← Book details Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 22

Sashe 3

Allah Gatan Bawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isowa asibitin dakin da mama take suka nufa auna ta likitan yafarayi da mamakinsa yaga ba numfashi atare daita hankalinshine yafara tashi yana gudun kar ace ita ma babu ita awo n'a musamman yashiga yimata sede yamakaro Allahn dayayita yafishi kaunarta innalillahi wainnailaihirrajuiun itace kalmar dayake nanatawa zufa ce tashiga keto mishi ta koina dubansa yakai gun ameera wacce har Yanzu kukan rashin ganin ilham takeyi. Tausayinta ne yakamashi Jan hannunta yayi suka bar dakin bayan ya rufe gawar umman wasu nurse guda biyu yagani yabasu umarnin akai gawar umma mutuware
Office dinshi yashiga da ameera bayan Sun zaunane yafara magana " kiyi hakuri kinji kowa dakalar kaddararsa ketaki kaddarar Bata da kyau amma kigode Allah kinji .kai kawai tadagamasa sabida Bata fahimci meyake nufiba duba da kankantar shekarunta. Address dinsu yasake tambayarta tasanar dashi Jan hannunta yayi suka sake fita kai tsaye unguwarsu yaje da ita wani makocinsu yasamu mesuna malan sule bayan sungaisane yake tambayar sa shin koyasan wannan yanuna ameera dago kai malam sule yayi yakare mata kallo sannan yace yasanta yar gidan malam bukarce inafatande lafiya. Lafiya kalau likita yabashi amsa daganan likita yakoro masa bayanin abinda yafaru harda mutuwar umma se anan ameera taji ummansu itama tarasu kuka tasamusu me tsuma zuciyar duk wani me imani shikanshi malam sule kukan yakeyi yakara da fadin jiya jiyannan mutanennan sukabar gidannanfa yanuna gidan ashe tsautsayine yafitardasu Kuka yasake barkewa dashi
likitane yakatseshi dacewa malam ba kuka zakayiba sonake ka kaini gidan megari inyimishi jawabi sabida asan yadda zaayi da gawarwakin. Tashi malam sule yayi gami da fadin biyoni muje gurin me garin. Kama hanya sukayi likita narike da hannun ameera ,akafa sukaje gidan megari dayake banisa bayan sungaisa dame gari sukayimishi bayanin abinda ke tafe dasu megari bakaramin girgiza yayi da labarinba duk da besan malam bukar amma yatausayawa rai shela yasa akayi agari akan jamaa suzo fada zaayi janaiza sannan yamike yabi doctor suka dunguma zuwa asibitin da isarsu akasaka gawarwakin amota bayan doctor yagama daukar hotonsu awayarsa sannan yayi cikecike a file dinsu. Kai tsaye kofar gidan megari akayi dasu Wanda yacika da jamaa cikin gida aka kaisu akamusu wanka megari yasallacesu aka kaisu gidansu nagaskiya
Wayyo rayuwa kowa nagurin yatausayawa wainnan bayin Allah se addua ake musu nasamun rahamar Allah.bayan anyi adduoine doctor yace zewuce sabida yanaso zetafi gida dan shi acikin garin kano yake ayki yakawoshi wudil. yanemi megari daya bashi ameera yatafi da ita dan zamanta agarin zedunga tuna mata danginta tana shiga damuwa.hakuri megari yabashi akan yayi hakuri zuwa Adan kwana biyu sabida karyayi gaggawar bashi ita daga baya danginsu nagurin iyaye suzo nemansu dan haka yayi hakuri aga abinda hali zeyi. Va ason ran doctor yatafi yabartaba wacce harzuwa lokacin daze wuce kuka takeyi ita ummanta dakyar ya rarrasheta bayan yamata alkawarin zekaita gurinta, naira dubu goma yakirgo yaba megari akan asiyamata kayan sawa .yanacikin maganar ne yatuna da kayansu nabayangari dan haka motarshi yanufa yaje yadebo kayan Wanda bawanda yatabasu sabida bawasu kayan kirkibane. Megari yaba kayan sannan yabukaci da à adanasu kodan gaba. Sallama yama megari yawuce, bayan tafiyarsa megari yasa akashiga da kayan cikin gidan shima shiga yayi rike da hannun ameera yana shiga matanshi sukayo kanshi kowacce burinta yabata ita sabida me gari baya haihuwa dan haka dukansu basu da y'aya ganin inyace gawacce yaba abin ze zama da rigima shiyasa yace dukansu yaba kowa nada iko akanta ameera kenan baiwar Allah .

