Sashe 17
Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Basu gama saduda ba saida motarsu ta saka hancinta cikin farfajiyar gidan ,mutane ne damkar,kamar ana biki wanda duk dangin umma ne da suka gujeta da dangin Abbey na niger da suka kwashe masu gadonsu ,Aseem yasa duk aka nemo su ,kudi kare magana aikuwa duk sun hallara kowa na asuwaki da naman kaji da lemu.umma da ta rasa me zatayi kawai sai ta fashe da kukan murna su baba luhi (Kanin baban yumnah) su suka zo har ƙofar motar suka tare ta suna rarrashinta da bata baki ,har falonta suka zaunar da ita. sannan suka shaida mata duk wata gado nasu ma sun dawo masu da abinsu ai don ba hakkinsu bane ba.
Dangin umma ma haka sukayi ta bata baki cikin nadamar abunda suka aikata mata yau gashi takan Aseem ya kwashe maza biyar a danginta ya neman masu jami'a a kasashen waje,masu ɗan kwalin FCE da su poly Kuma duk ya watsasu a sabon kamfaninsa da ya buɗe a birnawa ,buzayen nan dangin baban yumnah ya debi wasu aikin gadi , watering flowers ,masinjoji aiki dai cikin watanni ƙalilan ya sauya masu rayuwa duk takan Yumnah diyar umma.
Sosai umma tayi kewan en uwanta ji tayi komai ya wuce ,bayan sunyi wanka sunci abinci suka sarƙe da hiran zumunci .
Yumnah tsam ta mike a cikinsu ganin kiran Aseem a wayarta ,dakin da ya zama tamkar mallakinta taje ta zauna a gefen gado ta cakumo pillow ta ɗaura a cinyarta tadan matse da hannu kunnenta maƙale da wayarta tana gaishesa kana ta sarƙe da masa godiyar abunda ya masu ,tana farawa kawai kuka yaci ƙarfinta tana ambata sunan abeey abeey ....
Aseem dake zaune a falonsa ,duk rudewa yayi ya fara bata hakuri “Yumnah ki bar kuka nayi maki alkawarin maye gurbin uwa da uba a gareki,zan baki kulawa zan gatantaki har sai kin manta da maraici,abu ɗaya abeey yakeso ki bishi da Addua a duk sanda kika tunosa in kina da hali ki masa sadaka yafi shararar d hawayen nan da kikeyi kinji Yumnah ta”
Gyada kai tayi kamar yana kallonta ,a shagwaɓe tace “To Ni yanzu duk wannan abinda kayi mun da me zan biyaka?”.
“Sa soyayyar ki Yumnah ,ki amince in aureki a sati Uku ,wannan kadai ya isheni ,Kinga gasu kawu sunzo kafin su koma za'ayi komai a gama ”
Wawiyar ajiyar zuciya ta ajiye kafin tace “Aseem bazan iya ba ,kana da mata ,cin amanar yayi yawa ,and beside bazan bar mamana ita kadai ba ”
Rudewa sosai yayi bai taba expecting zai samu matsala a wajen Yumnah ba har haka
“Yumnah Matana ba matsala bace ,na isa da gidana ,maganar umma kuma in har Zaki aureni zan iya dauko ta ku zauna a gidana tare”
“Me? Hauka ma kenan,so kake mutane suna mun gori? Aseem ka dubeni fa er talakawa ta dani wai me ka gani a jikina ka liƙe mun?”
“So da sarkewar jini wanda bazaki taba fahimta ba sai nan da sati Uku in kin shigo gidana matsayin matata ....”
Ƙara yaji a bayansa kana yaji kwatsatsa!!! Alamun fashewar kwalba.
Tsaye take tana tararar da hawaye ,tabbas mijinta ne yake hira da budurwa cikin nishadi suna zancen aure ,nan da sati Uku amma munafukan danginsa basu gaya mata ba .
