← Book details Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 22

Sashe 16

Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani katafaren asibiti suka nufa Wanda tunkafin su ISO tuni anyi waya asibitin danhaka koda zuwansu ilahirin maaikatan gurin suna waje suna jiran akawosu

kai tsaye emergency akawuce dasu akahana su ilham shiga awaje suka tsaya suda securities dinsu

Tuni akayi waya office din daddy akasanar dashi cewa yazo fa gida balfy yanxu haka suna asibiti

Hankalin daddy ne yatashi matuka yana tunanin meyafaru da family dinsa dawannan tunanin yakaraso asubiti shida makarrabansa

dasu ilham yaci Karo akofar emergency ward
Ihsan dagudu tafada jikin daddy Tana kuka cikin kukantane take fadamasa abinda kefaruwa
jikinshine yafara rawa alamun zefadi dasauri security dinsa yazaunar dashi

doctor ne yafito daga dakin yayinda abayansa wasu nurse ne guda hudu suke gunguro mommy akan gado hannunta daure da drip

agigice sukayi kanta wani daki aka kaita na musamman
bayan ankwantar da ita doctor yafarayiwa daddy bayanin abinda ke faruwa
Dan durkusawa yayi sannan yafara mgn Kamar haKa

ranka yadade madam bawani abubane yasameta illa frgita datayi asakamakon ganin abinda yafirgitata wanda insha Allahu nanda wasu lokuta zata farka dan tuni mukashawao kan matsalar
shikuma yallabai anwar am sorry to say

to say what!!!! Inji daddy
afirgice doctor yace
am Sorry sir but anwar yana cikin halin mutuwa ko rayuwa domin zuciyarshi takamu da matsanancin ciwa Wanda single mistake zaayi ta buga sannan ahalin yanzu yakamu da ciwon paralyse

gaban dadine yayi mummunar bugawa yayinda ihsan tarushe dawani matsanancin kuka. itako uwar gayya wato ilham wani malalacin murmushi ne yabayyana akan fuskarta Wanda faruwar hakan akan idon mommy Dan tuni tafarka Tana sauraronsu

daddy ne yamike yace doctor yakaishi yaga anwar
karaf mommy tace nima zani dasauri suka waiga suna kallonta Dan basusan ta farkaba
daddy ne yaje yarungumeta yayinda itakuma tafashe da matsanancin kuka ihsan ma rungume mommy tayi Tana kuka doctor ne yacirewa mommy drip din hannunta yayin dasu daddy suka matsa Dan doctor yadubata
bayan yagama dubatane tayi yunkurin tashi dasauri ilham takai Hannu domin taimakamata hannu mommy tadaga mata alamar tabarshi ihsan ce taruko mommy ta Mike abun yadaurewa daddy Kai ammayayi shuru mikewa sukayi suka nufi dakin da anwar yake ga mamakin daddy seyaga ilham tanemi kujera tazauna hankalinta kwance
mamakine sosai ya bayyana afuskar daddy koda ilham tawaigo taga yana kallonta dauke kanta tayi yana kallonta har yakarasa fita

duk dauriyar daddy dayaga yadda anwar yakoma seda yafashe da kuka kamar yaro su mommy da ihsan ma kukan sukeyi

sefito dasu akayi adakin Dan baason hayaniya agurin dayake

koda suka dawo dakin da ilham take ga mamkinsu waya takeyi da ameera se dariya takeyi bamecewa a asibiti take kuma mijintane Mara lfy

ganinsune yasa tayi sallama da ameera tayimusu sannu da zuwa

daddy ne yaamsa amna kan ihsan da mommy ko kallo bata ishesuba

.suna asibitin har zuwa dare sewajen karfe goma sha biyu nadare suka wuce gida harda mommy sabida asibitin baa jinya

*bayan wata biyu*

anwar yanzu har yanzu anwar ciwo se abinda yakaru babu wani sauki

itako ilham tunda taje asibiti so daya bata sake komawaba amma kullum setayi kwalliya ta tafi mkrt

abun yanama su daddy ciwo sosai babuma kamar mommy wacce tafi kowa jin haushin ilham din amma sabida rashin kunya irinta ilham kullum setaje take gaishesu

