← Book details Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 22

Sashe 1

Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Compiled by Princess Aysha Muhammad

[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*Bismillahirrahmanirraheem*
*Nagodewa Allah mekomai me kowa daya bani ikon rubata wannan littafi nawa me suna *Allah gatan bawa, ina rokon Allah yasa littafina yasamu karbuwa agurinku masu karatu,innayi kuskure kusanar dani da gaggawa domin in gyara ,dan adam ajizine nagode.*

*Page 1-10*

Azaune take akan dakalin kofar gidansu hannunta dauke da kara tana wasa dashi yayin dasauran yaran makwabtansu suma suke nasu wasan ita kuma tana binsu da ido domin ita Bata da yencin shiga cikinsu tayi wasan yarinyace yar kimanin shekara takwas da haihuwa wacce Allah yajabceta da lalura irinta zubar da miyau sanna kafarta daya dahannunta daya duk ashanye suke intana tafiya tana jefa kafarne yayin da hannun yake makale a kirjinta
wannan lalurarce tasa yara da sauran mutanen garin kyamatarta ko wasa basayi da ita sede tazauna agefe tana kallonsu

*Asalin labarinta*

Ilham bukar shetima shine sunanta na aynihi mahaifinta malam bukar shetima hafaffen garin medugurine acikin garin bama inda fadace fadacen daakeyi ayankinsu yayi sanadiyyar mutuwar iyayensa hakanne yasa yayanke shawara shiga cikin ayarin yan gudun hijira domin yin hijira daga yankinnasu. Bashi kadai bane agurin iyayannasa su biyu ne shida dan uwansa mesuna imamu amma rudin dagarin ke ciki yasa suka bacema juna yayi kukan bakin cikin mutuwar iyayensa da kuma bacewar yayansa Wanda besan awanne hali yakeba shiyasa yarungumi kaddara yayi hijira
Acikin ayarin yan gudun hijirarne yahadu da wata budurwa wacce itama ankashe iyayenta( Bata da kowa )me suna maryam tunda suka hadu yake tausayamata sabida ita macece shiyasa yashiga dawainiya da ita har suka shigo garin kano bayan ansaukesu asansanin yangudun hijirane washe gari yakirata gefe inda yashawarceta dasuyi aurene zefi kulawa da ita sabani basu da aure Batare da Bata lokaciba ta amince inda dattawan cikin yan gudun hijirar sukadaura musu aure bayan yabata sadaki nera dubu biyar
tundaga lokacin yadukufa gurin kwadago acikin gari har Allah yataimakeshi yakama masu hayar gida me daki biyu acan garin wudil sabida beda halin kamamasu acikin gari be kaunar zamansu acikin sansanin "yan gudun hijirarne shiyasa yakamamasu haya bayan tarewarsu badadewa Allah ya albarkacesu dasamun karuwa ta cikin suncigaba da kulawa da cikin har zuwa haihuwa inda Allah yasa maryam tahaihu lafiya tasamu "ya mace yarinyar kyakkyawace ajin farko sabida daga uwa har uban shuwa arabne sede kallo daya zaka mata kafahimci Bata da lafiya maana nakasasshiyace basuyi kasa agwuiwaba suka samata suna inda taci sunanta ilham bayan suna ilham iyayenta sundukufa neman magani amma duk inda sukaje amsa daya akebasu bazata warkeba tunda da lalurar aka haifeta hakan yasa suka hakura suka mikama Allah lamarinsu
ilham na dada girma lalurarta nakara bayyana ahaka har aka yayeta bayan yayetane Allah yasake basu wata 'karuwar inda wannan haihuwarma tasamu mace suka samata sunan mahaifiyar bukar fateema suna kiranta ameera bayan haihuwar ameera basu sake haihuwaba har zuwa yanzu da ilham kede shekara takwas ameera kuma biyar
rayuwa suke mecike da tsanani sabida malam bukar me karamin karfine wani lokacin ko yafita bayasamun dakon haka yake dawowa ahaka yakokarta yasa su ilham awata makarantar gwammanti ta pramary ilham na aji uku ameera aji biyu duk à tunaninsu ilham bazata iya komai amakarantaba amma Allahyataimaka yasa tana ganewa sede ko tambayarta akayi bazata iya fadaba sede gwaranci dan harshenta akarye yake. ko amakaranta tsokanarta suke yara sede ameera tatunda taremata dukda itama bawani wayo garetaba ita ilham kuwa sede taita dariya miyau nazuba tadauka wasa suke mata, to ko sundawo gidama yaran unguwa bakyaleta sukeba shiyasa mahaifiyarsu batason ilham nafitowa sabida ko ina hantararta akeyi tun mamansu na magana har tadena sabida tasan *Allah gatan bawane*

