← Book details Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 22

Sashe 6

Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kayan lefe kuwa tuni anhadoshi daga dubai baabunda babu fadin abinda ke cikin lefen ze cinye data baa gamaba
Bangaran dazasu zaunama tuni komai ansaka inkukaga daular daakasa abangaren da ilham zata zauna zaku dauka bazaa mutuba kayane na nunama saa yayinda shikuma megayya me ayki wato ango tuni yabada hotunan ilham akayimasa enlargemet dinsu manyan size yasaka agidan wasu kuma akayi editen danashi aka hada bame cewa batare suka daukaba abokanshi kuwa kowa yaga hoton amaryarsa murna suke tayashi insuka bukaci yakaisu sugaisa da ita sede yace bata gari wani lokacin har mamakin Anwar sukeyi sabida Anwar miskiline nabugawa ajarida amma yanzu yazama suda sabida auran ilham dazeyi
Ko invitation card na bikin abin kallone sewanda yagani

***********
Abangaren ilham kuwa har yanzu bawani sauyi dangane da lalurarta batamasan wainar daake toyawa akantaba
Inna ladi tsohuwar arziki itace tashiga gyara ilham tunda taji labarin aure zaamata duk da tana tausayinta agame da lalurarta haka taci gaba da durawa ilham magani na gyara mace dan ita gani take wata kila wani yakusanci ilham kafin zuwanta abuja.
Ilham ko takara wani fresh tayi kiba yayinda hips dinta suka fito masu kyan tsari cikinta ashafe yake maana bata da tumbi ilham mace ce har mace sede lalurarta ita zata hana ganin hakan

momy ce zaune ita da dady suna tattaunawa gameda bikin tace alhaji har yanzu baka fadamana ranar kai lefennanba gashi yau saura kwana uku biki nifa banganewa wannan auranba kaki kabudemin komai insanshi meke faruwane.murmushi dady yayi sannan yace sweet heart matukar baa daura aurannanba ankawo amarya ba bazaki gane komaiba dan haka kisa ranki a inuwa. Lefe shi kuma abangaranta zaku ajiye intazo tayi amfani dashi kallon mamaki momy take binshi dashi zatayi magana yadakatar da ita tahanyar fadin enough hajiya rai abace yatashi yabata guri baki asake.

Anwar yakosa yaga Princess dinshi dan yanzu har mafarkinta yakeyi. ahalin yanzu tunda dady ya sa ranar auranshi yadena shaawar kowacce mace bayan Princess itace burin ranshi yanzu duk da haka amma yana ganin yanzu tayi kankanta da daukar lalurarsa duk da yalura tanada girman jiki but zebi komai ahankali shiko romance da ita yakeyi yawadatar
Shiyasa gaba daya yagaza sukuni yakosa ashafa fatiha

gidansu yafara cika da danginsu kama daga na uwa harna uba sabida bikin Anwar duk inda yabi andunga ango ango kaga na ilham ay in ana masa wannan kirarin har kyautar kudi yakeyi Wanda shi kanshi besan yawansuba har security na gidan yimasa sukeyi dan su Samu nasu rabon
media kuwa bainda labarin auren Anwar bekaiba in tv ka kunna labarin ake in radio ne itama haka social media kuwa baa magana dan hotunansu daaka hada ake ta yadawa koina kowa yagansu yasan sundace dajuna yan mata masu son Anwar kamar zasuyi hauka dan bakinciki dan sunyi imani me mace kamar ilham baze kara kallon wata y'a maceba dasunan soyayya itako nafeesat yar gidan gomnan kano ganin hoton seda tayanke jiki tafadi agigice akayi asibiti taita Dakyar akasamu tafarfado kuji wahala darai shida besan tanayiba amma shine harda suma 🙄

*RANA BATAKARYA*.............

