Sashe 15
Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Munyi kukan rashin Abbah mutum mai kirki da taimakon mara karfi ,haka muka dangana aka share makoki aka zo rabon gado nan en uwansa sukace basu san maganar ba ,komai nashi yana hannunsu sukuma sunƙi bayarwa wai mamana zara cinye mun dukiya ne ,amma fa a zahiri karya ne ,don cikin manya manyan gonakin babana duk shekara yayyanka ma mutane suke suna noma ana biyansu galla tun baban nawa yana da rai ma amma bai damu ba tunda suna ɗan samun na cefane ne a cewarsa.....amma da ya mutu duk sai suka handame komai nasa,da dangin mamana suka matsa ,saima cewa sukayi zasu amshe Ni inje su cigaba da kula dani a Niger din,umma na da Ni kadai na rage mata haka ta rungume Ni aka saida gidan da muke ciki muka siya karamar gida muka cigaba da rayuwa cikin mutunci tunda tana business dinta maraicin kadan ya taɓa mu...katsaham bayan na kammala Sakandire sai karatun ya tsaya sakamakon ƙurji da ya fito ma mamana ,tun tana shan ampiclox har ya kaita da kwanciya wannan yasa muka rankaya asibiti gwanjin farko aka gano Cancer ne,nan fa aka fara daura mu a magani ,yi ake yi ake komai saida namu ya kare muka daga gidanmu muka saida ,muka koma gidan haya en uwan mamana ba masu karfi bane ba amma dukda haka yaci su taimaka muna amma kowa sai ya guje mu ....bazan taɓa mantawa ba akwai watarana mamana ta tashi batada ko sisi da zamuci abinci Ni kam ban sani ba ,dama mun saba in anyi abinci da dare mu dumama da safe muci ranar na fitini mama nifa ban ƙoshi ba ,haka ta dauki sauran na safe ta tasa mun na cinye ...washekari da safe naga shiru bata hura wuta ba ,sai cewa nayi umma kinki hura wutan...cikin tausayawa tace Yumnah in an hura me za'a daura? Munanan muna jira a taskar Annabi ,haka muka dinga hamma mu na birgima a tsakar leda har doshin yamma,lokacin na galabaita na fara ma mamana kuka ,rarrashina ta somayi kiyi hakuri Yumnah na yanzun nan zan mana girki ,mai kike son ci? Cikin fara'a nace Taliya 'yar murji mai manja da wake da kifi...Murmushi mamana tayi ,to Yumnah nan,maza jeki filin sai ka rama , kiyo diddigar icce mu samu mu dafa abincin.....haka na suri tiren da nike siyo icce naje na samo diddiga da yawa a inda suke faskare na kawo ma umma,nan tayi ta nuƙu nuƙu ,har bayan magrib sanann ta haɗa wutar nan ,nan fa hayaƙi ya bulbule gidan ,na fara tari ina hawaye ,sai kada baki tayi tace “Yumnah wannan hayaƙin tamkar maganin sauro yake ,kaf zai kora mana su,haka na daure na hakura na shige daki na kwanta ina jiran hayaƙi ya kare a daura girki,tabbas ya kore mana sauro don haka barcin ukuba ya sureni ,da taga nayi barci sai taje ta kashe wutar ta koma ta kwanta ....to a wannan daren nan wani makofcinmu ya bamu kyautan dubu daya ,nan fa mama ta shiga murna ina tashi da safe ta sa na siyo kamun koko da sugar da kosai muka dama mukasha ,haka na dinga shansa har doshin magriba saida yunwa ta gama sidar mu sannan ta Kwanto sauran ,dari hudu da ya ragu ta kwada mana garin rogo mai ƙuli da dan mangyada mukaci muka kwanta.....haka fa rayuwar namu take gwanin tausayawa ....to da kuma ciwo yaci karfin umma saima aka daga gidan aka siyar muka koma gidan hayan nan da ka ganmu a ciki ,aka dunkulawa wani mai maganin gargajiya wai komin riɓewar cancer a jiki da ya baka magani zai gudu ,tabbas mun yarda kasan mara lafiya idonsa rufewa yake nan muka hada kudi muka bashi ,ashe ɗan damfara ne ,ciwo yayi sauki na kwana biyar sai kawai ya dawo da zafinsa kamar ma yafi nada ,wahala wahala Allah ka yaye mana ,nan na koma maula gidajen masu kudi saboda umma na , sanadiyyar hakan na haɗu da Tasneem ita kuma ta haɗa mu....to kaji labarina
*ABU UKU*
Page M
Oum Aphnan✍🏽
___________
Da sallama ta shigo ɗakin hannunta rirrike da ledojin magani da ta siyo mata ,uwar Binta tayi zaiiii da ido ba tare da ta tanka ta ba ,wannan ya sanyayyar mata da gwuiwa duba da in normal ne da ta dinga washe mata baki kenan tana kiran mata sannu .
Jikinta a mace ,ta samu gefenta ta zauna ,ta firfito da magungunan da abu sadeek ya biya masu ,ta dauko bottled water ta mika mata ,batayi musun amsa ba ,ta karba ta sha duk magungunan,daga nan shiru ya biyo bayan zaman uwar zuba mata ido tayi ƙyam tana mamakin sauyawanta.
Tsarguwa Yumnah tayi kawai tayi zunbur zata miƙe ta bar wajen . Da sauri umma ta damƙi hannunta cikin zafin nama,wannan yasa hantar cikin Yumnah karkaɗawa da karfi .Zaro idanuwarta duk waje tayi sannan a furgice ta kira sunan ta “Umma😳”
Lankwasar da kanta tayi ta kwanta akan pillow din ta tana numfashi a hankali .komawa tayi ta nutsu tana kallonta ,saida ta huta sannan tace “Yumnah yaushe zaki fito da miji kiyi aure?!”
