← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 63

Sashe 24

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Miss green ce*
[23/09, 16:20] Miss Green🍀: 33🟫34

. . . .muna zuwa kai tsaye labour room aka kaita duk ta galabaita sosai,sa ƙer take nishi duk hankalinmu atashe muka zauna a reception ɗin bayan sun shigar da i'ta ɗakin ƴan haihuwa.

Na kalli yaya Aliyu wanda duk a ruɗe ya ke na ce"bro ka kira mutanen gida mana susan halin da ake ciki?".girgiza min kai kawai ya yi alamar baya buƙatar hakan.

Munfi awa biyu a zaune sannan likitab ta fito ta ce"ta kasa haihuwa da kanta suna tunanin ma operation za'ayi mata,likitan ta tambayi mijinta?yaya Aliyu ya bisu zuwa wani office.

Data na da ke kunne naji saƙonni na ta shigowa,sunan Rashida da na gani ne yasa ni duba saƙon na ta,anan na ke gaya mata abinda ke faruwa,na ce"Rashida ni naso ya faɗawa mutanen gida don baki gani ba wallahi ta sha wahala sosai".

"Ai gwara kada ya gaya musu,kin san dai yanzu a halin da ake ciki,ni bana son su ganki ma tunda su basu yarda da ƙaddara ba,kuma abinsu babu bincike,yanzu hajiya kaka ma tana cen rai a hannun Allah kuma nasan duk sanadin wannan abin ne".

wata irin muguwar faÉ—uwar gaba naji ina hawaye na ce"Rashida kina son ki ce min hajiya kaka ce tace babu lafiya?innalillahi yanzu a gida take ko a asibiti?kuma me ya janyo ciwon na ta?".

Duk alokaci ɗaya na rattabo mata waɗannan tambayoyin?ganin hankalina ya tashi sosai yasa ta fara ƙwantarmin da hankali sannan ta ce"khairat kada kice zakije gidanmu ki ƙelesu aƙwai lokacin zuwan,Hajiya kaka addu'arki take buƙata ba wai kuka ba,idan ki ka yi mata addu'ah ko a i'na take Allah zai amsa,don Allah khairat kada ki ɗaga hankalinki kinji don Allah".

Muna cikin wayar mijinta yaya Aliyu ya amshi wayar ya ce"khairat kada ki É—aga hankalinki babu abinda zai faru da hajiya kaka kinji".goge hawayen fuska ta na yi ina jin kaina ya yi min wani iri kamar zai tsage gida biyu.

A haka har yaya Aliyu ya dawo ya sameni ganina riƙe da kaina wanda ke barazanar rabewa gida biyu ya ce"khairat me ya ke damunki?kanki ne ke ciwo".?duk babu amsa don haka ya saka bayan hannunsa kan goshina yaji mugun zafi kamar wuta,yana cirw hannuna daga kan goshina sai yaji na tafi luuuuu.

Sosai ya tsorata ya fara girgiza ni yana kiran sunana,amman ina sai na yi sharaf a hannunsa,wani irin salati ya saka da gudu ya É—aukeni kamar Æ´ar tsana yana ihu yana kiran likitocin.

Da sauri likitocin suka bayyana,suka sakani a gadon marasa lafiya suka yi wani ɗako dani,yaya Aliyu fa ya zama kamar wani mahaukaci sabon kamu,ga matarsa tana labour ga ƙanwarsa babu lafiya,ya rasa awani bigire zai kira wannan ƙaddarar ya ɗaga hannayensa biyu sama yana ce wa"ya Allah ina roƙonka don tsarkin sunayenka tsarkaka Allah ubangiji ya bawa waɗannan bayin na ka lafiya ƙanwata da kuma matata.

Da ƙer likitoci suka dai-daita numfashi na amman ina wani stage wanda addu'ah kawai na ke buƙata,waya ta dana ajje i'ta ce ta fara ringing yaya Aliyu ya ɗauka yaga an saka mamana,shahada ya yi kawai ya ɗauka ya kara a kunnensa hawaye na fitowa daga cikin idanuwansa.

"Haba khairat me yasa ki ke ajje wayarki ne ki tafi wani wajen ina ta kiranki baki ɗaga ba"?.hankalin yaya Aliyu ne ya ƙara tashi ya ce"a'aaa mama ni ne Aliyu ne".
Gaban mama ne ya faÉ—i sosai ta ce"a'a to ina khairat É—in"?.

