← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 63

Sashe 51

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki dinga yawaita karanta qur'ani saboda yana cire damuwa da saura Ƙunci na rayuwa,Allah ubangiji ya bamu dauriyar karanta qur'ani amin.

85. . . . . .86

. . . . .anyi suna lafiys taron ya tashi,wanka na shiga saboda tun safe sun hanani yin wankan,Haidar da baida haƙuri sai kuka ya ke,mama kuma da ƙanwarta sunje sashen Hajiya kaka ba daɗewa zasuyi ba.na ce"Allah haidar ka yi ka gama don ubanka ba yanxu na baka kasha ba?to shine kuma zaka dameni"?.na faɗi hakan ina wanka a banɗaki sosai na kejin daɗin ruwan zafin don ni gaskiya bana gudunsa ko kaɗan.ai kuwa nan da nan na fara komawa dai dai.

A guje ya shigo sashen namu daman kuma shigowar zai yi,ya duba yaga su mama basa nan faɗowa ɗakin kawau ya yi yaga Haidar sai uban kuka ya keci,yana ta saka hannunsa a baki,alamar tunwa ya keji,su kuwa sauean baccinsu suke amman ganin haidar na kuka suma sai suka fara,haka suke min duk abinda ɗaya ya yi to ɗaya ma sai ya yi,haka suke da daddare su hanani bacci sai tsotso,da rana ne na ke samun lokacin bacci don ko da yaushe suna hannun mama ta riƙesu insha bacci na.

jin zuciyarsa ya yi tana mugun zafi,to ina suka yi suka bar masa yaransa?ya É—aukesa yana rarrashi tunda su nasu bai kai nashi ba,ya kira Nusaiba da Amira ya ce su É—akko masa su duka.ai kuwa haka aka yi suka É—aukesu suka fita dasu.

Shima ya fita daga ɗakin ya buɗe mota ya shiga da haidar a hannunsa Amira,da Nusaiba sai ƴar baba ƙasim Suwaiba,ya ce su shiga bayan motar,suka kuwa zzazauna sai asibiti,yana zuwa ya kira likitan da ya yi masa magana kan ingantacciyar madarar da za'a dinga bawa yaransa,saboda ya lura suna shan yunwa,don wai yaga har sai an rarrashi Khairat sannsn take basu mama susha,abin nan yana bashi haushi don dai babu yadda zai yine,don ko ƙurarsa Khairat bata kalla.

Ina fitowa daga wanka lokacin su mama suka shigo har da hajiya kaka,da sauri na kalli inda na ajje yarana naga babu su,tuni na fara kuka ina ce wa"na shiga uku na ni khairat waye ya shigo ya É—aukesu?".na faÉ—i hakan ina muxurai ina jin zuciyats kamar zata fito saboda azaba.

Hajiya kaka ta ce"a'ah to waye kuwa zai ɗaukesu sai dai ubansu,wataƙil kin barsu suna kuka ne shiyasa,jiya ma wallahi ya kawomin ƙararki,bakya kula masa da yaransa,kinga kuwa bazaku shirya ba".da sauri na ce"o ho shine ya samu damar zuwa ya ɗaukemin su?ya sakani cikin tashin hankali saboda shi damuwarsu suna kuka ko?to duk ranar dana bar masa waje na ce yazo ya kula dasu iyawa zai yi?amman duk a haka bai gani ba shinr yazo ya ɗaukesu ko?to babu laifin haka.xan bar masa yaransa ina shikkenan ko?sai ya samar musu uwarda zata kula dasu,tunda ni ya raina nawa".

Na faɗi hakan ina fashewa da kuka Hajiya kaka ta ce"haba khairat ya zaki ce zaki bar masa yara?ya yi yaya dasu?karma ki faɗi wannan maganar wani yaji bayan mu."da sauri na ce"ok idan kun san haka me yasa zaku barsa ya tafimin da yara na?shi ya yi min naƙudarsu?ko ya fini sonsu ne?da zai ɗaikesu?to gasu nan na bar masa,ya ƙwaɗanta ya cinye duka".

