← Book details Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 23

Sashe 13

Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nishadi ya karkaɗo kan motarsa ya taho gida ,wani malolon takaicine yazo ya sandare mata a maƙoshi ,bayan ta daga ido ta kalli lokaci . Wai sabon angone yake kaiwa wannan daren bai shigo ba ,what the fuck?
***
A nutse ya shigo falon fuskarsa fal fara'a amma yina ganinta ya nema walwalar fuskarsa ya rasa ,ya wani murtuke fuska da sauri ta mike tsaye da nufin ta dinfare sa ta rungumesa,saidai rashin ganin fuskan hakan ya sata jan reverse ba tareda ta iya ƙarasawa ba,sai wasu Mayun hawaye da suka kwanta mata a ƙwarmin ido...wani tunani tayi “Labeeba lokaci yayi da ya kamata ki fara taka ma mijinki burki ,ya gane cewa kefa matarsa ce” da tunanin nan tajefa masa tmbyr da ya sashi ƙamewa ƙyam akan ƙafafunsa

“Aseem daga ina kake?....wai me yasa kake kaiwa dare ne? You own me explanation”

Kallon banza yayi mata irin na ɗage din nan
“ni namijine ina da damar kaiwa dare a duk inda naso harma in kwaana”

Cikin hargagi tace “Noo wlh baka isa ba ,nan gidanka ne ,amma dole ka dawo akan lokaci ,kuma dole ka kwana a cikinsa Matsawar ba tafiyar dole bace ta kama ka ba...to idan har ka shirya kaiwa dare a waje dole ka fada mun,kana ina? Tsawon yaushe zaka kai a wajen? Kuma tare da wa kake?”

“To banda lokacin nan ynz” ya fadi yana murtsuke ido da alamun barcine cike a cikinsu .

Wani zabura tayi ta sura tsalle sai gata tasha gabansa

“Taf ai wallahi sai ka magantu....(muryarta rawa ya kamayi irin za tayi kuka din nan) see atleast idan ma nayi maka wani abu ne ,da baka so gwara ka fada mun Ni na gaji da rayuwar rashin encin nan ” tsaida idonsa yayi a kanta cikin mamaki yana gyargyada kai ,wannan yasata kautar da kai ta rike ƙugu tana girgiza kai

“Baza kuwa kabar wajen nan ba yau sai kayi magana” nuna gefen kafadarta yayi da hannu ta inda yakeso ya raɓa ya wuce “Uhm ko zaki dan bani hanya in wuce?”

“Wallahi bazan baka hanya ba yau sai kayi magana ko mu kwana a nan”

Baice komai ba yaja baya ya raɓe gefe ya sama kujera ya zauna ,ya daura hannunsa a Kasan ƙuncinsa ya lumshe ido ,da alamu dai barci zaiyi a wajen.

Cikin kwaratsi tace “Mr. Aseem...hehehehe...au maimakon ka yi magana ka gunmace kazo kana gyangyadi anan? Aseem bana son inyi judging Dinka negative Amma tabbas hakurina ya kare ina bukatar in rike ɗan kaina ...inaso kayi mun ciki ,mai yasa baza ka bada naka gudunmawar ba a matsayinka na mijina”

Shurune ya ratsa ba uhm ba uhm uhm ,saima ɗagowa da yayi ya kalleta ,bayan yaji ta kusa minti biyu bata sake magana ba “Is that All?”

Dafe ƙirjin tayi kamar mahaukaciya “Aseem na shiga uku...tambaya na ma kake na gama? Anya Aseem bakayi gamo ba?”

“Naji duk abinda kike cewa amma matsalar shine na gaji ,ina bukatar barci idan na huta za muyi magana”

Tsirrr wani hawayen takaici ya zubo mata
Batasan sanda ta ƙwalla masa kira ba,amma ina ! Shi tuni ma ya bar mata falo din ya yi wucewarsa.

