← Book details Al'farma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 39

Sashe 4

Al'farma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_____________________________
Bayan wasu watanni
"""zuwayanzu kararu nasa agabana tukuru, danmunkusa ayayemu, shinkafar gonar baba tayikyau matuka da akacirota bakaramin alheri baba yasamuba,harzakka saida yafidda aciki, da akasaida shinkafar kudi maiyawa akasamu, ranar baba yayi alheri wayan unguwarmu,nida mama kuwa munsan baba nacikin wadata...
Ranarda yarage saura sati daya ayayemu,baba yashigo gida rikeda babbar laida ahanu,kantaburma damuke zaune da mama ya isa yazauna.mama tayimasa sannu dashigowa nimahaka, yaturomin wanna laidar gabana.gashi mamana kayankine aciki gara mufara shiri tun yanzu,dabarin jiki nabude laidar nashiga ciro kayakin dakeciki. Zannuwace turmi shida sai hijjab kala uku da takalma guda biyu harda kayan kwalliya masuyawa,bakina kasa rufuwa yy dan murna mama kigani kigakayana da baba yasayamin naturawa mama kayan.itama murnar tayi sosai dasanya albarka"
Baba yaciro kudi yamikawa mama gashi gobe idan allah yakaimu saiki bada dinkin kayan dan asamu ayi kar lokaci yakure,mama tasa hannu biyu takarba,baba yagerazama tareda gyaran murya yace.kunga ikon ubangijiko shikeyi dabayinsa yadda yaso yanzu kuduba kuga yanda yawadatamu da abinda zamu gudanar darayuwa cikin ikonsa.allah kena maji tausayin bawansa,mama tace hakane ubangiji mungode maka..baba yacigaba. dazunna naje mukayi cinikin wani shago maidauke da kayakin abinci nabiya kudin zanfara sana'ar saida kayan abinci.ina bukatar adda'arku kamar yanda kuka saba,sanna ke mamana zaki koma makarantarki bayan kingama hidimar gama islamiyar ki,mikewa nayi narika salle inafadin allah mungudemaka.su mama saidariya suke dafadin yarinta dangin hauka..
Washe gari cikin ikon allah baba yafara zuwa sabon shagonsa.aranarma munga nasara dankuwa rabin kayan abincin masaya suka saye.saizuwa yy yakuma saro wasu...
Fitowa nayi cikin shirin tafiya islamiya, ina isa natadda dalibai kaf anhadu. Malam nuhu yashigo aji yafara yimana jawabi. Ayau za abaku hutu sai ranar asabar shine zaikasance ranar daza a yayeku.amma kafinna akwai wata sako datashigo mana yau dasafiyarnna.cibiyar makarantarna datake cikin birnin tarayya abuja.AL'MU'ASSASA"ISLAM"ta aiko dasakon cewa kafin ayi yaye dole sai anyi musabaqa, tabukaci dalibai guda biyu daga cikin wadanda za'a yayesu,domin gudanar da musabaqa nakasa baki daya acin birnin na abuja wanda za'a gudanar ranar'asabar mezuwanna.sanna suna bada hakuri akan rashin aiko da sanarwan dawuri.yanakaina yasauke numfashi.kunji sakonda ya isomuko,tsit yan ajin akayi kowa sai raba ido yake da sakar zuci.tirkashi wanna wani irin musabaqa ce haka bazato basammani kuma acikin kwanaki biyar dayarage ayi yariskemu.kuma bana iya jahaba nakasa baki daya,maganar malam nuhu yakasemun zancen xucin danake, khadeeja umar"RUMAINA adamu,kubiyoni yana fadar haka yajuya yy waje.
Kulululu cikina yabada mukahada ido da khadeeja itama daga kurinta hakan takasance, muka mike jiki asabuli mukafita.can muka hangoshi gindin bishiya shida sauran malamai muka karasa inda suke muka sunkuya kasa gefe dasu, RUMAINA khadeeja malam nuhu yakira sunanmu,hada baki mukayi gurin cewa na'am, kune zaku kasance mutum biyunda akabukata dan gudanar da musabaqa takasa dan haka kudage daga yau harzuwa ranar asabar idan allah yakaimu kuzage wajen yin bita,kunajiko? Ai babakin amsa saidaikai kawai mukagyada,suma sauran malaman sukayi kalar nasu jawabin,wai kada mubasu kunya,malam nuhu yamikamin wata farar dakarda yabawa khadeeja ma,yace kukaiwa iyayenku wanna takardar.daga karshedai sukace mutafi gida,
Duk jikina yagama mutuwa haka nadauki hanyargida jiki bakwari,karar mashin danaji abayana yasani jangefe dan tawuce.koda najuya sainaga ashe malam nuhu ne.yafaka akusa dani.yadubeni cikin tausashen murya dafadin RUMAINA nasanki da hazaka kikara akan nada kinga wanna karon musabaqa ce nakasa bakidaya inaso kibada hankalinki sosai kada kiyi wasa.to malam insha allah zan maida hankali.nafadi hakannekawai bawaidan nasamu kwarin guiwa damaganar dayafadaminba.to allah yataimaka jeki gida.nakama hanya..................

