← Book details Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 22

Sashe 12

Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iska ya fesar sannan yaruntse idonshi ranshi namishi kuna zuciyarshi kamar zata tsage. Azuciya yafara mgn haba dady meyasa zaku rusamin farincikina twince sune rayuwata amma kunrabani dasu ilham ninasan basonta nakeba amma zuwa yanzu inason ganinta. Wasu hawayene masu dumi suka gangaro akan fuskarsa tabbas yasan wannan shirin nadadyne dan yayi imani dady yafi kowa kinsa tashi yayi afusace yabar part din dakinshi yanufa yana shiga wayarsa yadauka yakira naseer awaya yana shaidamasa abinda ke faruwa
naseer seda yatausayamasa sabida twince kowaye mahaifinsu baze so suyi nisa dashiba hakuri yadunga bashi yanacewa horone su dady sukemishi abisa wulaancin dayayiwa ilham Wanda yasan nanda dan lokaci zasu hakura sudawo mishi da matarsa sallama sukayi

*Bayan wata biyu*

Zuwa yanzu Anwar yatabbatar da ilham tamishi nisa gaba daya yazauce akanta ita da yaranta kullum cikin kallon hoton daya musu yakeyi

kuma har yanzu iyayensa sunki suce masa komai gameda ilham da yaransa
harga Allah yanzu yasoma tausayin ilham amma basonta yakeba( nace kuji wawa )

*Ilham*

acikin watanni biyunnan anyi nasarar tsaida miyaun datake zubarwa haka shima lalurar yoyon fitsari andade da maganceta dayake akwai kudi domin baabinda dady betana darmusuba
haka suma su twince kullum kara wayo sukeyi abin gwanin shaawa kuma itama ilham yanzu tagane su amatsayin yaranta dan har wasa take musu

yaune aka saka ranar yima ilham ayki wajen ganin anmikar da kafarta dakuma hannunta wani injine zaa sata aciki na tsawon kwana uku ana kuma sa ran dazaran tafito dayardar Allah zata warke. Dan haka tun safe suke tawaya da inna da su dady tana fadamusu abinda ake ciki duk da shima doctor din yana waya da dadyn
tun zuwan dasuke asibitin doctor betaba kallon ilham ido cikin idoba sabida becika kallon mataba
yau anyi saa suna shigowa office dinshi idonshi ne yasauka anata afirgice yatashi yanakallonta badan komaiba sedan tsananin kamar datakeyi da mahaifinsa tirkashi wai waye doctor din ilham ne

Maman yusuf
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Zahra Muhammad mahmud

*page 51-52*

Har suka karasa cikin office din doctor natsaye yakasa zama har seda inna tafara gaisheshi sannan yadawo da tunaninsa zama yayi yana cigaba da kallon ilham

Bayan yadauko file na ilham ne yakara lura da sunan dake rubuce ajiki ilham bukar shettima. Tabbas zatonshi yazama gaskiya amma zebar komai har zuwa ilham tasamu sauki rubuce rubuce yayi sannan yaba inna madarar dazata dunga ba twince nan da kwana ukun

Anshigar da ilham cikin machine dan haka inna direba yadawo da ita gida ita dasu twince zuciyarta cike da adduar Allah yasa adace.

*Doctor Adnan imam shetima*

Shine cikakken sunan doctor dake duba ilham dane ga alhaji imam shetima saurayine matashi Wanda shekarunsa bazasu gaza 35 ba shikadaine agurin iyayensa kallo daya zakama adnan kasashi acikin jerin kyawawan maza domin kyakkyawane na ajin farko bashida son hayaniya kwatakwata shiyasa beson zama à Nigeria. Mahaifiyarsa sunanta hajiya hauwa macece me kirki haka shima mahaifinsa Wanda yanzu haka suke zaune agarin kaduna tunbayan barinsu garinsu na aynihi wato meduguri asakamakon yakin daake a yankin

