← Book details Auren Dole Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 15

Sashe 6

Auren Dole Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilkisu kuwa tana fitowa daga toilet din taga har ta shimfida mata sallaya sallah tayi Hudah tace ga kayan kwalliya nan a dress mirror powder kawai ta shafa ta dawo kusa da ita ta zauna tace ni sunana bilkisu kefa tace sunana Hudah bilkisu tace nice name Hudah tace tnx bilkisu naso suyi hira Ammah Hudah taki sakin jiki sai cin magani take Hudah tace ya sunan yaron nawa bilkisu taji dadin karan datayi mata tace sunan sa Ahmad tashi tayi ta bude drower ta kwaso turaren wuta da humra masu kyau da tsada tun na aurenta ne tasa a leda tace gashi ba yawa bilkisu ta amsa tayi godiya sunyi shiru ba mai magana bilkisu tana tunanin hali Irin na Hudah kamar mai aljannu Dalhat ne ya shigo yace madam ki fito zaku tafi juyawa yayi bilkisu ta dauki mayafinta tace to Hudah sai anjima itama mikewa tayi sukayi exchanging no a tare suka fito a tsaye suka tarar dasu Hudah tace Ahmad zo mana mu gaisa da yake yana da wayau baiyi quyaba yaje 2k ta bashi tace gashi ka sha sweet Ahmad yace ngd Aunty farook yayi gdy har waje ta rakasu tana harar Dalhat duk suna kallonta murmushi farook yayi yace wannan madam din taka yar daru ce Ammah fah tanada taushin zuciya duk da haka kayita lallashinta haka sukayi sallama cike da begen juna saida yaga tafiyar su sannan ya dawo gida ya tarar ta kwashe kayan da sukaci abinci ta gyara wurin kusa da ita ya zauna yace my wife ngd sosai sunanda ya kirata dashi ya bata mamaki bata gama mamaki ba taji yace ki shirya anjima zamu fita shopping batayi musu ba saboda itama tana son fita

Tace to don Allah inaso in shiga wurin hajiya yanxu yace to ba damuwa zuciyanta fari kal da gudu ta shiga daki ta dauko hijab dinta ta fito yana zaune tace sai na dawo

Da gudu ta shiga tana kwada Kiran hajiya, hajiya tace ke wai yaushe ne zakiyi hankaili turo baki tayi tace nine banida hankali ko hajiya tace ya Dalhat din Hudahh tace yana gida yau bazan koma gida ba sai dare suna cikin hira shahid ya shigo ya kalli Hudah yace ke bakida mutunci ko Hudah tace me kuma nayi yace bansani ba zakiyi shiru ko saina fasa bakinki anan wurin hajiya tace lpy shahid yace daxu ina gidan Dalhat ya kira Jiddah wai insu nada ta kawo masa yayi bakine yanxu hajiya abinda takeyi ya dace kenan hajiya ranta yayi matukar baci Hudah batayi aune ba taji saukan mari rike wurin tayi don azaba ta bude baki zatayi magana shahid ya bige bakin zai daketa hjy ta hana tace baa asan kotana da juna biyu......

🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰

💦💦💦 *TALENTED WRITERS* *FORUM*💦💦

*T. W. F*

Book 2

Page 66 - 70

Mufeedamuazuu.blogspot.com

STORY
And
WRITTEN
BY

*Mufeeda Muazu*

*Dedicated dis page 2*

*Rahmat Nalele*
*Husnah mb*

Bissmillahir rahmanir rahim

Hudah ta turo baki tace hajiya ki daina Irin wannan maganan Nifa banida komi kuma ma Allah ya kyauta in tsaya yayi mun ciki bana sonsa bana kaunarsa Shahid yace hajiya kinji abinda take fadi ko sbd taga kince a kyaleta mikewa tsaye yayi ya nuna kofan fita yace fita a gidan kafin in karkaryaki mara kunyar banza kawai hajiya kasa magana tayi lallai haryanxu Hudah batayi hankali ba

Hudah tayi kaman bada ita yake ba saida taga ya zaro belt zai daketa sannan ta daka tsalle ta koma bayan hajiya tana kuka tace ya zaayi mutum da gidansu a rika korarsa hajiya kice ya kyaleni hajiya tace aini Kinfi Karfina duk abinda zaiyi miki bazan sake magana ba tana gama fadar haka ta tashi ta haye sama abinda ganin haka yasa Hudah ta mike tana goge hawayenta jikinta duk ya mutu ta kalli Shahid dake nuna mata kofar fita tace Allah ya isa mugu kawai ta fita a guje koda ta shiga gida side din su Jiddah ta wuce a falo ta tarar da Jiddah da Radiya kusa da Jiddah taje ta zauna tana haki Jiddah tace ke lpynki sai kace an biyoki Hudah tace yaya Shahid ne don wulakanci wai zai dakeni da aurena mtsw.....tsaki sukaji a tare suka dago don gane ma idonsu Waye mai tsakin Rufaida ce ba Wanda ya kulata ta taso tazo har gaban Hudah tace ke banza baki ganin mutanene da bazakiyi musu sallama ba Hudah ta mike tsaye cike da masifa ta kalleta sama da kasa tace ina mutanen suke waike wace Irin karya ce mara zuciya ance baayi dake amma kin nace Rufaida tace ai naga dai kema din ba sonki yake ba kuma ai kece karyar Hudah ta kai mata magigicin mari kikake tas!