“Ka zalunce Ni Aseem kuma sai kaci wutar Allah ,Bansan dadin rarrashin miji ba ,amma ji yanda ka kwantar da murya kana ma wata er.iska magana mai sanyaya rai,rabonda inga faraarka na manta amma jibeka zero tension kana mun hira da budurwa a tsakiyar falona wallahi Allah sai ya tozarta ku kamar yanda kuka tozarta aurena ....” rike yake da wayar ya kasa kashewa ,itakuma Yumnah jin Muryar mace na magana kuka_kuka yasa ta gane matarshi ce don haka da sauri ta kashe wayar ta tsaya a gaban mirror tana kare ma kanta kallo tana son gano kyawunta da yasa Aseem like mata har haka.
Aseem da ransa ya gama ɓaci bai taba jin zafin tozarci irin na yau da aka zage masa Hurul'en dinsa ba(Yumnah) a zafafe ya nuna ta da yatsa
“Karki sake zagin mun mata na gaya maki in ba haka ba ynz zan kakkafeki da mari”
“Tsalle tayi ta dira a gaban sa kishi na cinta a rai bata taɓa jin tsanar aurensa ba irin ta yau ita bataki ma ynz su rabu ta kwashe kayanta ta tafi ba
“Ita matar taka taci kaza kazanta,ina matar take ? Matar bariki? Kwartuwar banza karuwar hofi ,dama ita ta hanaka ka sauke nauyin da ya rataya a wuyar ka ? To Bara kaji bazan iya zama da fasiki ba ka kare ko ɗebo mun kanjamau ina zaune lafiya ka goga mun balai”
Kafeta yayi da ido kana ya saki wani killing smile .
“Rashin kunya🤔 ke da nazo na kamaki turmi da taɓarya da zindirin namiji akan gadon mu ,gadon Sunnah na yana cinki,kina nishi kina ya ciki hard ,alamun kina jin dadin abun ba fyade ake maki ba ,ke kika gayyato shi ,amma duk da hakan Ni ban kyamaceki bane sai kece zaki gaya mun maganar wofi? Ki tafi mana ance maki Ina son bude idona in ganki ne a gidana? Aini kin dade da ficewa a raina keda farashi har abadan,haƙuri nakeyi Ina danne zuciyata amma bazan taba kusantarki ba har abadan haka zaki kare rayuwar auren ki matsayin bora ,ba ‘Yanci shashasha kawai”
Ƙafarta kasa daukanta yayi wani kunya takeji kamar ta nutse ,batasan sanda ta sulale ta zauna a kasa ba tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta rijif wani zufa na tsatsafo mata ta ko'ina yau ina kasa ta buɗe ta shige?
Ɗaukan wayarsa yayi ya raɓata zai wuce da saurin ta kamo ƙafarsa ,cak ya tsaya ba tare da ya jiyo ya kalleta ba.
Ka yafemun ,na yarda Ni mai laifi ne ,ka auri wacce kake so amma Ni dai ka dawo da sona ,ban taba zina ba wannan ne na farko kuma sharrin zuciya ce da kewarka mijina,kasan wacce ta saba da dadin namiji bazata iya jure sati Uku ba namiji ba”
Takaicine yazo ya tokare masa maƙoshi baisan sanda ya ɗage ƙafarsa da ta rike ba ya hambareta ta kuwa ƙumu da kujera haka ta goce da kuka mai ban tausayi da tarin nadama
Lallai kaji tsoron mara magana wanda zaita kallonka kana masa abu amma ya gaza da furta maka ,tabbas akwai ranar ɓacin rana.
