← Book details Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kuwa tafiya dama yina rike da maganar a ransa ya yi maza ya tura ma Yumnah Number labeebah ,don ko banza yanaso su zauna lafiya ai,kuma yana jin dadin kumar da labeebah take gwada ma Yumnah ,kuma ko yanzu ya gane labeebah sonda take masa don Allah ne soyayyar sa shi yasa ya tashi duk abu da yake so a fadin duniyar nan ciki har da Yumnah da ya lura tana azaban sonta .

“Yayanki ta matsa tana so ku gaisa ,ga numberta ki kirata ku gaisa”

Darararmmm ƙirjin Yumnah ya buga tunda ta karanta sakonsa ranta ya dugunzuma a bayyana tahau surutai

“Ni na kasa gane irin wannan Al'amarin ,dama can yasan Yana son matarsa yazo yace zai aureni ? Ynz baida wani magana sai ta matarsa ? Ni gaskiya na gaji wallahi bazan kirata ba,tunda nike a rayuwata ban taba jin an kulla zumunci kyakyawa tsakanin kishiya da kishiya ba ,don haka tsoron Aseem kar yace bana son matarsa bazan kirari in Burma ma cikina wuka ba”

Da wannan masifar yasa tayi kememe,ita bata kira wayar ba kuma ita bata bashi amsa ba.
Aseem shiru shiru yaga Yumnah ta bashi amsa ba labari don haka ya gaza hakuri ya kirata a waya ,ya kira yafi sau biyar har saida Ummah ta lura ,ta kuwa hau ta da fada
“Wannan ai wulakanci ne ,ke har kinyi rikar da mutane zasu ringa kiran ki a waya kina ignoring ? Me kwada ta ɗaras wa gaya? Tun kafin ki auri mai kudin kin fara koyon halayyan masu kudin na dagawa da wulakanta mutane? Ke wacece ke?”

“Ummah fa Aseem ne”
“Au Aseem 😳? Shine kike kin daga masa waya ? Aah ba lafiya ,kin dauka ko sai na Wullo maki muburgin hannuna ”

Kumburo Baki tayi cikin sigar shagwaba sannan ta kanga wayar a kunne
Ba tare da tace komai ba.
Jin shiru batayi magana ba yasa shi soma magana da “Da girman kujeran ki,kaina bisa wuya gimbiyaa huce don Allah Aseem na neman afuwa tun kafin yaji laifinsa”
“Ni bakayi mun komai ba ai”
“To menene kike kin daga mun waya ? Kuma muryarki yayi kama da na Mai fushi,ba faraar nan ,ba Dan gaishenin nan da aka sabayi duk in na kira waya ,kinsan wannan suna cikin siffofin ki da suka bambanta mun ke da sauran matan zamanin nan,ke ta dabam ce my world” Dan Murmushi tayi mai gauraye da jin kunya

“To ina kwana 😄” ta fada a lalace kamar wawuya ko irin shagwabaɓɓun yaran nan.

A hankali ya maimaita “Ina kwana” yanda tayi

Aikuwa kamar zata fasa kuka ta fara didderke kafa a kasa
”Ni wallahi bazan yarda ba ,nine kake kwaikwayo na🥹”
“Ahnnn sorry auren na bari”
“Tsallan kwaɗo guda goma,kuma Now ,a tashi ayi ina leƙen ka daga nan ” dariya ya kwashe dashi

“Dole inbi umurnin kwamanda”
“Kai kai kai😳 ka maidani namiji?😢ai wallahi bazan yarda ba ”
“Na shiga uku baby rigima ,just to show you ,ke ta musamman ce ,koɗa ki fa nayi”
Noƙe kafada tayi kamar yana kallonta
“Uhm uhm Ni ban yarda ba ,Allah sai kayi guda talatin ” shikenan Bara ma inyi yanzu ”
“Yawwa ina kallonka daga nan kuma ehen 1 naji nishinka ....lalala wallahi ka daina”

Bushewa da dariya yayi“Shikenan Amaryar nan zata sa angonta ya rame ayi biki yayi xuru zuru”..

