← Book details Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 23

Sashe 16

Abu Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Page O
Oum Aphnan✍🏽
____________
Lallai rayuwar su Yumnah gaba-daya Abar tausayi ce.
Aaseem hakuri ya dinga bata yana rarrashinta ,amma da yake tana da tender heart sau ta nuna sam ita abun ma ai bai dameta ba ,amma Deep inside she was hurt.
***
Kwana uku tsakani Ummah ta warke sarai tana gane mutane ,sauki Alhmdllh suna jiran sallama ne ma su koma gida . Aseem kam duk wani condition dinta sun gama magana da likita ,ya kuma tambayi shawararsa wani kasa yake ganin ya dace a fita da ita ,Cairo nan ne asibitin da suka tsayar da shawara,don haka ya amsa Number equipped doctor din yayi mata booking asibitin online ,Saida aka gama komai a kwanaki ukun nan sannan ya zo ana bata discharge daga asibiti airport suka wuce direct da ita umma tayi mamakin haka Yumnah ma haka ,bai basu wani damar tambaya ba ya basu tikitin su ,suka wuce jirgi so speechless.
***
Yumnah da Umma lafiyar Allah suka sauka a Cairo ,Suna sauka drivern asibitin ya daukesu aka wuce dasu dakinsu .
Asibitine amma kamar gida ,ko'ina a tsare ga Centre table an shirya masu tuwon shinkafa miyar egusi da kifi da nama ,da jollop rice irin na en Nigeria ,sai bottled water da tarkacen tea.
Lallai asibitin suna da tsari wato kitchen dinsu caterers suke dasu na mabanbantan ƙasashe da an kawo ka za'a kawo maka abinci irin na kasanku.Saida sukayi wanka sukayi sallah,sanann suka zauna cin abinci , Umma taji dadin tuwon nan don haka taci sosai ,itakam Yumnah rice din taci don itafa a duniyar ga bata son abinci mai nauyi shinkafa ma na dole take ci......ƴar talaka da bibiyar jidali ,ohshaaa maybe shiyasa kullum take jinta shakaf ba nauyi tamkar a hureta.

Sun gama cin abinci lafiya ,daga nan umma ta dinga zambadawa Aseem kyakyawar addu'a , Yumnah daukar wayarta tayi ta tura ma Aseem sakon Godiya ta whatsapp ,aikuwa yina online don haka ya kirata sukasha hira yana tambayarta tsarin asibitin yayi masu ko a sauya

“Hmmm asibiti kamar muna hotel ,Ni na kasa banbancewa ,bude ido mukazo ko ganin likita”
“Hhh duka Yumnah ta ,amma dai ynz ina ummah” waigawa tayi ta kalli umma dake kishingida tana sipping tea.
“Ga Umma nan”
“A ce ina miƙo gaisuwa”
“Uhm uhm gata ku gaisa da ita”

“Ƙasimu Ina yini ya tsofaffi? To ƙasimu Allah yayi Albarka , Allah ya raba ka da Tsoho da tsohuwa lafiya,Allah ya baka zuriya ta gari da zasu taimaki Al'ummar musulmi baki daya ”

Da Amin Amin ya dinga bata amsa amma bakinsa fal,dariya wai ummah ita lallai ba sunansa Aseem ba sunan sa ƙasimu ne,wai bata taɓa jin sunan nan ba.

Yina jin dadin umma saboda yawan Adduarta a gareshi.

***
30days later

Ummah dukda asibitine na jin daɗi amma fa jiki ya tsananta ,Allurai ake mata masu ƙarfin gaske ,wanda akace da gubar dafin maciji akeyi ,wannan yasa harta faratanta koɗewa suka koma baƙaƙe.
Gashi idan ana mata wannan alluran mai mugun tsada wani kumfane zai ringa fita daga bakinta kamar dafari ,sai Yumnah tayi ta nade mata shi da tissue tana discarding a dustbin

Tafiyar farko duk wani gashi a jikinta ya fara kaɗewa yina ciccijgewa saboda tasirin alluran a jiki.