*****
Tasneem kallon Yumnah tayi da taci azaban gayu tayi kyau ba'a magana gashinta yasha gyara sai sheƙi take ta mirza dauri daidai da yanayin kayan ,bubu ce na skyblue Les Mai ratsin dari blue ,yana da Dan nauyi ,ta zuba fashion necklace a wuya da dan kunne da Bangles tayi kyau ,fuskarta wasakayau daga powder sai man leɓe sama ya ɗanyi pink sama ya ɗan yi duhu sai sheƙi yake ,ta taje giranta ta miƙar da gashin idonta da mascara yes she look take away. Tayi kyau so matured.

Yumnah yanzu ne lokacin ki da zaki yagi rabonki ,yanda kikeji da kyau din nan ,ga karuwar jiki Allah ya baki mai daukan wanka,to kiyi maza maza ki yayyaga rabonki yakai ki macca ya siya maku gida ki mallaki mota da gwala-gwalai daga nan inma zata watse ta watse...”
*_ABU UKU_*

Page L

Oum Aphnan✍🏽
_______________
Yumnah fa ta amshi ,tayin Tasneem hannu bibiyu kuma da Alamu tana neman zurmata a harkar bariki sosai da sosai ,wanka take dauka na fitar arziki ,Aseem warware mata aljihu yake yana masu bindiga da kudi ,saidai ko da alama baya neman ta da iskanci ,shi in ance me Yasama ya damu da ita shi bai sani ba ,amma dai yasan yina samun farinciki sosai a wajenta ,in yazo gidan ya dinga jin drama dinsu da innanta kenan yana kyalkyalewa da dariya.
Kullum sai sun sa abinci dashi ,tun baya sakin jiki yanzu ma permanent ne yana da kaso a abincin gidan ,Yumnah ta zage da kashe Aseem da girkin en gayu da na gargajiya, wannan ya kara wanzar masa da mantawa da duniyar Labeeba sanann kana ganinsa kasan yana cikin farinciki bakamar kwanakin baya ba.tsakaninsa da gida can daren kwanciya barci .

***
Yau Yumnah da kanta ta dauki mamanta da taimakon me keke sukaje sukaga likita ya dawo dasu gida da tarin siyayyan magunguna masu mugun tsada,wanda indai Allah ya taimaketa akwai possibilityn ya kone cancerous cell din dake jikinta.

A falo ta kwantar da ita ,ta shiga ciki ta dauko mata bargo ta lulluɓe mata daga ƙafarta zuwa ƙirji kana ta kawo Mata ruwa ta ajiye mata a gefe in case in tana da bukata ,ta kwashe kayansu ta maida daki ta zo ta fice .

Tana fita ƙofar gida ta fara tare ɗan sahu ya kaita central ,Saidai masu dan sahu ta tare suna canyara mata kudi masu yawa ,don haka take sallamarsu .
Haushi abin ya fara bata ga zafin rana gashi masu abun hawan tsada suke mata gani suke kamar akwai kudi basu san duk Kuru bane , alhamdulillah yanzu anfi karfin ci da sha kuma ba zullumin wajen kwana amma kudin kashewa baya banbaruwa tunda dai ana ta maganine ,kuma batason Aseem ya gaji dasu shiyasa take hidimar mamanta a boye.

Tana tsaye tana kange fuskarta da rana sai ga er mota ƙirar Venza tazo zata wuce ta gabanta ,har ta gifta sai kuma motar tayi reverse kadan ta dawo gaban Yumnah ,da mamakin wanda zai santa a tsakar ranar nan ya faka mota ta leka kanta windown motar da aka sauke don ita dai tasan rankatakaf danginsu babu mai mota ko peogeot kuwa.

Washe baki tayi dukda bata gama wayansa ba amma tabbas ta taba ganin fuskar
“Heyyy Yakike ? Abu_sadeek man friend din tasneem”

Washe baki tayi tabbas ta gane inda suka hadu gidan su Billy wato dai jarumin su Tasneem da ake buga takara akansa don ya fi jin daya a cikin ransa tsakanin Tasneem da Billy .