su ameera dasu Adnan da daddy nsa da mommy sa dasu megari da yan gidansu moneer kowa yaje duba anwar yafi akirga
koda daddyn Adnan yatamvayi ilham Tana zuwa gaida mijinta kuwa budar bakinta secewa tayi aa ita meze kaita gurin Wanda bataso dauketa daddy yayi da Mari ze karamatane mommy nadnan tarikeshi
fada yashigayi ta inda yashiga batanan yake fitaba daga karshe yace duk sanda bataje ta dubosaba bashi babu ita abinda daddy besaniba tuni daddydaddyn anwar yagama shirin fita da dansa kasar Egypt domin aduba lfyrsa adaren ranar

ayko hakan akayi adaren ranar jirgi yadaga da anwar da mommy da ihsan da daddy zuwa kasar Egypt

se awaya daddy yake shaidawa daddyn Adnan fatan alkhairi yamusu gami da cewa next week sunanan zuwa suma

itako ilham batasan basa nan ba seda taje gaishesu security dake gadin kofar shiga part din yake sheda mata abinda ke faruwa

bataji dadin abinda sukayimataba narashin yimata sallama jiki bakwari takoma part dinta inda su twins suke ta waansu
kwanciya tayi tashiga tunani gaskia tasan bata kyautawa su daddy ba batayimusu adalciba sabida basu cancanci haka agurintaba to amna yataiya dansune bataso kuka tafashe dashi afili tanayiwa anwar Allah yaisa Dan dashi badansu mommy bane baabinda zeshiga tsakaninta dasu narashin kyautawa
kuka tayi me isarta sannan tamike tanufi daya daga cikin dakunan part dinta Wanda bata taba shigarshiba tsawon zamanta agidan koda shigarta dakin kamshin turaren anwar yakeyi jin kamshinne yasa zata juya da sauri idontane yasauka akan wani littafi akan side drower na gadon dasauri taje tadauki littafin haka kawai taji tanason karanta abinda keciki Dan ta Lura diary ne
fara karantawa tayi
abinda tagani a littafinne yarura tsananin kiyayyar da takewa anwar azuciyarta domin kuwa gaba daya labarin haduwarshi da itane a littafin harda irin azabar daya dunga ganamata hawayene yake zuba afuskarta jin first night dinta a toilet sukayishi bakincikine yaziyarci zuciyarta tabbas tayarda anwar ba masoyintabane duk da a diary din yafadi irin tsantsan kaunar dayake mata amma bata Lura dashiba kiyayyar daya bayyana yamata itace tafi tsayamata arai daukar littafin tayi ta tafi dashi dakinta yayinda taci gaba da kuka akan rashin kyautawar datayiwa su daddy
Daga karshe yanke shawara tayi akan gobe zata bar musu gida sabida zamanta da anwar yakare Ashe shidin bakin azzalumine haba no wonder taji tatsaneshi da yawa

maman yusuf
[3/13, 07:09] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Zahra Muhammad mahmud

*page67-68*

Tun karfe takwas nasafe ilham tagama shiryawa tashirya su twins tadebi kayan sawarsu da duk wani Abu me amfani takira security yafitar mata dasu zuwa mota itama fitowa tayi rike dasu twins suna ganin tafito suka bude mata kofar baya tashige ita dasu twins Kai tsaye kaduna tanufa

Se sha biyu na rana suka isa kaduna
Sallama tayi tashiga falom gidan yayin excode dinta suka shigo mata da kayanta sallamarsu tayi suka juya Abuja

Mommy tunda tashigo take kallonta baki bude
Guri ilham tasamu tazauna sannan tagaida mommy
Bata amsa gaisuwarba tashiga jero mata tambaya
Ilham mekikeyi a nigeria bayan anwar bashida Lfy yana Egypt zaman mekikeyi baki bisu kuntafiba
Baki ta turo sannan tace ni ni ni bansan suntafiba ay
Salati mommy tayi tasanar da ubangiji
Sannan tace ilham Anya kinada imani kuwa dama Ashe baki janye wannan maganar tsakaninki da anwar innalillahi wainna ilaihir rajiuna ilham tafadi da karfi
sannan taci gaba wlh ilham kingama asara duniya da lahira yanzu irin wannan sakayyarce tadace da mahaifan yaronnan yau ko yau ko yankaki anwar yakeyi ki mutu ki dawo bedace da abinda kike masa ba

Wlh ko rantsuwa nayi bazan Yi kaffaraba ciwon anwar da hannunki aciki

Tunda baki da hankali duniya zata koyamiki
Kina da yara dashi Amman kike neman kashemusu mahaifi wlh insukayi wayo suka fahimci kece silar mutuwar mahaifinsu ko kallonki bazasuyiba
tunda haka kika zabawa kanki kije kiyi Allah yabaki saa
mommy nagama fadin haka tatashi taja hannun su twins suka shige daki suka bar ilham zaune afalo kamar mayya