Sundade suna hira sun dawo normal kamar ba abunda ya faru kafin Aseem Sarkin naci ya sake dawo da maganar kiran waya ,ɗif kuwa tadauke wuta

“Kamar baki ji dadi ba,ko baki son kiranta ne? Ina baki so just tell me wallahi bazan sake maki magana ba kuma ba”

“Uhm uhm kawai dai bani da kati ne a wayar,amma zan kira ai”

”Ok to shikenan ,one😍”
Ji tayi kamar ta jawosa ta shakesa saboda haushi amma dai ta dake kawai .

Sun gama waya tsakani minti biyar sai ga vtu an lodo mata kati na dubu Goma.

“Au saboda dai sai na kirata shine ya turo mun katin ,kuma bazan kira ba” .
Karaf a kunnen umma da tazo giftawa daga kitchen ta gama nuna ma baba Mai girki yanda zata karasa hada abincin gidan.

“Meke faruwa?”
Yumnah bata ɓoye ma mamanta matsalar ta tunda dama ai bata da wata kawa bayan iya ,don haka cikin kuka ta fara labarta mata yanda yake matsa mata da zancen matarsa last last ma yau ya turo mata numberta wai ta kirata itakuma sam bata so.

“baki so ki kirata kiran waya kadai? Anya ? Yumnah anya? Ita da zaki shigo mata gida bata gwada koshinta a kanki ba sai kece zaki gwada bakya sonta? Kenan inma bariki me ta fiki iyawa ,maza daddage ki bari mijinku ya gane matsalar rashin jituwar zata fara ne ta bangaren ki,wallah sai kinsha bakar wahala don koda kunyi aure ko me zatayi mako na cutarwa zaice ke kika tada rikicin dama can baki sonta ita ke like maki ...kinga ai matsala ta afku

“Amma umma kinsan fa namiji minafikine da baya mun taɗin matarsa sai ynzu umma anya bazan fasa auren ba”
Tafhanni ta shigayi tana salati
“Shikenan tayi nasara ,da kissa da kisisina ta kwato mijinta ke da kanki kin gudu ma auren. Yumnah ina wayonki yaje ne?

Da bai mako tadin matarsa,to ai abinda ya kamata kenan wajen nagartaccen miji amma kuma ynz da kuka kusa zama abu guda hakkinsa ne ya hada kanku wanann ba laifinsa bane ba .....don haka Yumnah ina maki nasiha kar ki yarda ki shiga gidansa ki wargaza masa farincikin ahalinsa ,shi ya taimake ki ke kin jefasa halaka”

Hawaye ta fara gogewa

“Shikenan umma dama nasan kinfison Aseem dani ai”
“Eh nafi sonsa saboda shi yana kan daidai....maza kirata a waya in gani...”

Oum Aphnan

ABU UKU
Page R

Labeebah taji dadin waya da Yumnah alamu ya nuna ba er duniya bace ba ,wannan ma bata da wani wayo ,in ta yi ƙoƙari to tabbas ko bayan aure zatayi mata biyayya ba irin matan da zasu nuna lallae sai sun kwace maka miji bane ba .
Tunda ta samu Number Yumnah shikenan duk safiya sai ta tura mata da sakon gaisuwa ,tama fi Aseem din zakewa ,amaryanmu ya shirye shiryen biki...amaryanmu kinji a sabon gidan mu zamu tare ko? Ni wallahi ma tsoro nake ji ,hope kedai jaruma ne ,don kinsan mijinmu ba mazauni bane bashi wanann kasar bashi wancan kasan,don haka ne ma yasa nace Ni bazan dawo gidan shi ba sai da er uwan zama na to ko yanzu rana daya nike so mu koma gidan mu gwanin sha'awa ko ya kika ce?