Ynz Yumnah ta fara jin tsoron anya uwarta zata rayu kuwa a maimakon sauki ciwo gaba yakeyi duk ta shafke.

Gashin kanta na fara fita ,Nurse dinta ta aske gashin kaf dake kanta ta dawo kamar namiji ,aka koma bata abinci ta hanci ana amfani da roban Bada abinci da magani (NG tube)

Hankalin Yumnah fa in yayi dubu ya tashi don haka taje ta samu likita da ƙorafinta
“Likita kana ganin Umma ta zata rayu kuwa?”
Amsa ya bata kai tsaye
“Ni bana ceba ,rayuwar ta yana under possibility en yanda jikinta ya amshi maganin ne ,amma abunda muke bincike akai ,Cancer a iya ƙafarta ne ? Ko kuwa sankarar jini gareta ? Gaskiya in na jinine akwai matsala....”

Duddulo idanuwa tayi waje cikin tashin hankali ,ban gane ba likita kuna nufin kawai kuma amsan mana kudi kuke baku da maganin ciwon mamana? Wannan ba yaudara bane ba?”

Miƙewa likitan yayi ya ɗan yage labulen window ɗin sa kadan ,daidai sata balarabiya ta fito daga quaters dinsu da matacciyar fulawa duk tayi yaushi ta zama mai ruwan ƙwai(Yellow) wannan alamu ne dake nuna shukan bata samun iska kuma tayi yaushin da yarda ita za ayi bazata taɓa rayuwa ba,don haka ne ma matar ta dauko fulawar zataje inda suke zubar da shara ta zubar.

Nuna mata matar yayi da ɗan yatsa.
“Kinga ,idan har wancan fulawar da ke hannun matar can zai sake rayuwa bayan halin da ya shiga ,to tabbas ummanki zata iya warkewa daga jinyar da takeyi bayan sankarar jini ,amma fa wannan alluran da muke mata matters ,Saidai muna da hope inda zAa gayyato wani likita daga India to zai iya magance matsalar ,shikuma kafin ya kashe uzurorinsa yazo kawai sai an ajiye masa kamar miliyan hamsin? Can You afford that?”

Wani wahalallen kuka Yumnah ta barke dashi ,ba tare da tayi sallama da likitan ba ta fice da gudu ,duniyar na juyawa da ita,Wannan wani irin jarabawa ne? Ubangiji ka sassauta mana....

Kewayawa da gudu tayi wajen balarabiyar nan,taje daidai tana shirin jefa kaskon fulawar a cikin ƙatoton abun tara sharan asibitin ,tayi maza ta riƙe mata hannu

Da sauri ta ɗago ta kalleta
Yumnah ji take kamar zata cilla mata uwa a shara ne,don haka ta ce “Ya zaki kashe halitta mai rai ,ki hofintar dashi ba tareda kinyi yinkurin tattalin lumshinsa ba”
“Bazai rayu ba” ta bata amsa kai tsaye da turanci.

Ras! Gavan Yumnah ya fadi ,maganar likita ya sake dawo mata kai ,indai fulawar nan zai rayu to mamanki ma zata rayu.

Warce fulawar da sauri tayi a hannun balarabiyar ,cikin kuka tace “Ni ki bani zan raya ta”

Matar cikin mamaki ta sallama mata kaskon fulawar ta juya tana waigen Yumnah da mamaki sai buga tuntuɓe take kamar zata ci ta baki ,koda ba abun mamaki bane,don Anga mutane irin na Yumnah a asibiti ,maybe tazo ganin Neuro_psychiatric doctor ,ko Kuma she's depressed.

Yumnah carefully ta rungume pot din tamkar jariri ,taje bayan windown dakinsa inda ta gani akwai kasa ba interlockz ta samo karfe ta cacake ,ta fasa roban fulawar ta fiddo shi a ciki kamar manomiya ,ta maida fulawar a kasa tayi watering din fulawar ,sannan ta wanke hannu ta banzama kasuwa nemo taki asalin masu kyau wanda akeyi da Natural elements,wato
(NPK fertilizer,Nitrogen, phosphorus and potassium)haka ta siyo tazo tana watsa ma shukar, ƙura_ƙuran kamar dawa, amma zo careful batareda ta bari takin ya taɓi jikin root ko stem din fulawar ba ,Saida ta gama tas ,sanann ta dawo daki tayi wanka ta cigaba da kula da mamanta .