Adnan yayi primary da secondry schools dinsa duk agarin meduguri kuma Allah yaba mahaifiyarsadamar dauko jakar takardunsa shida mahaifinsa lokacin dazasuyi hijira dan haka kobayan zuwansu kaduna basu sha wata wuyar rayuwaba mahaifinsa yasamu ayki a nnpc kuma ana bashi albashi me tsoka shiyasa yanemar masa Abu zaria inda acanne yayi degree dinsa nafarko
Lifes move on mahaifinsa yazama hamshakin mekudi dan haka yakaishi kasar india domin yakarasa karatunsa n'a doctor acan
Duk da yawan tarin dukiyar mahaifinsa kullum cikin damuwa yake da bacewar dan uwansa bukar Wanda yanemeshi har yafidda ran ganinshi suko dama iyayensa yasan Sun mutu dan haka yake musu addua amma rashin sanin labarin kaninsa nasashi acikin damuwa dan so tari ze kulle kanshi adaki yaci kuka
Halin da mahaifinsa keciki yana dagamasa hankali har yakejin da yanada ikon cirewa mahaifinsa damuwarsa dayayi

bayan wasu shekarune mahaifinsa yafada harkar siyasa inda ananne suka hadu da mr président wato dadyn Anwar
Mahaifin adnan shine yadauki nauyin campagne din dady har kuma Allah yasa akayi nasara dady yaso yabashi minister naman petur amma yaki tun farko hawan dady mukamin Abban adnan yace bashida raayin mukamin amma shi ya yarda yadunga basa kwangila haka ko akayi ko lokacin auren Anwar baya kasarne yana saudiyya shiyasa be hallaci bikinba kuma shi baya hawa social media bare yasan wacece amaryar Anwar shide kawai dady yacemishi tsuntota yayi kuma sunanta ilham danse akwanakinannema yake shaidamishi Bata da lafiya shine yahadashi da adnan dan fannin yakaranta
Tsakanin adnan da Anwar basu San junaba dan iyayensune suke burin su hadasu Abota.

har kudi masu tsoka Abban adnan yasa gaduk Wanda yaga dan uwansa ko yaji labarinsa amma har zuwa yanxu bawani bayani yahakura yabarwa Allah

*cigaban labari*

twince koda suka daina shan nono basu damuba domin tun asalinsu masu hakurine shiyasa inna bata samu matsala dasuba

*Nigeria*
Anwar yanzu ko aski bayayi zuwa yanzu ko office yadena fita se mataimakinsane ke gudanar da komai.
da yadauka iya su twince kawai yakeson gani se yanzu yatabbatar da basu yake soba mahaifiyarsu yake da bukatar gani kuka da magiya yayiwa su dady ba iyaka akan sudawo masa da iyalinsa amma ko takansa dady bayabi ihsance kawai take tausayinsa take bashi shawara dayayi hkr komai lokacine shide sede yakalleta kawai amna bajinta yakeyiba domin yanzu yagama yarda 100% ya kamu dason ilham Wanda ko kansa bayaso kamar haka burinshi su sanar dashi inda take dan yanemamata Lfy sabida bayason taji lbrn abinda yadunga mata abakin wani shida kansa yakeson shaida mata kuma yanemi yafiyarta amma su dady sunki bashi hadin kai. Ko abinci yadena ci sosai sede ihsan tamatsamasa yaci domin su dady gaba daya sunfita harkarshi
kuma kullum suna waya da inna sunajin halin da ilham take securityn da dady yahadasu dasu sune ke daukar twince ahoto suyima dady sending through WhatsApp dan haka baya kewar jikokinshi tunda kullum seya gansu
Anwar ne kadai ke haukarsa

*India*

bayan kwana uku yau ne zaa ciro ilham acikin machine din da akasata. tun asuba su inna suka zo asibitin suna jira.

Damisalin karfe takwas nasafiya doctor adnan yaciro ilham.

hasbunallahu wani imal wakil wala haula wala kuwwata illa billahil azim

ilham ce nagani tsaye akan kafarta hannunta daya lankwashe shima asake kai kubarni nakara yiwa Allah kirari

lalle Allah shine Allah kuma shine meyin yadda yaso Alokacin dayaso babu meyiwa dan Adam baiwa se Allah

