← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 63

Sashe 62

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

+bagaruwa ( Zaki samu a wajen masu magani gargajiya ).
+zaitun soap ( Zaki samu a Islamic-medical-centre )
+farin miski ( miski samu Islamic center )
+hulba na ruwa (Islamic center )
_Amma zaplan zaitun ake hadawa dashi ki Duba idan Zaki saya Amma idan kin rasa zaflan Zaki iya sanyan zaitun soap._
in kin sayo sai ki dauki bagaruwa ki daka' tayi laushi ki zuba a roba. Sai ki yayyanka soap zaitun din kanana a kan garin bagaruwa ki nemo miski ki hada tare ki kwabashi da ruwan hulba ki kwaba sosai yayi kauri ya damku. Sai ki zuba a roba mai kyau ki rufe.
In kin ga dama in kwaba wa zai baki wahala ki daka a turmi in kin gama wanka sai ki wanke gabanki dashi.
Idan kika kiyaye wadannan babu wani abinda zai Hana farjinki dandano ko ni'ima kuma babu ruwan ki da wani matsi idan zakiyi aure haka Zaki shiga gidanki kuma zakiga yadda Zaki gigita mijinki ba tareda kin saka komai a farjinki ba.

 

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿

1005. . . . ... 1006

. . . . ."babu abinda ki ka yimin khairat,amman ko sani ƙaunarki ce ta janyomin hakan,don haka ki yi haƙuri ki karɓi wannan ƙaddarar daman Allah ya riga daya tsara hakan kuma bamu da yadda zamuyi,sai dai mu taya junanmu da addu'ar samun abokan rayuwa na gari".

Duk yadda ya yi wa su Baba na bayani haka ya yimin ranar na yi kuka sosai,mama ta dinga rarrashi na don ita tuni tasan da maganar daman,shiru dai kawai ta yimin.

*********

yau ne yaya Bilal zai dawo daga ƙasar germany,na yi tsaye a kitchen ina tunanin abinda zan dafa masa,tuno da ko kallon ƙurata ma baya yi yasa duk jiki na ya yi sanyi sosai,na dawo farlo na samu waje na zauna na yi tagumi,Nadiya tazo ta rungumeni ta baya ta ce"sai amaryar yaya Bilal yau kuma tunanin me ki ke?bayan yau dai alƙawari ya cika an mayar da aurenku".

Da sauri na tashi ina girgiza kai tunanin hakan kamar ba zai yiwu ba,Nadiya ta sanya dariya sannan ta ce"kada ki yi mamaki khairat yau Abba ya É—aura mana aure ni da ke,ke da Yaya Bilal ni kuma da Yaya Abas".

Abas ɗan gidan baba Hamza ne shine babba daman kuma baiyi aure ba,matuƙin jirgin sama ne sosai na yi murnar haɗin auren Nadiya da Yaya Abas don shima bai da matsalar komai sai matsalar mahaifiyarsa,ita ce bata barin surukanta su zauna lafiya,don ma hajiya kaka na taka mata burki.

A yadda aka saka tarewa ta sai nan da wata uku ma masu zuwa don little khairat ta ƙara ƙwari.Babanta yana bugo waya kullum yaji muryar ƴarsa don yanzu suna ƙasar england shi da amminsa.yana aiko kuɗi duk wata masu mugun yawa wai a kula masa da ƴarsa.

Har ɓangarensu Yaya Bilal naje Umma wato hajiya Ruƙayya tana zaune a farlo Iman da Irfan na ɗafe kan cinyarta suna bata labari,Iman na ganina ta taso da gudu ta rungumeni amman irfan ya juya ƙeyarsa baya ƙarshe ma ya tashi ya nufi ɓangaren mahaifinsa.sosai abin ya tsayamin araina yaron yana bani mamaki sosai,tabbas ayau ba sai gobe ba zan dawo da komai sabo,zan gyara rayuwar ɗana da kuma ta mahaifinsu,ya zama lallai inyi wannan aikin.