“Laaa sannu ko ! Na gane ka"

“ya kike tsaye a rana haka? Kyakyawa kamarki ai abun kunyar samarin zamanine irin mu mubar irinku rana na taba lafiyar skin dinku"
Yumnah Bata saba da karuwancin nan ba don haka ta sinnan da kai gami da cewa “Wallahi iyakata central ,kaga keken kamar an sharesu..”
Haba ba damuwa shigo in karasa da ke " ya magana yana mika hannunsa gefen me zaman banza ya buɗe ta shiga ta rufe suka nausa kan kwalta.

***
Umma kasantuwar likita yayi mata alluran masu yawan jini dana kumburin da kafafuwarta duk suka tartasa ,yasa ta jin fitsari sosai .don haka dakyar dakyar ta mike zaune ta jawo sandarta ta san dogara tana bin bango har ta isa Toilet dinsu tana fitsarin kuwa tajita wasakayau,ta dawo falon tana korafin Yumnah tabar kaya ko ta ina.

Mika hannu tayi zata janye ninkakkun kayan da suke ƙasa a gefen Ghana must go din Yumnah kawai sai ta janyo wani abu a bakin leda ,kafin ayi haka washarrrr wasu abu masu yalala sun zubo kamar safan hannu na ganin likita . Gaban umma haka siddan ya fadi ras! Da sauri ta duƙa ta mika hannu ta dauki daya tana jujjuyawa ,sannan ta kanga idonta cikin hujin roban mai kama da balo balo ,maiƙo ta gani yalolo gwanin ban ƙyama ,,yamutsa fuska tayi tana kara karantar suffar ledan ,gayinan shatin alauran namijine ,wato kenan dai condom ne (kwaroron roba) da mazinata sukafi anfani dashi in zasuyi fasikanci suna tsoron daukan cuta.

Kanta ne ya sara mata ,to mai Yumnah takeyi da abun nan mai yawa haka na maza da na mata? Shin ma a ina ta samu? Saka hannunta tayi a ledar Saiga damin kudi sunkai dubu ɗari tsofaffine dai kudin en dubu dubu da en dari biyar .

Ƙirjin umma ne ya doku.
Lahaula wala kuwwa ta illa billahi.ya rab karka jarabceni da bakar gani ,ace na gaza da baiwa diyata daya tilo tarbiyya har sai ta fada tarkon zina da mazinata......

Tagumi ta rafka a wajen hawaye marasu a sani suka fara bulbulo mata,mutuwar marigayi ya dawo mata sabo fillll....gatan da ya dinga gwada masu sanda yake raye shi yake dawo mata a rai.
“Allah sarki Alhaji bazai yafemun ba Matsawar nabar bayansa ya lalace ...mutuwa! Mutuwa mai yankan tanaji da kauna ....Bara in jura dawowar yumnan tayi mun bayani”

*ABU UKU*
Page M
Oum Aphnan✍🏽
___________
Da sallama ta shigo ɗakin hannunta rirrike da ledojin magani da ta siyo mata ,uwar Binta tayi zaiiii da ido ba tare da ta tanka ta ba ,wannan ya sanyayyar mata da gwuiwa duba da in normal ne da ta dinga washe mata baki kenan tana kiran mata sannu .

Jikinta a mace ,ta samu gefenta ta zauna ,ta firfito da magungunan da abu sadeek ya biya masu ,ta dauko bottled water ta mika mata ,batayi musun amsa ba ,ta karba ta sha duk magungunan,daga nan shiru ya biyo bayan zaman uwar zuba mata ido tayi ƙyam tana mamakin sauyawanta.
Tsarguwa Yumnah tayi kawai tayi zunbur zata miƙe ta bar wajen . Da sauri umma ta damƙi hannunta cikin zafin nama,wannan yasa hantar cikin Yumnah karkaɗawa da karfi .Zaro idanuwarta duk waje tayi sannan a furgice ta kira sunan ta “Umma😳”

Lankwasar da kanta tayi ta kwanta akan pillow din ta tana numfashi a hankali .komawa tayi ta nutsu tana kallonta ,saida ta huta sannan tace “Yumnah yaushe zaki fito da miji kiyi aure?!”

Ɗas! Gaban Yumnah ya fadi
“Ummah aure? Ummah miji? Wlh umma ba Mazan ne”
Chapter 13 · 0% Book details