ganin ilham danayi yasa na kara tsoron Allah
dakafarta tafito inda su inna suke dakon futowarta doctor nabinta abaya
inna naganinta sujjada tayi ga Allah sannan takarasa da sauri tarungumeta
tabbas ilham bata manta innaba dan haka itama rungumeta tayi tana kuka
ihamce ke fadin Alhsmdulillahi Allah nagodemaka daka azurtani dasamun Lfy. inna seda takusan shidewa sabida Jin ilham namagana cikin muryarta kamar ana busa sarewa rungumeta inna tasakeyi tana fadin lalle Allah shine abin godiya ilham
waige waige ilham tafara Wanda inna tafahimci yaranta take nema dasauri taja hannunta zuwa inda aka ajiye su twince dasauri ilham tasa hannu tadaukesu duka subiyu kuka takara fashewa dashi nafarincikin ganin tadauki yaranta da hannunta Wanda da sede amiko mata kissing dinsu tashigayi kamar zata lashesu suko su twince se dariya sukeyi nace ikon Allah
doctor ne yashigo sannan yanemi guri yazauna yana murmushi yace to maman twince Lfy tasamu kuma se kuka nide karki koyama twince kuka sabida basayi murmushi tayi sannan tafara yimasa Godiya..
magungunan dazata cigaba dasha yabasu sannan yamusu fatan alkhairi suka hadayanasu yanasu suka wuce masaukinsu

maman yusuf

[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Zahra Muhammad mahmud

*page 53-54*

Tunda ilham tasamu sauki kullum suna waya dasu momy abin bakaramin dadi yayiwa dady ba momy ma ji takeyi kamar tayi tsuntsuwa taga ilham

Dady sunyi mgn da doctor inda dady yanemi daya nema masu ilham biza daga india zuwa saudiyya domin suyi umara

Ayko hakan akayi domin ilham basu kuma sati guda agarin india ba se asaudiyya
Tun isarsu garin madina ilham ke kuka na farinciki kwanansu shida amadina suka Isa makka
Ilham tayi addua sosai aciki kuwa harda Allah yabayya namata yan uwanta sabida inna tafadamata komai game da tsuntota da dady yayi shiyasa Bata da sukuni illa Allah yabayyanamata danginta

Tafiyarsu zuwa saudiyya tare da doctor adnan akayita
Dan haka yanzuma shi dady yawakilta akan yanema musu biza zuwa UK sabida yanason ilham taci gaba da makaranta acan

Dan haka adnan beyi wasaba yayi abinda dady ya umarceshi

Koda zuwansu birnin london basuyi sati biyu ba adnan yakai ilham wata makarantar secondry tambayoyi suka mata Wanda seda sukayi matukar mamakin amsoshinta dan har inda basu tambayaba take kaimusu amsa lalle Allah me girma da daukakane gashi yaba ilham ilimin da bawanda yayi zato

Kudi dady sosai yasaki kamin ayiwa ilham certificate din primary da na junior waec domin a ss1 akasata

Sosai ilham take maida hankali ga karatunta Wanda take ganin dashine zata taimaki iyayenta😭

So tari intadawo gida zata zauna tayi shuru Tana tuna wasu abubuwan dasuka faru wasu tamanta wasu kuma bata mantaba
Duk abinda anwar yamata nacutarwa tamanta shi sannan mutuwar iyayentama bata tunaba hatta auran da ke kanta seda inna tamata Karin haske akai amma fa yanbiyu Tana matukar kaunarsu kuma tarasa dawa suke Kama itade tasan bada ita suke kamaba

kamannin anwar gabadaya tamantasu shiyasa ko tunaninshi batayi. kawai abinda tadaukarwa ranta shine ko waye baban su twince gaskiya baya kaunarta itada da yaranta Wanda Zuwa yanzu tanajin tsanarsa azuciyarta sabida tayi imani dayana sonsu dayazo inda suke musamman data samu lfy

*bayan shekara daya*

su twince sunyi wayo komai sunaci basu fiye damuwa da nonoba shiyasa inna tashaidawa momy momy tace ayayesu
zuwan daddy da mommy hudu gurin su ilham suna dubasu shima doctor Adnan yana yawan zuwa dubasu Dan soyake yabi aynihin tarihin ilham yasan wacece ita

Yanzu ilham na ss3 inda dady yace inta kammala ss3zata dawo Nigeria abun yayiwa su ilham dadi dan harga Allah sungaji da zama akasar dabatasuba

Ilham tayi kyau matuka bame cewa ajikinta su twins suka fito tsayawa fada muku kyan da ilham tayi da cigaban datasamu page dinnan yayi kadan sosai dady yake sakar musu kudi

Twince koda aka yayesu basa rigima tafiyarsu sukeyi ko ina gasu tun suna yara sun taso da kaunar junansu dan ko kuka daya yakeyi se dayan yatayashi

*Anwar*
Chapter 12 · 0% Book details