← Book details Al'farma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 39

Sashe 34

Al'farma Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

""""""""""Ahankali yasakeni yadago hannusa yana kallon agogo saiyayi saurin nufar kofa..komawa nayi nazauna bakin gado yayinda nakejin wani irin yanayi yana ziyartar ilahirin jikina" haryakai jikin kofar saiyakuma juyowa yakalleni asannu yakuma dawowa cikin dakin yana isowa gareni "saiya sunkuya yamannamin kiss agoshi saiyakuma juyawa dasauri yafita"
Nazube dabaya najanyo pillow narungumesa akirji tareda lumshe idanuna"haka narika juyi asaman gadon har akakira sallan azahar natashi naje nagabatar,daga bisani kuma saina nafito parlour natadda har alokacin dukansu suna zaune Goggo Larai da Rukayya ma sunfito"na isa nazauna"Goggo Larai tayi saurin cewa barka dafitowa meza akawomiki?tayi tanbayar tana kallona kai nagirgiza nace babukomai ai yanzu naci abinci banjima saidai zuwa anjima.tace to"
Najinjina kai wato tunranarda nadawo gidanna naga sauyi Kala kala dagagun Rukayya da Goggo Larai idan zasuyimin magana cikin sakka da girmamawa sukeyimin ita"Rukayya har sotake tarika kukkusamin nicedai banbata kofaba dan komagana nayi saitasa bakiciki akasin da dako kallon kirki ban ishetaba"um ALLAH mai iko nafada araina"Ummee tayi sallama tashigo duka muka amsamata ta iso cikin parlour tazauna kusada Hajja Umma tayitamata tsiya Mommy nakare yar tsohuwarta..haka makatahiri har lokacin sallar la'asar tayi sanna kowa yatafi dan bautatawa mahaliccinsa"nida Ummee bedroom dina mukashiga bayan mungabatar da sallan saimuka tafi part dinsu adakin Aunty Asma'u mukayada zangonmu"inda mukatadda wasu mata biyu tanatayimusu bayani ga tarin magunguna jirgib agabansu suko saizaba suke duk kalan dasukadauka saitayimusu bayanin amfaninsa dakuma yanda akeyi ayi amfani dashi"sosai sukajidi kayan suka zubemata kudadenta sukayimata sallama sukatafi...nan tajuyo gareni tace dama inanimanki saigashi kinkawo kanki"murmushi nayi nace to tasamu kena itama murmushin tayi tace babban samuwama kuwa"saukonan tanunamin kasa kusa da ita nasauko nazauna inda tanunamin din"tace to inazuwa tamike tanufi kitchen can saigata dauke da madara da cup tazauna inda tatashi"nace oh Aunty Asma'u niyaushe zansha tea da yammacinna "tace ai wanna yafi tea amfani ajikinki" dasauri Ummee tasauko tanafadin au Aunty Asma'u ita kadai zakibata bandani"murmushi tayi tace kemazakisha idan lokacinki yy yanzu lokacinta ne ita kadai zatasha"tarika zuzzuba magungunar sunkai kala goma wanda tahada acikin cup din tazuba madarar ruwa harsaida taga yatsinkar da maganin tamosashi sosai sanna tamikomin"ido nawaro waje nace wanna abunfa Aunty Asma'u waini zansha?tace kwaraikuwa kishanye duka"naceto baridai nasha nabaiwa Ummee dannidai bazan iya shanyewa dukaba.tace a'a wanna nakine banda ita kedai rufe idonki kishanye"nakarbi cup din nadibo maganin acokali nakai bakina nayatsina fuska dan jin kalarsa"tace shamana mikomin cokalin kisha dabakin cup din"namikamata sanna nakafa kaina nashanye kamar zanyi amai"tace yauwa kokefa takarbi cup din "nace ALLAH wanna abun bashida dadi" tace Hmm abakiba amma amfaninsa acikin jikinki yazarce zuma,nidai ido nazuba mata "Ummee ko sai zuba take tanafadin Aunty Asma'u nida tunyanzu kk fara tsumaninna kafin ALLAH yakawo mijin aurenna kinga komai zaitafi daidai,baki narike nace ALLAH ke Ummee bakida kunya ashe abunda naseeba tafada ranna gaskiyace ashe watakila ma hardake acikin yanmata masu kaikansu gun masu gyaran amare tunkan aurensu. " dariya Aunty Asma'u tayi tace kidai bari lokacin din yy kamar saura 2 manth sai atsumakin" kuma ai balaifi bane dan yanmata sukaikansu gyaran kansu kan aurensu tunda akan aure zasuyi hakan to ai basu karkace hanyaba"wadanda suke zuwa dan suwatsar da kansu atiti sune abun kyama"so kidaina yimusu kallon abunda suke rashin dacewace kiduba zamaninmu nayanzu har ayanzu wasu iyayen basudamu da idan zasu aurar da yayansu su gyarasu kosukaisu a gyarasu dansamun kwanciyar hankali da nutsuwa azamantakewar aurensu.ninan dakike gani saunawa yanmata sukezuwa danna gyarasu lokacin aurensu"kinsan idan gyara yahadu da budurci tofa abun ba a magana"
Uhm kawai nace inajinjina lamarin......
Haka mukayita hira saidaf magrib Ummee tarakoni nakoma part dinmu......
************
Tundaga ranar Kullum sai Aunty Asma'u ta hadamin kalolin magunguna wani sa inama sainaki zuwa part dinsu hakuma zatabiyoni dakanta saitatabbatar nasha kafin takoma.wani sa in harsai takirawo Mommy kafin nakeyarda nasha"ranar takeyimin fadar cewa nadaina kinshan dan Mommy bazataji dadinba nan take sanarmin dacewar ita Mommy dince tasata tarika tsumanin"nidai nasha mamakin jin Mommy ce tasa arika bani maganin.....
Yau sati daya kenan datafiyar ya***I'B
Kwance nake asaman bed saijuyi nake duk damuwa yagama cikani abun mamaki waikuma tunaninsa itace kehanani sukuni" lokacinda zaitafi harmurna nake yy yatafi saigashi ayan kwanakin da yayinna saigani nake kamar yayi watannine"
Nalumshe ido tareda Jan numfashi nadafe kaina oh ALLAH wai mekeshirin faruwa daninekam"namike zaune ahankali nazuro kafata kasa nashiga bathroom nadauro alaula nafito nagabatar da sallar isha..ranar dakyar nayi yaki dazuciyata nasamu barci yadaukeni"abu kamar wasa sai dada girma yake saiyanzu nagaskata zuciyata lallai nayarda kewarsace kedamuna inason ganinsa inason jin muryarsa"uwa uba kamshinsa,
Narasa yanda zansa rayuwata"bantaba tunanin akwai wani namijin dazanji wani abu akansa bayan Ana's ba "saigashi abunda nakeji akan Ya***I'B yazarce tunanina inajinsa acikin jinina" saidai haryanzu naki yarda da sonsane ke dawainiya dani"nafiyarda kewar tasace kawai ALLAH ya aikomin amatsayinsa na mijina.
Haka narika gudanar darayuwar kunci......