Rike wurin tayi tace ni kika mara Hudah tace an mareki din ke din banza ta murmushin mugunta tayi tace yanzu kam duk abinda zakiyi kiyi lokacinki ne nan da kwana kadan ba kya gidan nan wlh sai kin barshi Jiddah tace ke Rufaida mekike fada haka Hudah tace kyaleta ai ni nafison haka sbd nima dole akaimun kare yayar da zuciyarsa an dauka kullum ana gidansu saurayi don nasan ba don zumunci kike zuwa ba ai sai ki zauna a gidan ubanki yazo ya sameki sakarya kawai wadda bata da aji tana gama fadar haka taja hannun Jiddah suka haye sama suka barta a nan sororo

A dakine Jiddah take fadawa Hudah ankawo goron sa rana da nata dana Husnah 6mnth zaa sa Hudah tace lallai ne shine ba wanda ya fadamun yanzu da ba danke da kika fadamun ba bazan sani ba koda yake yanzu na zama bare kwallah ne ya cika idonta Jiddah tace ba haka bane kene kinki ki kwantar da hankalinki ki natsu ki rungumi kaddara ba wanda bai sonki so ake kiyi hkr ki gyara komi mai wucewa ne watarana sai labari

Hudah tace bazaki gane bane amma kinsan wani abu kuwa? Jiddah ta girgiza tace aa sai kin fada Hudah tace naga kwana biyu ya chanza sai wani kula dani yake yana tattalina kinga dazu da yayi baki ban dafa abinci ba da ace da ne da wlh raina sai ya baci Jiddah tace ni dama nasan yaya Dalhat yana sonki kene dai kike shirmenki Hudah tace rufe mun bakinki anan bani yake soba jikina yake so Jiddah tace kwaji da shi dai ku kuka sani Hudah ta mike tace ni kinga tafiyata magriba tayi Jiddah tace to muje in rakaki koda suka sauko ba kowa a falon

Side dinta suka tafi anan sukayi magriba sukai issha sannan suka ci abinci suna zaune wayar Jiddah ta fara ringing dubawa yayi taga mai Kiran mikewa tayi tace matan yaya swtyna yaxo yana jirana gud nyt bata jira jin me zata ce ba ta fita da sauri kwallah ne ya kawo mata tace Allah sarki soyayya ni ban samu wannan daman ba

Jiddah na fita ba dadewa Dalhat ya shigo sannu da zuwa kawai tace shi kuma gogan dadi yaji yau ta kulashi bai san sbd yace zasu fita bane yace yawwa ki shirya ko da sauri tace to ta tashi ta tafi dakinta shima dakinsa ya wuce tana shiga ta bude wardrop dinta taga kayanta ba yanda yake ba

Dalhat harya shirya ya fito falo yaga bata fito ba dakinta ya shiga ya ganta tsaye tana fitowa da kaya yace ya dai madam juyowa tayi tace yaya bayan na fita waye ya shigo min daki Dalhat yace ba wanda ya shigo nima fita nayi lpy tace lpy bkm yace ko inzo in tayakine tace Aa ka barshi kawai nakusa gamawa ta janyo wani kaya kenan wani magani ya fado kallonsa tayi ta kalli maganin shima kallon maganin yayi ya kalleta ya duka ya dauka har an sha rabi karantawa yayi maganin family planning ne tsareta yayi da ido jikinta ya fara rawa ta bude baki zatayi magana ya bige bakin cikin zafin rai ya kaita bango ya matseta yace waya baki wannan maganin a ina kika samu bakinta na rawa tace Allah yaya bani na sha ba ni ban san wanda ya kawo mun ba ranshi ya dada baci wato shi zata rainawa hankali ga abu ya gani da idonsa......

🌱🌱🌱🌱
Muffy
🌱🌱🌱🌱
[3/11, 9:27 AM] Naja: 😰😰😰😰😰
AUREN DOLE
😰😰😰😰😰

💦💦💦 *TALENTED WRITERS* *FORUM*💦💦

*T. W. F*

Book 2

Page 71 - 75

Mufeedamuazuu.blogspot.com

STORY
And
WRITTEN
BY

*Mufeeda Muazu*

*Masoya littafin Auren dole ina mai baku hakuri na rashin jina da mukayi kwana2 fatan zamu kasance tare dani ngd Allah ya bar kauna*

Bissmillahir rahmanir rahim

Hudah da tuni hawaye ya wanke mata fuska tace don Allah yaya kayi hkr wlh bazan kara ba ammah don Allah kada ka fadawa su hajiya Dalhat ya koma gefe ya xauna cikin damuwa yace yanxu kin da kike mun har ya kai haka Hudah dai batace komi ba don ta san ita dai bata taba shan maganin family planning ba to waye ya kawo mata har cikin drawer koma waye Allah ya saka mun Dalhat ya daka mata tsawa yace ba magana nike miki ba Hudah tace Allah yaya ni ban san da shiba ba nawa bane hannu ya daga ya sharara mata mari yace ni zaki rainawa wayo banaki bane nawa ne ko

Tashi yayi ya kwashe maganin ya fita a dakin don idan ya zauna zai iya zaneta sbd yanda zuciyarsa ke kuna yana fita ta dauko wayarta numbern Jiddah tayi dialing ring biyu aka daga tace jiddah don Allah idan bakya komi ina son ganinki jiddah tace lpy ba yanzu muka rabu ba Hudah tace don Allah ke dai kizo Jiddah tace to ganinan zuwa baa sauki wani lokaci ba Jiddah ta shigo Hudah ta rungumeta tana kuka ta kasa magana Jiddah ta dagota fuskarta cike da damuwa tace kince inzo gani kuma nazo kin tasani a gaba sai faman kuka kike ko in kira su Ummi ne

Hudah dai ta kasa magana sai ajiyar zuciya takeyi da kyar tayi shiru tace jiddah don Allah ki taimaka kicewa Ummi tasa yaya Dalhat ya sakeni ni gsky nagaji da wannan auren Jiddah tace waike Hudah meke damunki ne yanzu me kuma akayi
Chapter 6 · 0% Book details