Gaisuwa ta mutunci muka yi da Umma ta ce"yauwa gwara da ki ka shigo daman fita zanyi gashi kuma Nusaiba tana skull kin san yau ta fara shiga lecture,don Allah bazan rufe ko ina ba,idan babu damuwa kiÉ—an zauna yanzu zan dawo."

Adawo lafiya na yi mata na rakota ta fito sannan na yi sashen yaya Bilal,ina shiga na samesa da yaransa suna ta wasa suna Æ´an guje guje,na koma gefe ina kallonsu cikin sha'awa,ina ma ace tare dani ake wasan?cikin iyali na?.

Yana juyowa ya kalleni ya watsar,abin ya yimin ciwo sosai,amman sai na daure na ƙarasa inda suke na ruƙo hannunsa ta baya,da sauri ya juyo ya kalleni fuskar sa ta haɗe sosai alamar ƙiris ya ke jira.da sauri na tsugunna guiwowina bisa ƙasa na sunkuyar da kai na tare da riƙe ƙafarsa na ce"Yaya Bilal na kawo kai na gare ka,duk hukuncin dana cancanta ka yimin na yarda dashi bazan ga lai finka ba,don na cancanci ka yimin komai".

Na faɗi hakan ina zubarda hawayen,kada samun farin cikin rayuwa har yanzu.a hankali ya ɗagoni shima idanuwansu sunyi jawur.na kallesa nima yadda naga ya rame sai ya bani tausayi.hannunsa naji kan fuskata yana gogemin hawaye ya ce"Khairat dai na bani haƙuri,ni ya kamata in baki ba ke ba,tunda ni ne mr laifi,sai kawai ya tsugunna agabana ya ce"khairat ki yafemin don Allah duk wani laifi dana yi miki,wanda na sani da wanda ban sani ba."

Da sauri na tsugunna nima ina hawaye na riƙe hannunsa cikin nawa hannunsa me taushi da laushi na ce"Abbansu Haidar baka yimin komai ba ni ce ya kamata in nemi yafiyarka".

Murmushi ya yi ya rungumeni naji wani mugun daÉ—i jina jikin uban yara na,Irfan yazo da sauri ya ce"Dady ka daina rungometa bata son ka fa"?.da sauri Bilal ya janyosa jikinsa sannan ya ce"irfan mamynka na sona sosai kuma tana sonka sosai".da sauri ya ce"Dady yanzu ta daina xaginmu kuma tana sonka".?

Da sauri uban ya ce"ƙwarai yanzu duk tana sonmu daman cen tana sonku,kawai dai koya min darasi ta yi."

Irfan ya rungumeni sannan ya ce"ilove u my momy".da sauri nima na rungumesa na ce"ilove u too my son".na haÉ—a Æ´aÆ´a dukansu na rungume,da sauri Bilal ya ce"a'ah ina little khairat ne"?.murmushi na yi sannan na ce"ah ai kasan tana wajen mutuniyarta hajiya kaka".

Ranar da daddare har shopping muka je cikin so da kulawar juna.

******

*after three month*

sosai na ke shan gyara yadda ya kamata,little khairat na da wata goma har ta fara tafiya ta yi kyaunta sosai,ga ta Æ´ar lukuta ga tsayi don tayo tsayin mahaifinta.

A wannan karon ma Ahmad commissioner of police baiyi sa'a ba,don tuni Yaya Aliyu ya shaida masa an mayar da aurenmu da yaya Bilal ya kuma gaya masa maƙasudin saki na da miji na ya yi.saboda tausayin yaya Bilal da yaji don kada ya rasa rayuwarsa.

Yaya Bilal ya danƙara wani gida me kyau da tsari part uku ne agidan wau harda part ɗin yaransa.ɗaya kuma ni dashi ɗaya kuma na baƙi.