(Thursday 16 January 2020 )

Haka kuma yayidaidai dawatan Ya***I'B 1 "kallo daya zakayimin kagane tsantsar damuwa atattare dani dukda kokarinda nake wajen boye damuwar.zuwa lokacin nagama yarda sonsace ke wahalar dani,wani sa I har sainarikajin haushin kaina" idan nazauna nayi tunani sainaga balaifina bane dan Ya***I'B yacika danamiji irin cikakkennafa sosai,nayi iya tunanina Dan samawa kaina mafita inabukatar jin muryarsa nakuma rasa ta inda zanfara"ahankali nafito dagacikin bedroom dina babu kowa a parlour saina nufi dakin Hajja Umma "zaune na isketa tana Jan jarbi na isa nazauna gefe da ita taredayima barka da dare ta amsa tanafidin nadauka kunyi bacci ai dannaga Ku kamar kasa kuke" nayi murmushi dafadin kai Hajja Umma yanzufa karfe 9:00pm idonmu biyu"najanyo wayarta inafadin barima naduba nagani ko 9 dinma tayi"inadauka sainashiga contacts narikabin jerin sunayen numbers naduba yakai sau uku amma kasancewar bansan number dinsaba sainaketa kokonto akan wata number maidauke dasunan IBRAHIMA saikawai nadanna kira"yana ringin 1 2 sainayi saurin kashewa namaida wayan na ajiye inafadin ai 9 dinma hartawuce"nantake saiga shi anbiyo kiran jinayi gaban kirjina yabuga"nadago wayar nace Hajja Umma gashi anakiran wayarki" tace um yanzuhaka wanna fitinanniyar yar Ali ce rabu da ita kawai"nace barinadauka sainace da ita kina lazumi"inakaiwanan nayi picking na call din nakara wayar akunnena ahankali nace hello.............

Comments and Share

MAMYN TWINS CE
[9:59am, 11/03/2020] Rashida: 🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

ALFARMA

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

🅿79👉🏻80
Chapter 34 · 0% Book details