← Book details Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 23

Sashe 12

Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban kira matata ba a waya na biyo private jet savoda zaƙuwa na taho Nigeria ,ina sauka na yi bayan taxi daga airport zuwa gida.......just imagine???????

Oum Aphnan

*_ABU UKU_*

Page l

Oum Aphnan✍🏾
______
Nayi mamaki da na isa gidan ina ta horn ba Mai gadi ko daya ,don haka na sallami mai taxi nayi amfani da extra key Dina na bude gidan na shiga,duk motocin gidan suna fake a wajen su ba daya da aka zara bare ince mai gidan ta fita ne,a take na fara tunanin rashin hankalinta da ya aiketa aiken masu gadi gaba-daya .
Falo na danna kaina ko'ina a buɗe kuwa ga ac na bulbula ga fankoki na kasa ,standard fans sina wainawa ,nasan definitely tana nan tana barcin jin dadi ,bansan sanda na saki murmushin tsokana ba ,na taune leben ƙasa
Lallai yarinyar nan kina hutawa ,ynz zan sadada saidai kijini ina laluben hakkina a jikinki a barci.
Da wannan farincikin na cusa kaina bedroom din ta
Ya salam!!!
Mai zan gani?
Yarinyar nan tana tareda wani gardi zaman turmi da taɓarya.
Akan gadona ,gadon Sunnah dinmu,first bed din da na fara kwanciya da mace a kai ,da aure na take iskanci da wani a cikin gidana .

Me zanyiwa yarinyar nan in huce? Na kasa tunawa,nasan ta zubar mun da mutunci nidai,amma tabbas nasan ta kori masu gadine saboda ta shigo da gardinta kuma bukatar ta ya biya .
Ban iya tanka masu ba ,tayi zurfi sosai basa gane motsi ko wani abu haka na sadada da baya da baya na fuce a dakin na bar gidan ma gaba-daya.

Ban dawo ba sai cikin dare ,duk yanda naso in kautar da Kai in cigaba da mu'amalan tarta na kasa....kullum sabo nake ganin abunda na gani ,in takaici ya tukoni sai in banzama neman mata saidai rasa feelings nakeyi ko naje.....amma Yumnah kinsan menene? Wallahi a kanki na fara samun feelings na son in kwanta da mace ,Allah na gode maka da shaidan ya ratsa a ranar nan har kikayi zuciya kika tafi da tabbas sai anyi aika aika.

Kautar da maganarsa tayi da cewa “im so sorry ,ina fatan ka bata kofar da ta baka hakuri?”

“Na fada maki batasan na ganta ba”

“Na kasa mantawa ,idan nazo ko kissing dinta zanyi sai in tuno yanda naga bakinta dagajeje da ruwan maniy din wani gardi can daban yana fucking dinta kawai a take sai kiga sha'awar nan ya koma bakar kiyayya da suyan zuciya....

“Kayi hakuru Aaseem

*_ABU UKU_*

Page J

Oum Aphnan✍🏾
______
Labeebah pov
Tasneem
Aseem

Saida ya Kai Tasneem har gida ,ya tsaya a ƙofar gida ya jira tayi masa iso ,dukda bata so ba Amma haka ya tursasa ta ,bata da zaɓi illah ta barshi ya zo ya gaida mahaifiyar nata kamar yanda ya bukata saidai ita batasan waye zatace a wajen ta ba .
Warr tayi da ido tana kare ma dakinsu kallo ,ko'ina tsaf tsaf an shafe tundurkin sumuntin dakin an goge tas ,don haka ta feshe room freshner a jikin labulayen ɗakin ta fita da sauri bayan ta baiwa mamanta hijab ta saka ,ta fita da sauri tana faɗin “ummana anzo gaida ki”

Aaseem tun daga zaure yake jin kamar ya tsillo masu da hawaye ,har ya shiga cikin gidan,falon ba komai amma fa akwai tsafta da kana’an zuciya .

“Yumnah dauko taburma a shimfida masa mana iya barsa tsaye....sannu da zuwa baƙo”

Shiru Yumnah tayi cikin damuwa tana ɗan rarrabe ido kamar mai neman inda zata hango taburman,nan kuwa tasan ba taburma a gidan bare darduma ,in zasuyi saklah saidai su shimfida dankwalayensu su yi sallah .