Oum Aphnan
*ABU UKU*
Page Q
Oum Aphnan✍🏽
Yanda Kasan ta toni ciwon haka ya faru ,ba uhm ba uhm uhm amma fa ta muzanci kanta ,kullum ya shigo gidan ta dinga binsa kenan tana bashi hakuri yayi mata afwa ɓacin rana ne,kuma barazana tsohon saurayin nata yayi mata akan in Bata yarda ya kwanta da ita ba zai nuna ma Aseem din tsofaffin hotunan da sukayi na can baya ,lokacin tana ganiyar clubbing , Tsoron kar ya kashe mata aure yada ta amince masa ya kusance ta ,to ashe tana jika ,abunda ake gudu dai shi ya faru in baa tura masa ta waya ba ya gani with his koru_koru eyes.
Aseem har ransa yace ya yafe mata amma ba ruwanta dashi ba ruwanta da matarshi in sunyi aure
A sanyaye take kwararo masu addu'ar fatan Alkhairi tana masa Alkawuran bazaa taba samun ta da matsala da matarsa ba ,Ta daura da shima auran Yumnah da Aseem Albrka tana binsu da kyawawan Addu'oi ,komun abunka sai ta baka tausayi.
Aseem kansa jikinsa ya ɗanyi sanyi don haka tana addu'ar yana daukan ma Yumnah a waya ba tareda ya bari ta sani ba ,saida ta shige daki sannan ya tura mata a waya
“Ki saurari yanda Uwargidan ki ,ke zunbuɗa maki Addu'oi hurrey,Allah yasa ku zauna Lafiya ku zama tsanin faruncikina ,har karshen rayuwarmu”
Haka ya rubuta a ƙarƙashin voice note din da ya naɗa ta manhajar whatsapp .
Yumnah haka nan taji ƙirjinta na harbawa da gudu da gudu
Anya kishiya kuwa zata ƙaunace ka don Allah ? Anya ba wata a ƙasa? Duk da baya gabanta amma ta kasa nuna jin dadinta a wannan al'amarin ,sai kawai emojin Murmushi ta tura masa(☺️) ,don dai kar ta bar message dinsa ba amsa .
Wani mugun damuwa kuma duk ya dameta amma bata fada ma kowa komai ba.
****
Biki kam sai ƙara matsowa yakeyi ,Labeebah na ƙara matsan Aseem tana shiga jikinsa ,saboda yanda take gwada son Yumnah sosai a ranta ,da ya dawo bata da magana da ya wuce na Yumnah .ina amaryan mu? Halan daga wajen amaryanmu kake?
Uhmm anya amaryanmu bata maka wayo kuwa😄naji wani ƙamshin turare me dadi kake yi ga dukkan alamu a jikinta yake...
All these tsokana irinsu ke shiga tsakanin Aseem da labeebah ,wannan yasa ya kan ɗan saki rai har yayi slipping line yayi ta bata labari ai Yumnah tayi kaxa ,ai anyi kaza aima ba tare zaku zauna ba a sabon gidana zamu zauna da ita...bla bla.
Labeebah bata taɓa nuna damuwarta ba dukda batun komawa sabon gidan da zasuyi ba ita ya caki ranta,shiknn er talakawa ta caɓa ,wato ita an kaita secured waje suna maƙoftaka da gidan gomna ,in ta haifa yara ,ba zasu ringa abota da gama garin mutane ba sai yaran gomnoni masu hawa da sauka ,ita kuma da aka ɓata lokaci ana tsara yanda fasalin gidan zai zama harda contribution dinta a wajen fidda fasalin gidan tun kafin suyi aure ynz duk ya tashi a banza???
To ya ta iya da nata ƙaddarar? Tsalle daya ake a fada rijiya amma sai kayi dubu baka fito ba.
“Love ka bani number ƙanwata muna gaisawa ko ɗan gaisuwar jumma'a din nan ne”
Yi yayi kamar baiji mai tace ba ,saboda baida niyyar bata ma ,da labeebah ta lura kamar ransa bai so ba sai tayi maza tai zipping bakinta ,ba tareda ta matsa ba . Saida ta tabbatar maganar ya bar tunaninsa kamar na tsayin minti talatin sannan ta tashi jiki a mace tabar dakin .