*Cigaban labari*

tanana zaune yaran suka fara tsokanarta itako se dariya take harda kwantawa miyau nazubowa daga bakinta, jiyo hayaniya da mahaifiyarta tayine akofar gida yasa tayi saurin lekawa daki inda tabarsu suna wasa da ameera ga mamakinta ba ilham sede ameera datakeyin homeworke dinta dasauri tadauki hijab dinta tasa tayi kofar gida sabida ta tambatar da ilham akeyi ayko ilai tana fita tayi tozali da ita tana dariya yara natsokanarta suna watsamata kasa bakinciki besa tayi yunkurin hanasuba illa iyaka dauko ilham datayi tashiga gida daita itako baabinda yadameta se dariya take .

love you all maman yusuf✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
_Writting by Zahra Muhammad mahmud_

*Page 11-20*

Suna shiga gida kai tsaye toilet tashige daita tsifa tafara yimata sannan tawankemata kai Wanda yasha kasa sannan tayimata wanka tafito daita daki takaita sannan tayimata shafa tasauyamata kaya karkuso kuganta à time din kamar kadauka kagudu sabida kyan datayi.
Abinci tazubo mata tafara Bata abaki Wanda ita ilham har zuwa lokacin dariya takeyi sabida intafara dariya tana jimawa bata denaba itako mahaifiyarta kwalla kawai take sharewa natausayin diyar tata

**************
Yauma kamar kullum suntaso daga makaranta, ameera narike da hannun ilham suna tafiya yara suna tsokanarta ameera sekuka take musu tana dan Allah kudena metayimuku Wanda agefe daya ita wacce abin yashafa inbanda dariya baabinda takeyi ganin hakane yasa yaran suka cigaba da tsokanarta ahaka har suka karaso gida babansu suka tarar akofar gida yana alwala zashi masallaci ganinshine yasa yaran komawa da gudu sabanin da dahar cikin gida suke binsu
Sannu baba mundawo cewar ameera sannunku mamana kushiga gida ina zuwa bari nayo sallah yafadi tareda shafa kan ilham wacce takafeshi da ido ba um ba umum
Dashigarsu gida dakin mamansu suka shiga suka tarar da ita ta kabbara sallah ameerace tayi kokarin zuwa daukar buta itama tayo alwalar tazo tabi bayan mamanta sukayi sallah. Tare da yima ilham adduar samun sauki.itako ilham kiciniyar cire safa take har suka idar bata cire KO guda dayaba ameerace taamsa tacire mata sannan mamansu tacire musu Uniform Wanda gaban rigar ilham jike yake da miyau Wanda hakanne yatilastawa rigar kodewa daga gaban wanka tamusu sannan tajika musu garin rogo suka sha
bayan sungama sha ne malam bukar yashigo gida fuskarsa ba walwala kan tabarmar dasuke zaune yazauna cike da kulawa maryam take tabayarsa malam meke faruwa naga ranka abace. Yace haba maryam dama haka yara suke biyo ilham baki taba sanar daniba kamar sunga dodo Sun m'aida ita kamar abin wasa haba maryam kinyimin adalci kenan. Maryam wacce tunda yafara magana take zubar da hawaye dakyar tabudi baki cikin kuka tace haba baban ilham menene amfanin insanar dakai indaga hankalinka yarannan badenawa zasuyiba konakai kara gun iyayensu basa kwabarsu to yazanyi ilham de ba ita tayi kantaba Allah ne yayi ta kuma shi dayayita ahaka nasan yanasane daita kuma nayi imani shine gatanta danhaka kaima kazubama sarautar Allah ido inda rabon musha kallo nangaba zakace nafadamaka takarasa zancan tana kuka. Jin maganganunta yasanya jikin bukar sanyi cikin sigar rarrashi yafara magana nafahimceki maryam kuma nima zanyi yadda kikace amma kinsa ba dadi adunga tsokanarta tace hakane amma bamuda yadda zamuyi sede mufadawa Wanda yayita
haka sukai ta tatyaunawa agame da matsalar ilham har akakira sallar laasar suka tashi domin bada fatali.

love you all 😘 maman yusuf
[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_writting by Zahra Muhammad mahmud_

*Page 21*

*Bayan shekara uku*

Kwanci tashi bawuya agurin Allah yaune ranar dasu ilham suka gama pramary school ita da ameera sabida tun suna aji hudu akayima ameera jumping takamo ilham.cike suke da murna daganin ranar dagasu har iyayensu murna suke harda ilham wacce batasan meyakawo murnarba.atamfa 'yar leda babansu yasiyamusu akadinkamusu Riga da siket ba laifi sunyi kyau kuma sunji dadin kyautar da babannasu yamusu na atamfar,
Chapter 1 · 0% Book details