Comments and Share

MAMYN TWINS CE
12/30/19, 14:53 - 拼ar Gatan 茦ainuwa: 馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲
ALFARMA
馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM

by鉁嶐煆�
Rasheeda S' Director

ALLAH KA ALBARKACI ZURI ARMU"BAKI DAYA,
KABAWA BABY KHAYRAT LFY馃げ馃徎

Page 5

Wanna page in nakine anty fati na grp in 馃啋NOVEL MEKEUP AND KITCHIN kiji dadinki kiyi lasting馃じ鈥嶁檧馃槝

""""Hakana isagida bawalwala tattare dani.naisa nazauna kusa da mama,tadubeni yau kosallamarma babu ita hakafa kk shigo babu sallama,nayifa mama bakiji bane kawai.yanayin danayi maganar yasa mama dada dubana cikeda kulawa dan fahimtar yanayina,abinka da uwa kallo daya tafahimci inacikin damuwa.RUMAINA meke damunki?kamar jira nake tayi tabbayar nayi saurin ruko hannuta mama wai musabaqa zamuyi,to shine zaki damuhaka saikace yau kksabayin musabaqar.mama wanna musabaqar ba irin wanda nasaba yintabace.wanna nakasace bakidaya kuma a abuja zamuyi mama inajin soro gawanna takardar malam yace mukaigida.namikamata takarba tana dubawa.
Muna cikin haka baba yashigo,nan mama keshaidamasa,shima dayaji zancen saida yajinjina amma dan yakarfafamin guiwa saiya. to mamana zamu tayaki addu'a saiki maida hankali sosai kamar yadda nasanki.maza tashi kijekici abinci kisamu guri kinutsu sosai dan kisami damar yinbita"to nace namike nashige daki .ranar ko waigen abincinci banyiba saida mama tazaunar dani agabanta kamar kullom kafin naci,
Inayin sallar isha nafara bita,inacikin karatun sainaji harshena nahardewa abin mmk saina tike saikawai nafashe dakuka, dasauri mama tashigo dakin tataddani nasaka KUR'AN gaba saikuka nake,rufe KUR'AN in tayi takamo kafadata namike saye tajanyo hannuna zuwa bakin katifata,kwanta kiyi barci idan kktashizakiji kin'iya,kaikawai nagyada mata ,saida taga nakwanta kafin tafita.aiko banjima dakwanciyaba barci yadaukeni, karfe shabiyu daidai nafarka,naje nadauro alaula nazo nayi sallah raka'a biyu,sanna nabude AL'KUR'A'NI nafara karatu abin mmk saigashi inda dazu nakasa yanzu na iya,banbar karatunba harsaida akakira sallar asuba"shima ina idarwa nacigaba....hakakullon nakeyi abinda ketadani salla saikuma cin abinci,saida wani lokaci mama tashigo tarufe KUR'AN din tace naje nakwanta kuma da ikon allah idan nayi barcin natashi sai inji kamar ankaramin iyawarce...
Yau juma'a'inazaune bayan na idar dasallar isha mama tashigo dalaida ta aje gefena tafita.najanyo laidar sainaga kayan da baba yasayomince har an dinka,naji dadi sosai.naturasu gefe nacigaba dabita kamar kullum. Yau karfe daya mama tashigo tatadani tace nakwanta haka tadauki KUR'AN din tafita dashi adaren mama da baba ko rinsawa basuyiba...washe gare da asuba mama tatadani tace naje nayi wanka koda nashiga bandaki natadda takaimun ruwan wankan maidumi,nawanke jikina saf nafito..bayan nayi sallah nasaka daya daga cikin sabin kayana masha allah bakaramin kyau kayan yaminba.ina gamawa mama nashigowa dauke dakayan karyawa.itada kanta tahadamin tea kasancewar yanzu alhmdllh tea and bred mukekaryawa dashi wani sa inma harda kwai, tace nayi maza nakarya kar lokaci yakure..
bayannagama baba yy kirana waje.yashiga yimin nasiha maishiga jiki.daga bisani mama tadaura nata nidai saisharar kwalla nake..baba yadubeni taso muje narakaki.namike nadau jakar danasa kayana kala biyu muka fita mama tanayimin fatan alkairi...harcikin makaantar mukashiga da baba,dalibai da malamai kaf sun hallara.can nahango malam nuhu sai duba agogon dake daure ahannusa yake kamar ance yajuya yana ganinmu yanufomu, yarissina yagaida baba baba ya amsa dafadin kace ita akejirama tundazu naga gayan uwanta duk sun halarci gurin,dan murmushi yy baba kasan yaune za afara musabaqar na kuma sunce bayan sallar azahar za afara gashikuma dagana zuwa abuja da dannisa shiyasa zamutafi dawuri,baba yace gaskiya kam gara ajedawurin dangudun makara.sai alokacin nagaidashi.baba yace to allah yasare yakuma bada sa'a.malam nuhu ya amsa da ameen.baba yajuya yafita amakarantar najuya zantafi cikin dalibai karaf mukahada ido da malam nuhu nayi saurin yin kasa dakaina nagotashi nashige cikin dalibai...