Aaseem kamar yaso ya fahimce su ,yayi maza ya yi zaman en bori a gaban maman nasu “Haba babu komai ai nan ma yayi ina yini umma ya sahan jiki”

Kunya ne ya rufe Yumnah matashin milloniya kamar Aseem ne ya zauna a dandaɓaryar ƙasar ɗakinsu?

Cikin girmamawa da tausayawa suka gaisa da ummah .a sanyaye cikin Muryar majinyaci tace “Yumnah baki gaya mun baƙon nawa ba...kayi hakuri ɗan nan Kasan majinyaci baya gane mutane"

Kafin tayi magana yayi karaf ya amshe don ya lura batada abun faɗi
“Ogan ta ne a wajen aiki ,yau na dauke ta aiki a kamfani na ,so a maganarta take shaida mun baki da lafiya shine naji Inason in duba ki ,Sannu da jiki”
Washe baki umma tayi tana zumbuda masa godiya ,bai ankara ba sai kuka ya goce a idonta .

Da ƙyar suka shawo kanta ya mike zai tafi ,ya daidaici saitin ƙafar umman ya ajiye masu mint din dubu dubu ,na dubu ɗari kenan ,dukkansu ba wanda ya ankare da kudin ,amma haka da ya mike zai fita suke zumbuda masa godiya tamkar ya basu doki da kaya .wannan karamci nasu yayi matukar tsaya masa a zuciya ,talaucinsu ya saka masa karin imani da tsoron gamonsa da Ubangiji,wai dama akwai talakawa irin wannan a garin Kaduna? Shifa ya aza duk Kaduna masu kudine ,ashe baya bi ta layukan masu jira a gaban warabbuka ne.

Har yakai bakin ƙofa ,Yumnah batada niyyar tasowa tayi masa Rakiya ,a sanyaye yace “Yumnah ba ko ɗan rakiya?” Murmushi tayi ta kalli mamanta “Ummah inje?”
“Habawa Yumnah ogan naki? Dadina dake kenan ,maza jeki ,sannan ki kara masa godiya mun gode da kulawa ,a gaida tsofaffi”

Zura takalmi tayi ,ta bisa tana tura baki,a bakin mota ta tsaya tana wasa da yatsanta a ɗan ɗarare na rashin sabo .
Shigo mana ” yayi magana cikin tsare gida bayan ya shiga motar ,wanan ya sata shiga motar Ba shiri ai tana rufo ƙofar ya figi hanya da ita ,a tsorace ta waiga ta kalle sa
“ina zaka kaini?”
“Saida kanki zanyi”
Cikin ƙunƙunai tace “Zaka iya ”
Zaro ido yayi cikin mamaki dariya nason kamashi “Me kika ce”
“Ammm ,ehhhh dama cewa nayi ai ku masu kudine”
Murmushi yayi kawai ya girgiza kai ya cigaba da driving .
Wawakeken store ɗin da ake ji dashi a ƙwaryar Kaduna ya faka ,bai kai ga fita ba yaran wajen suka zo gaban motarsa cikin T_shirt mai tambarin kamfanin suna masa Barka da zuwa ,kayan abinci komai 5 yasa aka ɗebo mashi kama da buhunan shinkafa ,macaroni ,indomie , spaghetti,semovita,sugar cubes ,Madara ,Milo ,custard , cornflakes , Mayonnaise,Palm oil , groundnut oil,tins of tomatoes ,pepper mix,Maggi ,kifin gwangwani ,bake beans ke kaya kamar za'a bude ƙaton kanti,saida ya gama tas ya miƙa masu adress din gidansu Yumnah yace aje a sauke.

Yumnah sai yabon ƙazonsa take a ranta lallai wannan mai kyautata ma iyalinsa ne ,ji kayan girki mashaAllah.