Love you all maman yusuf
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_written by Zahra Muhammad mahmud_

*page 32*

*RANAR ASABAR*

ayaune dubban jamaa suka shaida daurin auran Anwar tare da amaryarsa ilham shetima bukar daurin auran dayasamu halattar shugabannin wasu kasashen, gwamnoni, sanotoci, yan majalisu, yankasuwa damanya manya atajirai dasauran talakawa masoya mulkin dady amatsayin shugabansu.
Andaura aure abisa sadaki naira dubu dari biyar inda aka bada dukiyar aure 50 millions à babban masallaci na kasa wato central mosque dake abuja taro yayi taro kota ina security ne dan tabbatar da tsaro Ango baki yaki rufuwa se gaisawa yake da jamaa ana mishi fatan alkhairi
Daga gurin daurin aure walima suka wuce wacce megirma shugaban kasa yahada anci ansha anyi danasha maroka ranar kakarsu tayanke saka

Abangaren matama momy kanta har zafi yadauka sabida taro matan gwamnoni da sanatoci abikin baa magana se tambayar momi suke wai yar gidan waye Anwar ya aura sede tace musu childhood friend na dady dahaka take kashemusu baki Wanda dayawansu haushi sukeji dan be auri yayansuba
Itama momy walima kawai tayi indatace sabida amarya Bata kusane dazaayi event kalakala suko sukace bakomai ayi da suna in amarya tahaihu

Bangaren amarya ilham ko inna ladi takira masu gyara amare dayimusu make off anyimata tsayawa fadinkyan datayi surmené domin bame cewa itace gashi anmata Jan lalle Wanda yakara haskata intakaicemuku inna ladi kwalin tissue taajiye akusa da ita dazaran miyau yataho zebata kwalliyar tagogemata kwalliya akama ilham sosai dan harda gwaggwaro aka nadamata yayin da gashinta aka zubo mata dashi ta kafarda ta hannun dama hotuna masu kwalliyar suka mata awayar da dady yaba inna ladi akan in anshiryata adauketa hoto zeturo a anshi wayar karkuso kuga hotunan domin iya kyau tayi kyau sukansu masu kwalliyar basuyi zaton itace sirikar mister président ba duk da sunga hotunan a social media amma basu kawo ita bace har suka gama suka fice bayan fitarsu bajimawa dady ya ayko abashi wayar inna ladi tamikawa dan sakon yajuya.

koda aka kaiwa dady wayar beyi mamakin kyan datayiba dukda kyannata nayau namusammanne danyasan itadin mekyauce
Da har zekira Anwar yaga kawai gwanda yatura masa ta WhatsApp hakanko yayi shigar hotunan badadewa Anwar yabude ihu yasa acikin abokansa yana my Princess my Princess dakyar naseer yanatsar dashi tahanyar anshe wayar ahannunsa ba naseer ba har sauran abokansa Sun girgiza daganin ilham dayawansu sunjinjina ma Anwar shiko yayi wa hotunan Kiss yafi akirga baa Bata lokaciba gurin yadasu à media

haka taro yaci gaba da wakana har zuwa dare kowa yawatse se dangi nakusa
Sebayan isha dady yasamu kansa yashigo gida momy ce tarufa masa baya bayan yazauna nane yasha ruwan data kawo mishi sannan tace alhaji yabatun zuwa daukar amarya ne naga har yanzu shiru gefen fuskarta yashafa yana murmushi sannan yace senanda sati biyu zaa kawota kallonshi kawai takeyi dan ita yanzu bata yarda da dadynba tasan dole akwai abinda yake boyemata amma yazatayi intayi wari zatajine afili kuwa cewa tayi Allah yanuna mana ameen yabata amsa

Anwar sanda labarin amarya se bayan sati biyu zata tare yasameshi jiyayi kamar zeyi hauka dan bakin cikin amma bayadda zeyi da dady shi yagode ma Allah ma da hukuncin dadyn yazomasa da sauki 😜

Abangaran dady kuwa yayi hakanne dan zuwa lokacin duk yanbiki Sun tafi sabida yayi imani Inde aka kawo ilham akan idonsu to labari mutumin dake china ma seyaji kamar agabansa akayi kunji dattijon arziki.

love you all😘maman yusuf
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_written by Zahra Muhammad mahmud_