jamaa ina labarin ilham ne ?

love you all 😘maman yusuf

[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_writting by Zahra Muhammad mahmud_

*Page 25*

Iham tunda ameera tatafi tabarta take tsaye abakin titin bata matsaba tananan har kowa yawatse bata da alamar motsawa.
Gungun wasu almajirai sukazo wucewa sundawo daga yawon bara suna zuwa daidai da ita kawai seta bisu dan ita atunaninta gidansu zasuje tafiya sukayi metsayi
Sannan suka iso wani dan kauye dayake suna da yawa shiyasa basu lura da itaba tsayawa sukayi abakin titi da alama tafiyar dasukayi sunyitane dan samun ragin kudin mota baa kauyan zasu tsayaba wata motace kirar akori kura tazo wucewa dasauri almajiran suka fara tsaida motar
Motar harta giftasu tadawo da baya ina zuwa direban motar yatambaya. Kano suka hada baki gurin bashi ansa gyara parking yayi sannan yafito yabude musu kofar bayan motan dasauri almajiran suka fara darewa kan motar har sungama hawa ilham natsaye sabida ita bazata iya hawa da kantaba direbanne yawaigo yaganta atsaye atunaninshi tafiyarsu daya danhaka batare da Bata lokaciba yadauketa yasa acikinsu bayan yarufe kofarne yace dasu kudin motarsu naira hamsin hamsin basu musaba sukace Allah yakaimu lafiya zagayawa yayi yatada motar sukadau hanya
Tafiya sukayi medan tsayi sannan suka iso kano parking yayi agefen titi sannan yasakko yabudemusu kofa kowa inze sauka seya mika kudinsa harsuka gama sauka yarage saura ilham sauko da ita direban yayi sannan yamika mata hannu alamar takawo nata kudin kallonshi kawai take da lumsassun idanuwanta Wanda KO baa fadaba yunwa takeji
Ganin Bata da niyar magana yasa yakyaleta yashige motarsa yawuce yabarta agurin sukuwa dama almajiran sundade da wucewa.
Tananan tsaye har akafara Kiran sallar magaruba bata matsa a inda takeba amma zuwa lokacin tafara kuka sabida rabonta da abinci tun karin safe kukantane yajanyo hankalin wata mata meseda kunu da kosai kanta .kobaa fadamataba tasan yunwa ce tasa yarinyar kuka dan haka kunu tazubamata kunun da kosai taje gurinta tabata kallon ilham datayine yasa zuciyarta tashi sabida ilham inbanda warin rana da karnin miyau ba abinda takeyi ga wani zarni daya cika gurin asaka makon fitsarin datayi ajikinta
Seda me kunun tayi dana sanin bata kunun a robarta. Itako ilham nagani kunu bata tsaya tunanin komai takafa robar abakinta batadamu da zafin kununba tashanye tas sannan taci kosan ay tana gama sha takwanta agurin sebacci da gudu me kunun tabar gurinta domin lamarin ilham yafara Bata tsoro Yarinya dakyau kamar aljana sannan gata nakasasshiya ay bata bata lokaciba tahada kayanta tabar gurin

Love you all 😘maman yusuf

[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_Writting by Zahra Muhammad mahmud_