“Sorry zaki kara rakani sani wajen karkice kin gaji ” caɓe baki tayi “Nadai soma gajiya ana zafi” dariya ya yi “Dukda Ac dake motar”
“☹️Uhm. Abunka da gida babu ai Ni sanyi nakeji mai sa mura ashe shine acn?” yasan bakar magana ta yanka masa don haka yaja bakinsa yayi shiru suka cigaba da tafiya.

Carpet irin wanda ake mamaye ɗaki dashi gabaɗaya ,ya siya masu mai yawan gaske wanda zai mamaye duk dakunansu har ya ragu ,ya siya masu jajaye ,da manyan labulaye masu kyau suma jajaye ƙofa 10 ,,center carpet biyu na parlour da bedroom ,Tv ɗan matsakaici ,sai standing fan,kana ya siya masu normal camp gas 12L da dai tarkacen ma’aikaci,saida ya gama haɗawa shima ya bada adress din gidansu Yumnah aka wuce masu dashi gida ,Yumnah tanaso tayi magana amma batason tsoma baki a harkar da bai shafeta ba ,amma irin wannan siyayya sai kace dan gudun hijira?!

Basu rabu ba sai bayan magrib ,ya kaita gida tana zuba masa ƙorafi kamar tayi kuka wai mamanta zatayi mata fada
“Shikenan ki shiga gida zan kira waya sai ki Bata in mata bayani”

****
Da sallamarta ta shiga gidan ,sai kuma tayi turus ganin kaya jibgu guda ,umma ta dogaro ta fito tsakargida ,tsahare da hausi makofatansu suna kewaye da kayan cikin kakabi ana jiran dawowar Yumnah

Tana ganin kayan salati ta rafka
“Kai dama gidan nan ya kawo ? Umma kiyi hakuri wallahi Ni ban rokesa ba ,rakashi nayi,na aza ma gidansa za akai kayan kuma bari ina kirashi kiji”

Ta ciro waya ta fara kiransa a waya saida ya tsinke tana kokarin kare kanta sai gashi ya kira wayar “Me yasa za kayi mana haka? Wato mu talakawa ko? I'm highly disappointed on you”

Haƙuri ya dinga bata sannan yasa a baiwa umma wayar yana cigaba da bata hakuri .

Ai tuni su tsahare sun warware sun fara share gidan suka watso komai waje aka fara shirya kaya a dakin ,tsohon kujeran dake falon kamar na jagoran makafi akayo waje dashi ,aka shirya komai ,anan ake ganin damin kudin da ya ajiye masu ,komai aka ƙalkale Yumnah taje ta masu rayayyen girki shinkafa da miya😃abincin da umma tafi so kenan ,yaji kifin gwangwani ,suka ci suka baiwa almajirai sadaka su tsahare suka diba dafaffe da danyu suka tafi gida suna addu'ar fatan alkhairi.

Oum Aphnan

*_ABU UKU_*

Page K

Oum Aphnan✍🏽
_______________
_Ayi hakury kwana biyu na jina shiru ba a san raina bane ,wasunku sunsan dalili ,Thnks for always been in my company🤍_

Labeebah tana zaune ƙuri ta rasa meke mata daɗi a duniyar nan ,tayi wanka tun doshin magriba tasha gayu cikin shaɗanun kayan da tasan ko fasikan matan barikin da suke jan mata hankalin miji iyakan gayun da zasu yi kenan ,duk kuwa tacewa da fitsaransu ,ta ɓata lokaci wajen inganta masa table da lafiyayyun girki ,ta wearing fuskarta da makeup Mai sanyi da daukan hankali ta zauna a falo ta inda indai ya dawo dole zasu hadu kafin ya shige daki ,yau tanaso ta kawo karshen rashin jituwarsu kamar yanda sukayi shawara da kawarta .
Saidai abun takaici har sha daya ta gota na dare ba Aseem ba dalilinsa ,gaba-daya fuskarta yayi dameji da maiko makeup din ya harhade varci ya gama lulluɓe mata ido amma haka ta daure takiyi .
Bai shigo gidan ba saida Yumnah takai ga koransa ,amma shi lalle ba wajen ta ya xoba yana tayata jinyar mamanta ne ,wannan wani irin oga ne???
Chapter 12 · 0% Book details