*salam sis kuyi hakuri da mistake din danayi narashin fadin Wanda yayiwa ilham waliyyi aranar daurin auranta.wani amintaccen malamin dadyne ya tsaya amatsayin waliyyin amarya.i hope that my apology is accepted*🙏

*page 33*

Anwar ne kwance akan hadadden gadonsa yana baccinsa mecike da kwanciyar hankali.abaccinnasane yayi mafarki da ilham gurguwa dayakewa dariya wai gasunan awani lambu me kyau yayi matashin kai da cinyarta yana fadamata kalaman kauna yayinda itakuma take wasa da gashin kansa tana murmushi miyau nazuba abakinta zuwa fuskarsa amma bedamuba sema kokarin hada bakinshi danata yakeyi azuwan zema Kiss bakinsu nagab da haduwane yafarka abaccin agigice zufa tawanke mishi jiki rawa jikinshi yafara kamar meshin sanyi yayinda cikinshi yafara juyawa kafin wani dan lokaci zuciyarshi tafara tashi dagudu yashiga toilet yafara kwara amai kamar ze amayar da kayan cikinshi ko aman yatsaya hannunsa yake kara sawa abaki wani yataho domin gani yake kamar da gaske ne abin yafaru tube kayan jikinshi yafada shower dirzar jikinshi yake kamar ze sauya fata yana gama wankan yafara brushing din bakinsa seda yaga yana kokarin jima kanshi ciwo sannan yadena. Tun abayin zazzabi yarufeshi me zafin gaske kuma har yanzu zuciyarshi tashi take dakyar yafito daga bayin akan kafet yakwanta domin gadon kyamarshi yake ga zazzabi yanaji amma ko bargo yaki dauka yarufa kuma baze iya dauko waniba dakyar yamika hannu yadauko rumote din ac yakashe ahaka yakwanta agurin yana rawar sanyi yayinda idonshi ke zubar da hawayen bakincikin mafarkin dayayi yayi danasanin ganin gurguwarnan afili da zuciyarsa haka har wani wahalallen bacci yayi nasarar awon gaba dashi

Koda gari waye lokacin yin breakfast yayi kowa yahallara amma banda Anwar ganin shuru befitoba dady yace ihsan taduboshi ko lafiya

Dakinshi tanufa kai tsaye sabida ko kofa baa kullewa agidan sabida security din gidamma sunwadatar turawa tayi tashiga gami da sallama amma baya falo danhaka dakunan baccinshi guda hudu tafara dubawa daya bayan daya se ana hudun tasameshi kwance akasa idonshi yajuye ba baki se fari kawai ga wani kumfa da ya fito abakinsa ihu takwala Wanda yajawo hankalin su dady da security din dake kofar dakin dagudu duka suka shigo dakin abin dasuka gani bakaramin daga musu hankali yayi ba momy kuka kawai takeyi yayinda ihsan ketayata suna jijjigashi suna Kiran sunanshi
Dady ne kawai me karfin halin Kiran family doctor din gidan baayi minti gomaba yakaraso dasauri yasa aka dauki Anwar akamaidashi kan gado gwajegwaje yafara inda yagano suma yayi allura yayi masa sannan yadaura masa drip suka koma gefe suna jiran farkowarsa domin doctor yabada tabbacin ze farka akowanne lokaci
dukansu tambayar junansu suke meyasameshi Bayanjiya lafiya suka rabu dashi abinda basu saniba shine bayan mafarkinshi nafarko yadawo kasa yakwanta wani mafarkin yayi Wanda yafi nafarko domin nabiyunne suke excanging na miyau shida ita yayin da gefe guda kuma yana making love da ita har yanamata kuka dan dadin dayakeji. Tofa koda yafarka yaso shiga bayi amma yanayin zazzafan zazzabin daya rufeshi yahanashi samun damar hakan shine dalilin sumannashi
suna nan zaune har azahar sannan yafarka koda farkawarsa da amai yatashi Wanda yashiga kwarashi bakadanba hankalinsune yakara tashi koda yagama aman bayi yanufa yafara brush hmmm intakaicemuku Anwar harda wankan tsarki🙈
Chapter 6 · 0% Book details