*Page 26*

Tanan kwance agurin kowa yazo wucewa sede yamata fatan samun lafiya domin azatonsu mahaukaciyace
Tana gurin har zuwa karfe daya nadare se alokacin tafarka koda tafarka Bata tsorataba cigaba kawai tayi da tafiya duba da yadda garin kano dan musa me kwankwasiyya yawadatata da haske dan haka ilham tafiya kawai takeyi batunanin komai ba mutane sede jefi jefin motoci masu wucewa
Duk motar datazo wucewa nacikin motar kallon mahaukaciya sukemata bare yanzu data cire hijab dinta acan inda tasha kunu gashin kanta awaje yake gashi da yawa har gadon bayanta .tayi tafiya meyawa har tazo dai dai gadar yankura anan tayada zango ajikin gadar daga gefen titi baccine yasake dauketa agurin ba ita tafarkaba se da garin Allah yawaye shima tafarkane asakamakon hayaniyar mutanen dataji akanta bude ido tayi ahankali sannan tamike zaune tana kallon mutanen dakowa yatoshe hancinsa asakamakon warin kashin datakeyi domin kuwa kashi tayi akwance
Korarta mutanen suka farayi haka tamike tana kuka ko tausayinta basujiba wata bayarabiya harda marinta tana harkadata. Jinsaukar marin akumatuntane yasata sakin kuka me tsanani gami da kwasa da gudu ay tana fara gudun mutanen suka fara dariya sabida gudun abin dariyane koni naso nadara kawai dannasan wacece ilhamne shine yahanani gudune irin naguragu tana fara gudun tafadi kanta yaji ciwo amma bata damuba burinta kawai tagudumma matar domin tunda tazo duniya baataba marintaba se ranar
Seda taci gudunta me isarta Wanda duk inda tawuce da gudun dariya jamaa keyi dan gudun abin dariya ne sannan ta tsaya tana haki yunwa tafaraji danhaka tafara neman abinci tahanya bin guriguri tana kuka kofar wani restaurant ta tsaya tana kuka to aciki akwai costomers suna brakefast acikinsu akwai Wanda yafara amai sabida ganin ilham dayawa daga cikikuma fita sukayi suka bar abincin ganin haka yasa matar me gurin tasowa takama ilham da duka bata barta seda tamata shegen duka sannan takoma ciki tadauko ruwan wankewanke ta kwaramata zuwa lokacin inka kalli ilham bazakace itabace sabida gaba daya fuskarta ta kumbura dan duka
matarce tafara balai dan ubanki gobe ma kikara zuwa kofar shagona ki korar min costomers mayya kawai wuce kibani guri. ilham nakwance agurin sabida jikinta yayi tsami ga yajin ruwan data watsamata yashigarmata ido da duk inda taji ciwo kuka kawai takeyi ganun ilham Bata da niyar tashi yasa matar janta akasa seda tayi nisa da ita sannan ta wurgar da ita cikin wata kwata Allah sarki ilham marainiyar Allah.

love you all 😘maman yusuf

[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_writting by Zahra Muhammad mahmud_

*Page 27*

*Bayan shekara biyu*

Zuwa wannan lokacin duk Wanda yasan ilham baze ganetaba sabida gabada takoma tamkar mahaukaciya sabida datti gashin kantama yadankare akanta kamar bata dashi
Rayuwace takeyi me cike da tausawa sabida ko abincin dazata ci yanzu yakoma sede tabi bola tasamu hakanne yasa duk Wanda yaganta yaga mahaukaciya
Har yanzu atiti take kwana ko kangon da baa gama ginashiba.
Yanzu shekarunta sha uku kuma awannan lokacinne Allah yakawomata jinin al'ada(wayyo Allahna)gaba daya jinin yagama bata mata jiki sabida jinin irin me rushing dinnanne ga azababben ciwon mara Wanda inya murda mata sede taita birgima har Allah yayayemata kuma koda jamaa sunga tana birgimar babu me bi takanta dan azatonsu duk acikin haukarne
Shiyasa yanzu warin datakeyi namusammanne ko ina tabi korarta akeyi babu me Jin kanta kuma lalurarta se abinda yakaru basauki sena Allah.

***********
Zuwa yanzu ameera na js2 sabida megari yamaida ita makaranta kuma har yanzu bata manta da yar uwarta ilhamba shiyasa kullum megari cikin bada cigiyarta yake sabida megari idan akwai abinda yatsana shine ganin ameera cikin damuwa Sam baya kaunar bacin ranta dan inkaga ameera yanzu bazaka taba cewa ba yarsa bace kuma suma matansa kowacce cikin kyautatamata suke ba banbanci. Rayuwar ameera de se sonbarka matsalarta daya ce rashin yaruwarta ga doctor kullum cikin yimata ayke yake duk week-end kuma yana hanya dan yanzu sunsaba dashi kamar dan uwanta haka tadaukeshi shima kuma zallar tausayintane aranshi dakuma wani abu Wanda yabarma ranshi sezuwa lokacin dazata mallaki hankalin kanta.

love you all 😘maman yusuf

[3/13, 07:08] Ussaina: *ALLAH GATAN BAWA*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

_writting by Zahra Muhammad mahmud_

*page 28*

*Anwar umar mutallib*
Chapter 3 · 0% Book details