Kasa haɗa kalma ɗaya ya yi wacce mama baza ta gane komai ba,ya yi dauriya ya ce"eh daman na shigo ne yanzu ta ajjs wayar a farlo i'ta kuma tana maƙontanmu nan".

Ajiyar zuciya mama ta yi sannan ta ce"to ka aika mata da wayar inason muyi magana da ita ne"?.

Jikinsa ne ya yi sanyi sosai da jin abinda mahaifiyarsu ta faɗa bakinsa yana rawa ya ce"am daman mama ni yanzu zan koma da gaggawa ne na kai khadija asibiti labour take".ya faɗi hakan yana jin bai ƙyauta ba ƙaryar da ya yi wa mahaifiyar tasu.

"Ayya to Allah ya sauketa lafiya,to nima ina kan hanya insha Allah daman suprise na yi muku,ni da mama muna kan hanya".

Gabansa ne ya yi mummunar faɗuwa da ƙer ya aro dauriya suka yi sallama,ya leƙa khairat wadda aka saka mata oxigien saboda numfashinta da ya ke tafiya ba dai dai ba.

Wasu hawaye ne suka zubo masa yasa bayan hannunsa ya goge,ya samu kan wani benci ya zauna yana kallon kyakkyawar fuskar ƙanwarsa wadda ke kan screen ɗin wayarta,ya shafa fuskarta a hankali yana kuka ya ce"sister Allah ya baki lafiya,Allah ya tona asirin waɗannan mugayen mutunen waɗanda sukayi silar rashin lafiyarki,da kuma silar mutuwar auren mahafiyarmu."

fashewa da wani matsanancin kuka ya yi,yana jin zuciyarsa na yi masa zafi sosai,yana zaune yana kukan wata nurse ta fito cikin farin ciki ta ce"congrat munyi nasarar cirowa matarka babynta mace yanzu haka uwar na É—akin hutu,babyn kuma tana nan."

Bin nurse ɗin ya yi har ɗakin ya hango kyakkyawar babynsa sai wulga fararen hannayenta take fafare ƙal,kamanninta da khadija kamar ta yi ka ki komai iri ɗaya.

A hankali yaje ya É—auki Æ´arsa ya sumbaci goshinta sannan ya yi mata huÉ—uba,da sunan khairat wato Rahama.

Har yanzu khairat bata dawo dai dai ba,khadija kuwa tuni ta warware kamar ba wadda aka yi wa operation ba,Æ´an uwa har sun fara zuwa,sai dai ko sau É—aya Aliyu bai gaya musu rashin lafiyar khairat ba,ya tashi ya tafi wajen Æ´ar uwarsa,har yanzu bata san inda kanta ya ke ba.

Ya yi kuka har ya gaji,Salim da maher zuwansu kenan Aliyu ke shaida musu abinda ke faruwa da ƴar uwarsu,da gudu suka ɗunguma zuwa ɗakin da aka ƙwantar dani,dukkansu sun ruɗe sai kuka suke yaya Aliyu yana ta basu baki shima yana share hawayen da ya cika masa ƙwarmin idanuwansa.

Ko zuwa wajen khadijan basu yi ba suka zauna kowannensu ya riƙe hannun khairat suna ta tofa mata addu'o i.

*****

Aranar mama ta sauka ita da mahaifiyar ta,asibitin suka fara sauka kai tsaye ɗakin da khairat take ya ƙwatanta musu,kasa ƙarasa shigowa mama ta yi ta kasa magana bakinta sai rawa ya ke,a hankali ta ƙarasa wajen khairat ta rungume ƴarta a ƙirjinta tana wani irin kuka mai tsuma rai,yanzu ƴar ta ce ta dawo haka?baki ɗaya ta canja kamanni acikin awanni,yarinya ƙarama amman Allah ya jarabce ta da ƙalubale kala kala.

Mahaifiyar mama i'ta ke rarrashin mamanmu su yaya Salim É—in ma kuka suke sosai,sun kasa rarrashin mama don basu san ma me zasu ce mata ba,don suma neman masu rarrashin suke.

Tsakar dare na fara É—an motsa É—an ya tsana yaya Salim da ke gefena ya É—aga fuskarsa da sauri don bai san sanda bacci ma ya É—aukesa ba,mama da ke kan sallaya ta tashi da sauri sukayo kaina su duka,kakarmu,yaya Aliyu,mama,yaya Salim,maher.dukkansu suka rufu akaina suna yimin sannu.