Motocine guda uku daya namalamai biyu kuma nadalibai sai'alokacin nasan asheduka za'atafi bamu yan musabaqa kadaiba harda daliban daza ayaye ,acan za'agudanar da yayen, aka umurcemu damushiga mota mukashiga.
Batareda batalokaciba.motacin sukabar harabar makarantar.muka lula titi.....
12:15 pm"
Mukashigo babban birnin taraiya abuja" direct masaukinda akatanadar mana motocin sukashige ,suna parking mukafirfito yan agajine hadeda sojoji zagaye dagun.munafitowa cikin sauri sukazo inda muke.hanjin cikinane yakada sakamakon ganin sojojinna danayi nandana jikina yasoma bari,tun ina yarinya nakemugun jin soron soja kotafiya zamuyi da mama idan mukazo (road block) (checking point) rufe idona nake gam harsaimunwuce kafin nabude.nayi baya dasauri nashige sakiyar dalibai narike hijjab inwata nayi kasa dakaina harsaida mukashiga cikin masaukinmu"suma sojojin musulunce wato yan'agaji,dasu sojojin gomnatin sukajuya danganin munshiga.
Masaukine maikyan gaske muzallar dalibaine aciki malamanmu dai awaje mukabarsu.mukazazzauna asaman kujerundake cikin katon falon,yan agaji sukashigo dauke da manyan kuloli nan sukafara zubana abinci sukarika mikawa kowa acikinmu sanna sunagamawa sukafita. Mukasunkuya cin abincin.da abinshan dasuka ajemana agabanmu.
Munagama ci anakiran salla wani dan agaji dake saye abakin kofa tashigo.gabayican kushiga kuyi alaula yace damu,to mukace.mukarika shiga munayin alaulan.mukazo muka gabatar da sallah,
Munazaune wasu yan agaji su uku sukashigo daya nagaba biyunabiye dashi koda ya iso indamuke yaja yasaya biyunna suka saramasa"tareda kamewa.sannuku yacedamu"mukahada baki wajen gaidashi.yy murmushi dafadin kutaso muje,duka mukamike mukabi bayansa,muna fita wadanna sojojin suka yisaurin zuwa inda muke sunrirrike bindiga kamar sunafilin daga.yandanayi dazu hakama nayi yanzu harmuka isajikin mota
Motocin kungiyace guda biyu mukashige ciki motocin sukaja...
Tafiya mukayi maidannisa..kafinmuka isa babban filin taro dake cikin abuja"tundaga bakin get in mukafara ganin mutane masu yawan gaske "direbar yasamu gefe yafaka dasauri yan agajinda ke sassaye abakin get din suka zo jikin motar tareda bude murafen motocin mukarika fitowa.suka budemana get mukashige ciki, ya'ilahi'yalillahi"ido naware bisakan mutanen dake cikin wanna filin taron,jama a kamar kasa.haka akarika kusawa damu cikin gurin har muka isa wani guri wanda akasa iyaka da jama ar dake gurin daya sallaken kujerune ajere dawasu mata wadanda suka sa kaya iri daya gawani tambari agefen hijjab insu wanda akarubuta da arabiq ALMU'ASSASA TARBIYATUL'ISLAM" hakan yanunamin suma dalibaine,takowace kusurwa agun da dalibai daban daban na jahohi daban daban,kuma kowacce da tanbarin makarantarsu, bangare daban aka bamu muka zazzauna...

Karfe 2 daidai..
Aka bude bilin da addu'a.megabatarwan yafara jawabi kamar haka.alhmdllh cikin ikon ubangiji yanzu za afara gudanar da gasar ALKUR'ANI maigirma,damm kirjina yabuga..irinwanna guri taya zan iya koda mosimaikarfi...mai gabatarwan yacigaba.
Daliba nafarko itace hafsat salihu abdullahi daga jahar kaduna state.............

Comments and Share

MAMYN TWINS CE
12/30/19, 14:53 - 拼ar Gatan 茦ainuwa: 馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲
ALFARMA
馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM

by鉁嶐煆�
Rasheeda S' Director

Page 6
Chapter 4 · 0% Book details