Na faɗi hakan ina ƙara fashewa da kuka,ita mama ma ta rasa me xata cemin,don wannan faɗan bai kamatz ta shga ba,itama fa har yanzu haushin Bilal take ji,na sakin rashin mutuncin da ya yiwa ƴarta.ƙanwar mama na ce tazo inda na ke zauna ta dafa kafaɗu na ta ce"yi haƙuri khairat kinji?son yaranne suka yi masa yawa,su maza fa haka suke kai zaka yi naƙudar yaranka amman kuma sai su fika sonsu,harma awani lokacin su nuna maka sunfi ka sonsu.don haka wannan ba wani abin mamaki bane tunda daman haka halinsu ya ke."

Ko da ya dawo wucewa dasu ya yi ɓangaren mahaifiyarsa,ya zauna ransa a ɓace ya ce"wallahi hajiya bansan me ke damun khairat ba?don tana ƙina kuma sai ya shafi yara na?meye laifinsu anan?shin sune suka yi mata laifi ko ni?,to wallahi na amshe yara na,taje ta yi rayuwarta tunda haka ta zaɓa".

Tunda ya fara magana Hajiya Ruƙayya bata ce komai ba,sai cen ta ce"Bilal ka taɓa ganin uwar da ta haifi yaranta taƙi su?kai ma kasan tana sonsu kuma har yanzu khairat yarinya ce. Da sauran yarinta akanta,kai da ka ke lallaɓawa kuma ina kai ina zuciya?don Allah ka rage wannan fushin,idan kuma ba haka ba ya sakaka nadama.saurin fushi yana haifar da dana sani,babu laifi idan ka zaunar da ita ka yi mata nasiha akan yadda zata kula maka da yaranka,ta lallashi da luma na amman ba ta faɗa ba,kaga ashe gyaran da ka keson yi sai ya ƙara rugujewa."

Shiru ya yi kawai yana kallon idon iman wacce ke hannunsa tana ta wawure wawure tana neman abincinta,ya ce"Hajiya wallahi son da na kewa mahaifiyarsu ya yi yawa,shiyasa suma ya shafesu duk wanda zai wulaƙanta min su to tabbas ni ya wulaƙanta ba suba,don haka dole ne inyi mata faɗa ko babu komai ai ni yayanta ne."ya faɗi hakan cikin fushi.

Sosai Hajiya Ruƙayya ta lallashesa har ya sakko,arayuwar duniya babu wanda yafi sanin kan yaro irin uwa,tun yana jariri take gane abinta,tun Bilal yana ƙarami ta sanshi ƙwarai da mita,ko mama ta hanashi da wuri to sai ya yi ta mita kafin ya amsa,shiyasa tun daga nan ta gane Bilal mutum ne me mita,amman bashi da riƙo ko kaɗan.

Ina zaune ina xaune na yi shiru har yanzu tawul ne ajikina wanda na fito da shi daga wanka,na zabga uban ta gumi sai gasu sun shigo da yaran su Nusaiba ne suka fara shigowa,da sauri na tashi na karɓi Ahmad wanda har ya fara kuka na rungumesa a ƙirjina,bai shigo ba sai ya aiko da yaran,Hajiya Ruƙayya ta zauna abakin gadon duk sai kunyarta ta isheni,bayan mungaisa ne ta ce"Khairat da farko dai zan baki haƙuri ne akan abinda Bilal ya yi na ɗebi miki yara,amman ki yi haƙuri badon saboda ɗanane shiba zan faɗa miki kema baki da gaskiya,ki daina barinsu suna kuka don Allah idan zaki shiga wanka ki samu wani ya zauna dasu kinji?saboda irin haka fa har shaiɗanu suna shigar yara,sai kiga an rasa gane kan matsala,kuma alhali mu iyaye mu ke da alhakin kula da yaranmu,don Allah ki kiyaye kinji"?.

Na ɗaga mata kai kawai tsabar kunyarta na kasa basu mama har sai da ta fita.hannuna na rawa na ɗakko Haidar da Iman na fara shayar dasu,ai kuwa zuƙar da sukemin ta yimin yawa har ƙwaƙwalwata sai da naji zafin tsotsar da suke min,na cije leɓe ina yarfe hannu.

