hannu

Dalhat yace C.S kuma Doctor? Doctor yace eh don aceto rayuwarta da abinda ke cikinta Dalhat cikin sanyin jiki ya daura hannu akan takardar kenan sai ga wata nurse ta shigo da sauri tace Doctor kan dan ya fara fitowa da sauri ya tashi suka tafi dakin dukkansu dakatar da Dalhat nurse din tayi dawowa yayi sai safa da marwa yakeyi yakasa zama Ummi sai baki take bashi

Doctor na shiga dakin Da na fitowa kato dashi sak irin babansa dan wani lokaci kadan nakuda ya dawo sabo wannan karon macece bayan 10mins saiga wanni nakudan lokaci kadan haifo yarta mace ba dadewa mahaifar ya fito saida suka gama gyarata tsaf aka gyara jariran sannan wata nurse ta fito hannunta rike da namijin da fara'arta tazo ta mikawa Ummi babyn sannan tace congratulations Dalhat yace ya mahaifiyar fa nurse din tace tana lpy ta haifa maka jarirai guda uku congratulations once again Dalhat bai jira ba yayi sauri ya shiga dakin sbd tsantsar farin ciki su Ummi suka mara masa baya Doctor dinne ya mika masa hannu yayi masa murna nurses suka mika masu jariran Dalhat hunnunsa rike da mace daya yaje kusa da Hudah inda take kwance ya riko hannunta yana jin sonta a ransa bacci take don anyi mata allurar bacci sbd ta huta nurse tace idan ta tashi likita yace zaa sallamesu don sun dubata sun tabbatar da lafiyarta kalau

Aunty Mufeeda ta kira Hajiya ta fada mata alokacin Husnah na nan tazo ganin gida da sauri Hajiya ta dafa ruwan zafi ta juye a flask ta hada kayan shayi ta hada mata a basket tace tayi sauri ta kai musu cikin lokaci kadan labari ya watsu cikin dangi Hudah ta haifi yan uku

Dalhat ya karbi yaran yayi musu huduba ammah bai fadawa kowa sunan daya sanya musu ba.......

Muffy😘
[4/9, 9:34 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰

Book 2

Page 116

🌐🔰 HAJOW 🌐

🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTER🌐

mufeedamuazu.blogspot.com

*STORY And WRITTEN*
*BY*

*MUFEEDA MUAZU*

Bismillahir rahmanir rahim

Dedicated dis page 2
*Muffy online Hausa Novels*
*Muffy & Maryam Ahmad paki*
*Feedoh online Novels*
*First lady Hausa Novels*
*Da sauran groups din Novels wanda ban ambata ba*

After four hours Hudah ta farka Ummice a gefenta sai kuma Dalhat dake tsaye a gaban gadon Ummi tace sannu Hudah rufe ido tayi sbd kunya Dalhat yace baki tambayi abinda kika haifa ba shiru tayi batace komi ba daya na hannun Ummi biyun kuma an kwantar dasu a gadon yara dake kusa da nata Dalhat yace yara uku kika haifa biyu mata daya namiji Hudah dai shiru tayi batace komi ba

Ummi ta mika mata yaron dake hannunta kin amsa tayi wai tana jin kunya Ummi ta mika wa Dalhat yaron tace bari in tashi nasan ni kikejin kunya tana fita Dalhat ya dawo kusa da ita ya daura mata yaron akan cinyarta kurawa yaron ido tayi cikin so da kauna duka yaran ya dauko mata duk tayi musu addu'a kallonsu tayi tace ammah yaran nan dakai suke kama fah Dalhat yace aa dake suke kama

Wani suna kasa musu Hudah ta tambaya Dalhat yace wani suna kikeso a saka musu Hudah tace duk sunan da ka sanya musu nasan bazaka zaba musu suna mara maana ba Dalhat yayi murmushi tare da shafa kanta yace Masha Allah Allah yayi muku albarka Ameen ta amsa

Dalhat yace namijin nasa masa Hibban matan kuma Kausar da Wahida murmushi hudah tayi tace masha Allah.Allah ya raya manasu

Bayan 1hr likita yaxo ya dubata lpynta kalau sannan ya sallamesu tun kafin su dawo mutane suka fara zuwa barka

Dama sun yake shawarar gidanta zaa barta wata kanwar Hajiya zatazo ta zauna da ita Dalhat yaji dadin haka don gidanta aka dawo da it a

Sumayya da Jiddah Suna zaune a gefenta Sumayya tace kinga Allah ya amsa adduata ko harda kari ma Hudah tayi murmushi tace aike zan bawa guda daya inba Jiddah daya

Jiddah tace ai muna so wannan babbar kyautace kinga Sumayya ta samu dan zaman daki dariya sukayi dukkansu.

Hibban ne ya fara kuka Jiddah ta miko mata shi don ta bashi nono Hudah tace wlh bazata bashi ba sai dai bashi madara ya cika tsotso dayawa Sumayya tace aiko dole ki bashi tunda babansa ya riga ya biya abu kamar wasa taki bashi Husnah dake gefe zaune da laulayin cikinta wata biyu ta mike zata fita Sumayya tace ina zakije ana zaune ana hira Husnah tace kaina ke ciwo zanje in dan kwanta ne Hudah tace Uhmm manya Husnah dai batace komi ba tayi tafiyarta gidansu tana shiga ta fadawa Hajiya duk abinda ke Faruwa baa jima da fitar Husnah na ba saiga Hajiya ta shigo sai fada take tundaga kofa tana shiga dakin ta amshi Hibban a wurin Jiddah dake kuka tana lallashinsa ta ajiyewa Hudah a cinyarta tace ta bashi nono da kyar tana hawaye ta ciro nono ta bashi tana cije baki wai zafi yake mata
Chapter 14 · 0% Book details