Sosai aka kashe kuÉ—i wajen yin kayan É—aki don Yaya Bilal da kansa ya yimin komai hatta kayan kitchen duk shi ya yi,ya gyara sashen yaransa ya yi mugun kyau da tsari.

Da yamma aka rakoni tariya kusan Æ´an gidanmu duk sunxo,aka dinga yi mana fatan alkhairi,Hajiya kaka ta rungumeni tana ce wa"Allah sarki khairat insha Allah yanzu zaku zauna zama na har abadan,babu wani tsautsayi da zai gifta muku insha Allah".nima a hankali na buÉ—e bakina na ce"kaka babu abinda zai rabani da yaya Bilal sai mutuwa mutuwar ma da tana É—aukar mutum biyu da sai na ce ta É—aukemu tare."

Nan aka tintsire da dariya gwanin sha'awa,Rashida ma sai dariya take itama yanzu tana nan É—auke da cikinta
Wata biyar,yanzu kuma shekararta shida da aure,sai yanzu Allah ya kawo,maryam kuwa har mun saka mata suna uwar haihuwa don yanzu ma tana nan da cikinta har wata baƙwai.tana arba'in ta samu wani.

Dare ya yi sai ni kaÉ—ai da yara na,na shiga wanka na fito naji suna oyoyo dady,ita kuma Little khairat ta yi barci.daman ita da wuri take bacci Allah Allah na ke in ga yaya Bilal yau tun safe ban gansa ba.

Ta baya na shigo don haka banji shigowarsa ba sai kawai naji ya rungumeni ya ya yi sama dani ya ajjeni akan gado,ya koma farlo ya kunna musu catoon ya kukkule ko ina na gidan,sai masu gadi sojoji har guda biyar sannan ya dawo É—akin.

Na rufe hannaye na da tafukan hannuna kunya duk ta kamani daga ni sai tawul,murmushi ya yi ya faɗa wanka banɗaki sannan ya fito yana goge ƙwantaccen gashinsa,wanda yanzu ya ƙara kyau da tsantsi.

Ya saka jallabiyarsa sannan ya kalleni ya ce"mamynmu taso muyi sallah mu godewa Allah"murmushi kawai na yi don da haka ya ke kira na,wato mamynmu yadda yara na ke kirana.

Cikin jin kunyarsa na tashi na shiga ban ɗaki na saka rigar bacci me kyau sosai,ruwan pink wacce ta amshi fatata don ayanzu zama a iya kirana da fara,saboda yadda fatar tawa ta ƙara samun cigaba yadda take shan gyara sosai.

Bayan mun idar da sallah mukayi addu'o'i muka shafa ya ɗakko fresh milk da wata banƙararriyar kaza wacce girmanta ma kaɗai da maiƙonta zaisa kaci.sosai naci nasha madarar itama shima yasha daman yanzu na ya little khairat don da kanta ta ya ye kanta,sabawar da aka yi mata da madara,kuma yanzu kununta take sha mai matuƙar ƙarawa yaro lafiya.

Baki ɗaya ya ɗaukeni yana yawo dani kamar a indian film.Hmm ranar fa an yi ƙwanan farin ciki da ƙaunar juna tsakanin khairat da yayan nata Bilal uban ƴaƴanta.

Bayan wasu watanni,ayanzu yaya Bilal ya yi nasarar kama Alhaji Damas biyo bayan tonuwar asirinsa na ayuukan da ya ke yi,sannan su kansu manyan ƙasa sunyi amunna da hakan don suma abin ya shafi yaransu don Alhaji Damas ya ɓata musu yara da basu hodar iblis,ƙarshe har ta yi sanadin kashe ɗan gidan wani babban commisioner,ai kuwa ana kaishi kotu aka yanke masa zaman gidan yari na har abadan.sai dai ya mutu acen biyo bayan laifukan da ya yi wanda ba zai yiwu ya fito ba.
Chapter 62 · 0% Book details