Gaba daya ta kashe ma Yumnah jiki “Ni fa nima ina da tsoro,don Allah Ni karki jirani gida naki ne kawai ki koma na biyo ki daga baya,ke kin ma isa? Wallahi ina bazai yiwu batare zamu koma😄” haka dai labeebah take jan ta a jiki da barkwanci .dukda har yanzu tana dari dari da ita don tasan kishiya dai ba Abar yarda bace ba .

Ga wani abun mamakin duk abunda sukayi da Yumnah koda Aseem bazai saurare ta ba sai ta bashi labari .bata nuna mata yaji dadi amma a ransa fa yana jin dadi yanda yake tayashi kuka da matarshi .

Babe tace wai tsoro take ji ita bazata iya zama a sabon gida ba saidai in Dani ,Ni nace mata taje abun ta amma na lura matar namu akwai shagwaɓa.”

“Oh sannu Radio iyayen Surutu tun kafin in fada mata a sabon gida zata zauna har kin guntsa kin fesa mata?”

“Allah sarki zumudine ,wallahi haka nan nike jin yarinyar a raina wallahi son ta nake kamar kannena nima bansan dalili ba amma in Nayi maka ba daidai ba kayi hakuri ,ita kanta naga yarinyar ma ta ki sakin jiki dani ,ko yau wani status din habaici tasa a status dinta kawai dai nayi viewing ne na kauda kai don nasan ƙuruciya ce ,ko kuma bata fahimci labeebah bata dauke ta a matsayin kishiya ba face er uwa.”

“Me tasa a status din? Nifa bana son tashin hankali”

“Haba is not something serious ,Ni bacin ma magana ta tada magana ai bazan maka ba,kawai nayi maka magana ne saboda ciwon 'ya mace na 'ya macene ,ta nuna ita fa matsoraciya ce dole Dani takeson komawa gidan kasan kuma kai ba mazauni bane ba ,adabi duba ma yarinyar nan”

Kunna wayarsa yayi ,yayi searching status din Yumnah saiga wani quotation “Bana sonta ,shiyasa nazo aurenki ,saboda kin fita komai ,da ke na fara haduwa dake da tabbas kece uwargidana daga kanki kuma zan rufe ƙofa...No kishiya in my house”

A kasar maganar sai Yumnah ta sa emojin dariya “Don Allah ku tafa ma maza😄”

Kowa dai yaji maganar yasan tana against maganar da maza suke in sunje wajen en matansu ne karo aure,amma duk wacce za ayi wa kishiya tabbas sai ta tsargu.”

“Kina da gaskiya labeebah I'll solve this case ,komawa sabon gida kuma zan duba in gani kila inje dake kila ba inje dake ba ,amma dai abinda nike so ki sani shine har yanzu fa a jingine kike a wajena ,ko akwai wani alakar auratayya dake shiga tsakanin mu?”

Girgiza masa kai tayi ƙwallon ya cika mata ƙwarmin ido
”to tashi ki bani waje ,Ni bansan ko karancin ilimin addininki ba ,ya sa kinsan idan fasika taje tayi zina kafin ta koma ma mijinta akwai bukatar tayi istibra'i ...”

Waigowa tayi ta kafesa da jajayen idanuwarta ,ta rasa me zatayi ya yafe mata ita kam

“Dallah Ni bar kallona kamar wata mayya ”

Sun sun sun ta wuce
****
Aseem bai ce mata komai ba har yamma saida tayi yaje har gida ya samu Yumnah ,anan ne yake mata korafin abinda labeebah ta gani a status dinta .

Da ta rasa me zatace kawai sai ta bushe da dariya,lallae ma matar nan ashe tana da kishi take wani ɓoɓɓoyewa?

Shiru tayi masa tana duba status dinta ta na sake karantawa .

“Ina so ki goge shi” a gatsale tace masa to kawai

Amma dai bata riga ta goge ba suka cigaba da hiransu har ya shiga suka gaisa da umma kana ya wuce .
Chapter 18 · 0% Book details