Hawaye takeyi kamar fanfo tabbas jikinta yayi sanyi dajin kalaman mommy kuma tayarda tayi kuskure sosai su daddy basu can canci hakaba kuka takeyi kamar ranta ze fita

Gashi yanzu su daddy sunyi fushi da ita uwa uba ga hakkin mijinta har ga Allah yanzu tausayin anwar yakamata tuno irin wulakancin data dunga yimasa yana hakuri tayi wani sabon kukanne yasake kamata lalle tayarda in anwar yamutu itace takasheshi Allah kagafartamin tafadi afili
Babu abinda inta tunoshi yakemata ciwo ayanzu irin yadda mommy taganta Tana rawa alokacin da anwar yafadi ya ilahi cigaba tayi da kukanta harsu mommy da daddyn Adnan suka shigo falon batasaniba seda daddy yayi gyaran murya sannan tadago dasauri
Tana ganinnshi dagudu taje tarungumeshi Tana kuka Tana cewa daddy karkace komai wlh nagane kuskurena kugafarceni wlh bazan Kara ba natuba kakira daddyn anwar kace suyafemin wlh bazan kumaba nayi nadama kukan datakeyine yasa jikin daddy yin sanyi rungumeta shima yayi sannan yace to yaisa haka naji share hawayenki kuma naji dadi dakika gane kuskurenki dawuri sede fatan Allah yasa agurin mijinnaki baki makaraba Dan iyayensa nasansu zasu yafemiki kitayin addua

haka suka sata agaba sunatayimata nasiha Wanda bakaramin shigarta tayiba

Koda tazo bacci kasayitayi tunanin anwar kawai takeyi da irin cin kashin da tamasa
takosa tasashi a idonta kozata samu sassauci azuciyarta danjitakeyi kamar zuciyarta zata fashe haka takwana Tana kuka

*EGYPT*

Tunda suka isa likitoci sunfi goma akan anwar Wanda yake asume suna kokarin ganin numfashinshi yadedeta allurai akayimasa sannan suka daura masa drip daga karshe suka turashi cikin wani machine Dan yataimaka Wajansashi yafarfado dansu sami damar gudanar da aykinsu

gidan dasuka sauka su daddy suka koma sabida baa zama a asibitin

tunda suka shiga gida ihsan da mommy suke kuka dakyar daddy yashawo kansu sukayi shuru wanda koshi kanshi dabasa gurin kukan zeyi Dan dauriya kawai yakeyi

hirar rashin hallaccin ilham sukeyi mommy tace wlh alhaji bantaba tsammanin ilham ko wuta mukace tashiga zata musamanaba amma wai kirikiri tanuna bata kaunar gudan jininmu tabbas ilham tacika tsintacciyar mage kuma tabani mamaki

daddy ne yakatseta dacewa ku kwantar da hankalinku ilham baita tadorawa anwar ciwoba kuma baitace zata yayemasa ba se Allahn daya dora masa Dan haka banaso kuna damun kanku kawai muyiwa anwar addua shine mafita

koda dare yayi basu rintsaba sallah sukai tayi tanafila dannemawa anwar sauki agurin Allah.

koda gari yawaye suka nufi asibitin
babban likitanne yataresu
bayan sungaisane yake shaidamusu anwar yafarka

murna ce takamasu gabadaya suka rungume juna
likitan yaci gaba dacewa tun karfe uku nadare yatashi amma tunda yafarka yanata kiran sunan ilham har zuwa wayewar garinnan duk da maganarshi bata fita sosai asakamakon paralyse din daya samu
pls wacece ilham dinnan

kallonkallon suka shiga yiwa juna cande daddy yace matarsace
good inji likitan sannan yadora dacewa to magana tagaskiya danku yana matukar kaunar wannan ilham din kuma rashinta akusa dashi ze iya jawowa arasa Ransa
agigice suka Kalli juna
likita yaci gaba
azahirin gaskiya inda hali kukawomasa ita kusadashi

sabida semun samu natsuwar zuciyarsa sannan mudorashi akan magani zuciyarsa ta kumbura sosai dole da ita zamu fara sannan muzo kan paralyse din dayayi
Chapter 16 · 0% Book details