Yana tsaye jikin ƙofa yana ta kallo na,sai kuma yaji tausayina duk ya kamashi,ganin yadda na ruɗe har na rame daga ɗaukesu tabbas kenan har yanzu khairat na sonshi tunda tana son ƴaƴansa.sai da na bari suka ƙoshi dukansu sannan na sakasu a kafaɗa ta suka yi gyatsa sannan na ƙwantar dasu ina tofa musu addu'ah tuni bacci ya ɗebesu,na yi murmushi na manna musu kiss a goshinsu ina shafa sajensu wanda ya ƙwanta luf irin na mahaifinsu,tuni na tuno dashi amman kuma madadin so sai naji tsanarsa ta ƙara samun wajen zama.

Na tashi ina cire kaya na kawai sai ya shigo ɗakin,ina juyowa na ganshi tsaye akaina tuni na runtuma da gudu na ɓuya abayan sif,sai kuwa ya ce"dama kinyi fitowarki don na riga dana ga komai tun ma ba yanzu ba".ya faɗi hakan yana hawa kan gadon shima yana binsu da addu'ah yana wasa da ɗan hannayensu gwanin sha'awa.

Sosai na keji da tsiwa ta na ce"don Allah mlm ka fita tun kafin wallahi in tara maka mutane".ina faÉ—ar haksn har hawaye na ke,sosai abin ya bashi dariya sannan ya ce"ok to yi ihun mana?ki tara mutanen kiga idan zan tsorata".?ganin bazai tashi bane yasa na yi saurin tashi na fara saka kayana.

Ya yi murmushi ya matso inda na ke ya ce,da sauri na matsa gefe na ce"Allah ka matso inda na ke Allah ya isa ban yafe ba".da sauri ya matsa gefe ya ce"khairat ni ki kewa Allah ya isa"?.da sauri na É—aga masa kaina alamar eh dashi na ke.

Bai ƙara magana ba ya fita fuuu kamar kububuwa ni kuwa azuciyata na ce.tafi nono fari daman ni haka na keso.

******

Madarar daya siyo ya aiko da ita,ina haÉ—a musu da ita yara suka yi manya dasu tubarkalla.

Tunda Baba na yasan auren mama ya mutu,sai yaƙi yarda ta koma Garinsu ya dinga aiko mata mutane akan ta yi haƙuri ta komawa gidanshi,sai da ƙer ta yadda sai da muka taru dukkanmu har da maher ƙaraminmu,muka saka mata kuka tausayinmu yasa ta aminci.

Aka mayar da aurensu,tuni aka ƙara gyara ɓangarenmu aka ƙara fitarwa da mama babban farlo da ƙurya biyu.ya yi kyau sosai su mama iklima kuwa rayuwa ta garasu inda ayanzu duk sunyi aure,sai dai duk ranar da yaransu suka je wajensu to fa da kuka suke dawowa,har tausayi suke bani.

Nadiya ma aure ya mutu ta dawo gida,don Yaya Aliyu ya gano har yanzu bata daina lesbian ba,ai kuwa ya sake ta saki É—aya.tuni ta lalace ra rame sosai yanzu idan ka ganta sai ta baka tausayi.

Nadiya me izza da ƙwalisa da rashin kunya,amman yanzu duk babu wannan har ɗakina take zuwa musha hira don tuni ta nemi yafiyarmu nida mama tana kuka.

Rashida ce yanzu agidan,har yanzu bayan ɓarin da ta yi bata sake samun ciki ba,Maryam ma dai haka don ita kamar da matsalar jinnu ma.amman dai an dage da magani.

*After 2 years*

A kullum Bilal hankalinsa na kan Khairat duk zuwan da zaiyi da magiya da naci,don sai ya ɓuge da ɗibarsu haidar wai duk don in dawo masa amman ko kallon ƙurarsa bana yi.

Shi kuwa Ahmad commisioner of police ya yi naci har ya gaji na ce bazan auresa ko don matarsa Xuhra,don tun da na haihu bata zo ba,kuma ko a skull yanzu ta daina kulani tunda ya bata labarin ni tsohuwar budurwarsa ce,shikkenan ta ƙaurace min ko aji bata shiga duk inda tasan ina nan.sosai abin ya bani mamaki sai dai ba abin mamaki bane don daman kushinmu na mata ya gaji haka.
Chapter 51 · 0% Book details