Ɗas! Gaban Yumnah ya fadi
“Ummah aure? Ummah miji? Wlh umma ba Mazan ne”
“Yumnah ba maza? Duk manemanki?”
“Ohwohoo ,mama don fa an ganka da saurayi ba shi yake nuna saurayin nan aurenka zaiyi ba,mutane basa ganewa sai ayi ta zaginka kaƙi aure nan kuwa Mazan ne basu shirya aure ba...Ni walh ba wanda yamun tadin aure Ni kuma kinga ai bazan masa ba ko”
Shiru ummah tayi tana Binta da kallon tuhuma
“Har Aaseem?”
Rararraasss gaban Yumnah ya fadi
“Ummah Aseem ba saurayina bane ba ”
“Amma yana sonki,ki bashi dama mana”
“Aah gasky,kawai dai zan san yanda zanyi in nemo mijin tunda haka ne”
Ta kare magana ranta na tururi ta rasa ya ake samun mijin nan ko itama zata samo a mata auren nan ta huta da yawan magana ,tasha kuka a praying mat Allah ya Bata miji ,amma mutane gani suke tunda tana da kyau duk Mazan duniya biyota suke suna son auranta Amma ita ke koronsu.
Wannan ɓacin ran yasa ta zabura da sauri zata bar wajen ,tanajin kamar tayi kuka ko zataji sanyi a ranta,don wanann babban jarabawa ne da ya samu mata a wannan zamanin Mazan duk ungulayene basa aure.
“Yumnah!!!!?”
Ta kira sunanta a kausashe.
A furgice ta juyo da mamakin sauye sauyen da take gani a wajen mamanta a yanzu din nan.
Zaro kwaroron roba ɗin da kudaden nan da ta gani a ƙasan cinyarta ta ɗago mata shi sama tana karkaɗa mata su ,da alamar tambaya damm a ƙwarar idon maman
Wani yankewa zuciyar Yumnah yayi ya fadi ras!!! Da sauri ta dafe ƙirjinta jin wani nannauyan tsoka na neman fice mata daga ƙirji.
Bakinta makyarkyata ya kamayi amma ta kasa magana.
“Yumnah”
Ta sake kiran sunanta with affirmation ,tuni idonta sun kawo ƙwalla bata san sanda ta zube akan gwuiwoyinta ba.
“Ummanah”
“Sharraf!!!...ko inzo in mitsitsikaki a wajen nan ,ko kinajin don ina ciwo bazan iya horaki bane ba...ko kinajin don kina bani abinci bazan iya zama da yunwa bane ba....i can starve to dieth Yumnah Kuma ke kikayi asara,zan mutu in barki da duniyar...but now back to my issue ,aina kika samo wannan...¿”
“Mamana ki gafarceni mamana,tsoron kar in rasaki ne”
“Kar kiyi min sharri ! Sai nace kije kiyi zina?!”
Dafe kai tayi da sauri
“Lahaula saka ƙuwwa,umma banyi zina kuma ba...”
“su wainnan kayan mazinatan a gidan ubanki kika samo su?”
Hawaye ta fara tuttulowa ,tunda take bata taɓa samun matsala da mahaifiyarta ba sai yau
“Umma tsoro ne!😢Tsoron Kar in rasaki yasa nayi colliding da en iska!”
Tabbas uwar zuciyarta yayi gautsi shirye take ta mata dukan tsiya,ita take kiran ta da zayi zina ,amma ynz da taji furucin daga bakin 'yar sai ji tayi kamar an watsa mata wuta. Dafa ƙirji tayi da ƙarfi
“Yumnah kinyi me???? Hasbinallh waniimal wakeel 😭...Allah ka jarrabeni ta kowani siga Allah ka dauki raina in huta... Alhamdulillah biniimatuka ya Allah” kawai sai ta fara tari ƙwal...ƙwal...ƙwal.
Hysteria follows tana ƙoƙarin shidewa nan take.
Zuwa tayi tana girgiza ta tana ihu tana kururuwa
“ummah banyi zina ba...umma bansan namiji ba ummmmmahhh karki mutu ......😭😭😭😭”
***
Yaseer haka nan yaji zuciyarsa na harbawa ,son ganin Yumnah na ninkuwa a ransa ,suna cikin magana da collegue dinsa ya zabura ya dauki keys din motarsa
Da mamaki ya kallesa yaga haramar fita yake ya barshi a office din
“Yaseer Ina zaka?”
“ina zuwa Yusuf ,kawai in ka fito sakatariyata ta rufe mun ko'ina...” kamar likitan da aka kirasa taimakon gaggawa ya fice daga Companyn da gudu ,wani tukin kasada yake yi saura ƙiris ya kwashe wata Almajira a kwanar gidansu Yumnah ,wanda in aka tambayesa wanann ujilan na menene? Shidai bai sani ba.
Sallama ya ringa kwadawa a bakin zaure amma ba mai jiyosa,tsaye yayi yana kaiwa da komowa gashi ya kira Number Yumnah Bata ɗagawa.....daga can ƙuryar gidan yaji muryr Yumnah ta kwararo ma uwarta kira cikin mugun tashin Hankali
“Ummaaaaah....umma karki mutu,wayyo ummana”
Fit! Ya fada gidan ba tare da yayi shawara da kowa ba.