← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 63

Sashe 1

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

[23/09, 16:15] Miss Green🍀: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!🥚*

📃Littafi na 1

By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*

_✨TEAM GAWURTATTU BIYAR 5✨_

-----------------------
Noticed⚠️Labari ne akan zazzafar Ƙiyayya,ban tausayi ban dariya,ban al'jabi,wa'zantarwa,nishaƊantarwa.

*Godiya:*
ina miƙa godiya ta ga dukkanin masoya na marubuta da kuma makaranta,ina ƙara muku godiya wajen nunamin kulawa da kuma soyayya Allah ya barmu tare amin.

*Sadaukarwa*

na sadaukar da wannan littafin ga mahaifiyata hajiya maryam moh da mahaifina engineer Bashir Abdullahi,Allah ya Ƙara musu lfy da nisan Ƙwana mai albarka.

*Doka⚠️⚠️⚠️:*

ban yadda a canzamin labarina ta kowacce irin siga ba,ba tare da an tuntuɓeni ba.

Ku kasance da gawurtattu 5 don jin yadda za ta kaya.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
-----------------------------------

HAJIYA KAKA POV

1🟨2

... . . .Kana shigowa tunda kan layinmu zaka san cewa ana wani mashahurin biki a layin,gidane kato sosai daga gani ko da ba'a gaya maka ba kasan cewa gida ne na family house farin fenti ne dashi me tsari,a ɓangare kusan sha uku ne agidan.

A babban hall ɗin na gidan ake sha'anin kamu,amaryar na hango taci adonta sosai cikin kayan fulani mai ƙyau da kuma tsari,ƴan matan amarya suna gefe suna selfie ana tsokanar amaryar.

"Khairat ki yi sauri ki fito,don Kin san ke kaɗai suke ta jira".wacce aka kira da khairat ta jiyo,wow na faɗa don yarinyar irin yarannan ce black beauty,ta juya eyes balls ɗinta da ɗan ƙaramin bakinta cikin shagwaɓa ta ce"to Mama ganinan fitowa".
Su Rashida ne suka shigo suna ce wa"don Allah Khairat ki fito kina ƙanwar ango amman kina yi wa mutane delay,ga ƙawayenmu nan duk sun zo mu kaɗai suke jira".
tsaki Iman taja sannan ta ce"Allah Rashida kina nema mana raini wajen wannan kucakar yarinyar shiyasa ni bana son haÉ—a harka da ita ko kaÉ—an,yanzu muna zuwa wajen wasu ma sai sun tambayemu anya kuwa wannan ba Æ´ar aiku ba ce?".
Wani irin baƙin ciki ne na ji ya tokaremin zuciyata amman babu yadda zanyi don Iman ba sa'a ta bace baya ga haka ma ni ba ma'abociyar yin faɗa bace.

Jikina ne duk ya yi sanyi don ganin irin kallon dasu Iman suke min da ƙannenta su Baby,na rasa me yasa suka tsaneni agidan tunda duj ba haka suke yi wa sauran ƙannen na su ba amman ni daga zagi sai hantara,kaf cikinsu mutum biyu ne suke sona daga Rashida sai Amira.Iman babanmu ɗaya dasu amman kuma sunfi kowa ƙyama ta.
A haka na zauna a tsararrun kujerun da aka ajje acikin gidan,ina juyawa na hango Hajiya Kaka wato kakarmu tasha gwaggwaronta harda jan baki,dariya na fara yi mata har ta yi gaba kuma sai ta dawo baya ta ce"ke kinji ja irar banza malik ne da Maryam su ki ke yiwa dariya don ni dai na fi ƙarfin uwarki da zaki sakani agaba kina yimin dariya yo me ye laifin wannan ƙwalliyar dana yi da zaki ringa yimin wannan dariya kamar kinga mahaukaciya?yo ko uwarki inyamura da take a uwar ango yau bata isa ta nuna min ƙyau ba,don haka ki shiga idona in rufe,shegiya ƴat baƙa kawai".
tana faɗar hakan ta tafi tana taunar goronta tana cigaba da mitarta don Kaka ta tsani ta yi ƙwalliya kace bata yi ƙyau ba.
Babu abinda yaban haushi a maganar kaka don daman idan da sabo mahaifiyata ta saba da wannan zagin da kuma toxarcin awajen kaka don ita arayuwarta ta Ƙi jinin mahaifiyata duk don a kasancewarta ba yaransu Ɗaya ba,uwa uba kuma gashi mahaifina ne Ya musuluntar da ita shiyasa gaba ki Ɗaya kaka ta tsani mama na,kullum cikin gori kuma abinda ke Ƙara bani haushi da kaka ko a gaban waye sai ta yi in dai Ƴan faƊan suka zo,yaya Aliyu shine Ɗan farin mama sai yaya Salim sai ni khairat sai auta afrah.

"ke kuma Khadija ranar auren na ki kika saka wannan ɗamammun kayan duk jikinki a waje?Ina shi sokon angon na ki ya ke ne?da ya barki kika saka wannan kayan?.Wannan tozarcin da Kaka ke yiwa Khadija a lasifiƙa ta taƙarƙare ta ke faɗa son ranta babu abinda ya shafeta.
Gaba ki ɗaya wajen shiru kowa ya yi don jin ƙatoɓarar da kaka ke yi,don yanzu kana magana masifar zata dawo kanka shiyasa ma kowa ya shafawa kansa lafiya don abin na ta sai ita ɗin.
Rafi'atu ce ta kalli kaka cikin fushi ta ce"Ke kaka shigar da kika yi a matsayinki na tsohuwa babu wanda ya ce miki komai sai ke ce zaki saka yaya ta a gaba da masifarki".
"inye a lallai Farouku ya baku daman cimin mutunci tunda gashi kina zagina a gaban uwarki bata iya magana ba saboda tana tsoronki to ko farouku ubanki bai isa ba,shegiya Æ´ar tsigi tsila".
ƙwashewa akayi sosai da dariyar dramar kaka don idan ka biye mata sai a ƙwana a tsaye.
Ana cikin hakan mukaji jiniya ta motoci ƙyawawa sun shigo cikin ƙaton gidanmu,ai kuwa sai Kaka ta fashe da kuka tana ce wa"To yau wai agidannan ni kuma kewa dariya tsabar rashin ta ido,ni dai wannan abin ya isheni ace ranar bikin jikata amman a nemi a kwashemin albarkar auren jikoki na to wallahi bazan yarda bari Soja Bilal ya dawo kowa sai ya ƙwashi kashinsa hannu".
Chapter 1 · 0% Book details