Tun daga nan marasu lafiyarta suka zama biyu ,mamanta da fulawarta ,indai bata daki to tana nan ta gurfana a gaban fulawa gwanin ban tausayi.
Ana wannan ritsitsin Aseem ya diro garin
Hankalinsa ya tashi matuka ganin jikin umma ,nan ya tambayeta ina Yumnah kwatanta mata inda kullum take ganin tana zuwa tayi ,yakuwa je ya sameta,sai nome kananun shukokin da suka fito kusa da fulawar ta take tana kuma hawaye a lokaci guda saboda sam fulawar bata ko motsi tana nan a langaɓe hopelessly.

“Yumnah ta meke damunki? Me ya sameki?,Taya zakizo kina bauta ma mataccen fulawa?”

Ji tayi kamar an watsa mata ruwan zafi “😡Idan har kana ƙaunata to ka tayani rayar da wannan fulawar,itane kadai fatana a rayuwa😭” kawai sai ta tsage da kuka.

Birkicewa Aaseem yayi ”Yumnah me ya sameki? Kinyi gamo ne wai?”

Oum Aphnan
09065990265
Abu uku @₦500 via
7782217014, mohammad Hassana, Fcmb

*ABU UKU*
Page O
Oum Aphnan✍🏽
______
Aseem
Yumnah
Aseem ya tausaya ma ,Yumnah kwarai a ransa ,amma bai nuna mata damuwarsa ba ,don hakan tamkar zai kara raunana mata dauriyar da takeyi ne,Saida ya gama settling komai na chemotherapy ,ya ajiye duk kudin da za ayi hayan likitan umman sannan ya juya Nigeria . Kwanci tashi asaran kwana ,gashi umma ta fara samuwa ras take gane mutane ,sauki mashaAllah ,sai amsan magani da takeyi under supervision ,bacin haka na da tuni an sallame su ,don da ƙafarta tana fita har varendar inda dakinsu yake tasha iskanta ta dawo dakin ta ,lapiyar da ta gagareta sama da shekaru nawa,ashe duk rashin kudine ba wani abu ba.....Ubangiji ka bamu Kudi na halas kayi mana rowar cuta.

Aseem kam zuwansa uku while hospitalization en Umma kuma a wannan zuwan ne ya samu damar shaida ma umma asalin muradin ransa na son auran Yumnah,da faty taso taki amincewa amma da ya lura da haka sai ya fara mata magiya ,da cewar shi ba tausayin su yasa zai aureta ba ,zai aureta ne saboda dama can tayi masa yana sonta kuma tarbiyyar ta shine abu na farko da ya ja ra'ayinsa .....” Umma tayi farinciki da dacen mijin da Yumnah tayi don samun miji irin Aseem babbar rabo ne,Rabo badon kasancewarsa mai kudi ba ,sai don halin dattakonsa da tausayin na kasa dashi ga kiyaye addininsa....

Aseem,saida ya tabbatar an kusa sallamarta sannan ya samu kyakkyawar gida a tsayensa a unguwar Rimi ya siya masu ,ya kira company aka gyara da kujeru gadaje da electronics ,in fa kika ga gida sai ka rantse gidan wata hamshakiyar macece da tayi dacen samun attajiri.

2Months Later
Jikin umma yayi garas bazaki taba cewa tayi jinya ba ,tayi luwai luwai kamar wata matan mai kudi dinnan daga Yumnah har ita sun kyau tsame hannu ka taɓa.

Haka suka rankayo Nigeria cikin farinciki da tarin godiya .

Daga airport Aseem yasa aka zarce dasu sabon gidansu da ya gama jin komai na morewar rayuwa ,gida yakai ya dawo ga masu gadi tun daga kofar gida da uniforms dinsu
“Oh Wai mu Yumnah mune a daular nan ,ashe dadin nan zai sake dawowa cikin rayuwar mu?”
Chapter 16 · 0% Book details