ABOUT THIS BOOK
Description
Dare ne mai ɗauke da baƙar hadari ko'ina yayi shiru,sai wucewar ababen hawa jifa² .
Ilahirin mutanen kirki sun soma ɗauke ƙafa zuwa muhallinsu don saukar da hakarƙarinsu akan makwancinsu don huce gajiyar ranar,da tsammatan gocewar ruwan sama mai Albarka.
Sosai Iskar ruwa ke busowa gamida Guguwa gadai dukkan Alamu ana ruwa a kusa da wannan waje kuma daf ruwan yake da gangarowa wajen.
Wawwaigawa nake a nutse don neman wajen da zan fakaice kafin wanann ruwan ya tsuge a kaina ,don bansan lokacin tsayawarsa ba ,bayan shafe tsawon sa'a guda ina jiran 'yan adaidaita ,amma kwatakwal kamar an sharesu.
Can gefen hanya wata Dalleliyar mota na gani ƙirar marcendi GLK baƙa wuluk da ita , a kunne take , danjojinta sun haske ko'ina ,mamaki yasa Hankalina karkata zuwa wajen.
Aseem Matashi ɗan kimanin shekaru 37 ne zaune a mazaunin driver ya goya hannuwansa akan kambin motarsa ,yana kallon Budurwar da ta ke tsaye a gaban murfin motarsa ,tayiwa murfin motar rumfa.
Dukda dare ne amma fuskarta kamar madubi saboda makeup da ya dauka zauu! Fuska fa yasha Foundation dasu bronzer leɓe sai sheƙin jan Jambaki yake ido na farfari da gashin idon kanti.
Fuskarsa ba walwala irin na wulakantattun matasan masu kudi din nan ,ya dubeta
“Kikace daga nan ina zaki?” “Nop,bani da zaɓi sai inda kayi dani ,Ready to spend the whole night caring of this gorgeous buddy”
Ɗan caɓe baki yayi kadan wanda hakan ya dade da zame masa jiki ,ba wai yana yinsa don wulakanci bane sababben sa ne.
“Jeki ɗauko jakar ki to”
Wani juyi tayi mai jan hankali ta ɗan kada masa boobs ɗin ta kaɗan cikin sigar jan hankali kana tace “Thank You mr man”
Ta juya tana karkaɗa masa baya tana wani irin cat walking a tsakanin duhun daren da hasken fitilu ,har ta shige rumfar da ta bar ƙawayenta suna jiranta.
A galabaice ya koma yaraf ya kwantar da jikinsa akan kujerar motan damuwa kar ki tona ransa ,so yake kawai ya fashe da ihu ko zai samu sauƙin zugin ransa
Tasneem Da gudu ta shanyo shataletalen hanyar zata ɗauke hanyar Unguwar su ,har ta gifta ta hango mutum kamar Aseem cikin mota a buɗe. Hakan yasa tayi reverse a nutse ta faka motarta gaba dashi kaɗan ,kana ta fito cikin firi firinta irin na yara marasa natsuwa
Da sanɗa ta fara takowa har gaban motarsa ,ya zurfafa sosai cikin tunani yaji an doka ƙafa da ƙarfi ta daka tsalle ta zuro hannu ta cikin glass din motarsa ta kai masa wawiyar runguma
Comments
Sign in to comment.