Murna da farin ciki suka cika zuƙatan waɗannan family,hawaye na fitows daga fuska ta na ce"mama na".da sauri ta amsa tana shafa fuskata i'tama kuma tana hawayen.

Na fara samun sauƙi sosai don ƙwanana uku suka sallameni,ita ma anty khadija an sallame ta muka wuce gida baki ɗaya,sai dai tun a asibitin sai da yaya Aliyu da khadija suka hau sama suka faɗo,don muraran ta nuna bata son mu koma gidanta,yaya Aliyu ya ce ai kuwa bata isa ba sai dai ita tabar gidan don duk duniya bashi da kamar mahaifiyarsa da kuma ƙannansa musamnan khairat wacce take mace.

****

"Oga mun gano yarinyar da wannan ɗan matsiyaciyar ya ke so,mu kashe ta ne ko kuma mu barta?".ce war ɗaya daga cikin yaran Alhaji Damas,baƙi ƙirin dashi kamar zunubi.

Sassanyan lemo Alhaji Damas yasha sannan ya ce"ni bana taɓa yin abuna ba tare da ba yi wa mutum mai kankat ba,ba zaku kashe ta amman zaku yi mata ƙanin mutuwa ta yadda zai san ce wa ni dashi ba ɗaya bane,ta yaro ƙyau take ba ta ƙarko."ya faɗi hakan yana miƙewa tsaye yaran nasa suka bishi abaya.yana saƙa mummunar ƙuduri akan Jidda wacce ta kasance budurwa ga Bilal.

Zama na da mahaifiyata yasa yanzu na É—an fara sakin jikina,ga shi ko da wasa bata bari na in zauna ni kaÉ—ai saboda abinda likita ya ce kada a barni ni kaÉ—ai saboda b.p É—ina ya hau sosai,kuma duk ta silar tunanin.

Ranar suna Yaya Aliyu ya ce baza ayi suna ba,saboda yasan abinda hakan zai kawo,barka ma kawai da ƴan gidansu sukazo sai da akaso ayi faɗa,wai mama tazo ta zauna gidan ɗanta wai ta ƙwaso tsohuwarta inyamura sun taho tare.

Wannan magana ta tsayawa mama sosai,a take mutuwar aurenta ta dawo mata sabuwa fil,hawaye masu zafi suka zubo mata,lallai su mama iklima sun cuce amman babu komai kansu suka cuta don har awajen Allah ta fisu tunda dai ita bata taɓa cutar dasu ba.

****

Hajiya Inna ta kalli ƙawarta hajiya kaka ta ce"yanzu Ramatu haka zamu yi ta zama kina tare da wannan ciwon da aka rasa gane kansa,kullum abu ƙara gaba ya ke ni wallahi gani na ke ma kamar a mafarki".ta faɗi hakan cikin damuwa.

Mero da ke gefen Hajiya kaka tana É—an yi mata tausa,itama duk shirmenta yanzi ta ajjesa a gefe tunda hajiya kaka ba lafiya.

Alokacin su Baba Abdullahi suka shigo,Baba Bashir,Baba auwalu Baba ƙasim, suka zauna suna gaishe da hajiya inna ta amsa itama tana musu ya mai jiki,suka amsa mata da sauƙi sannan hajiya inna ta ce"a'ah lafiya na ganku ku dukanku kunsha manyan kaya haka?".

Baba Auwalu ne ya ce"ai shi yaya Abdullahi ba tare muka fita dashi ba,yanzu dai shigowa ne dai muka haÉ—u dashi to shine ya ce daman zaizo duba umma ne,amman mu mun kai kuÉ—in Bilal ne har da saka ranarsa."

"Ikon Allah to Allah ya sanya alkhairi".
Suka amsa da amin suna kallon mahaifiyar tasu wacce ke kallansu itama har zuciyarta tana jin daÉ—in ganin kan Æ´aÆ´anta a haÉ—e.

Bakinta ya fara motsi alamar tana son yin magana,mero ce ta lura da hakan ta ce"la kaka nason yin magana".ta faÉ—i hakan da farin ciki don ta damu da ciwon hajiya kaka.

A hankali Baba Ƙasim ya saka kunnensa dai-dai bakin Hajiya kaka,jin abinda take faɗa ne yasa ya kalli ƴan uwansa da sauri.
Chapter 24 · 0% Book details