← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 63

Sashe 12

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan taro ya tashi ko wa da abinda ya ke saƙawa acikin zuciyarsa,Rashid ta kalli Khairat cikin tsokana ta ce"to ikon Allah yanzu fa agidannan mune muka zana gwauraye don kowa da mijinsa".nima ƴar dariyar na yi sannan na ce"gaskiya wannan haɗin ya yi min sosai wallahi kinga ni daman su Nadiya na ke tunanin amman kinga yanzu rayuwarsu za ta inganta kuma yaya Aliyu mutunne mai mutunci da karramawa."Rashida ta yi min sannan ta ce"wai kina nufin daman Nadiya da Aliyu aka haɗa?".saurin ɗaga mata kai na yi alamar eh.hawaye naga yana fitowa a idanuwan Rashida na ce"a'ah me ya faru kuma"?.

ruƙo hannuwa na ta yi duka biyu muka shiga ɗan lungu da ke manne dana kaka,a hankali cikin siririyar murya ta ce"Khairat muna soyayya da yaya Aliyu fa?".da sauri naja ɗan baya na zaro idanuwa na waje alamar tsoro.
tausayi ta bani sosai a zuciyata kuma ina tuna girman zurfin cikin ita Rashidan da ko ni ban taɓa sani ba,a hankali na ce"haba Rashida gaskiya kinyi kuskure ba kaɗan ba wallahi,ko ni baki taɓa gayawa ba?ballan tana ma in taimaka miki ta wani ɓangaren,kin san yanzu kan iyayenmu a haɗe ya ke kada azo ayi abinda kansu zai rabe,kin san kawu Auwalu matarsa ta fi ƙarfinsa sai yadda ta yi dashi gashi kuma basa shiri da Mamanku kinga hakan kamar zai janyo wata matsala fa"?.

"Na sani Khairat amman wallahi mundaɗe muna soyayyarmu daman munƙi bayyanawa ne sai har mun gama makaranta.

Kasa ce wa komai na yi cen dai na ruƙo hannuwanta duka biyu na ce"Rashida aduk halin da zaki shiga bazan taɓa gudunki ba ina nan tare da ke,tun daga kan wasan ƙasa har zuwa yanzu munanan tare babu wani mahaluƙin da ya taɓa shiga tsakaninmu don haka kinga yanzuma dole in tsaya kaida ƙafa inga wannan al'amarin ya dai daita".

Kamar daga sama mukaji ana ce wa"ya dai dai ta ma ai".muryar kaka mukaji ta nufo inda muke ta ce"munafukar yarinya au ke yanzu daman kina son gadanga ƙusar yaƙi kika ƙi magana sai yanzu".?ƙada da kai Rashida ta yi tana zubarda hawaye tausayinta ya ɗarsu a zuciyar Hajiya kaka ta ruƙo hannun Rashida suka nufo ɗakin kaka Yaya Aliyu yana zaune akan kujerar kaka wadda aka zuba mata ƙwanannan kansa a ƙasa idanuwansa sunyi jawur kamar harda kayan aikinsa ma ajikinsa ba tare daya ciresu ba,kayan aikin likita yaya Aliyu likita ne na ganycology ma'ana likitan mata.
Yana ganin Rashida ta shigo ya tashi da sauri yana kallonta jikinsa duj babu ƙwari ya zauna yana ce wa"Rashida kinga yanzu abinda shirin mu ya ja mana,kin fiya zurfin ciki Rashida kin hanani gayawa kowa saboda sai kin gama makaranta za'a sani how comes hakan ya faru."ya faɗi hakan yana kallon Rashida.mu dai duk muna tsaye mun kasa zama sai da kaka ta ce"to aadarawan sarki ku zauna kun wani tsayamin akai".zama mukayi a kan capet ɗin ɗakinta ba ta ce komai ba ta janyo wayarta ta ce"ke Abin cikin ƙwai kirawo min abdullahi dai malik dai auwalu duk ki kirawomin su alokaci ɗaya."
Gabana yana faɗuwa na fara kiran Babana faɗa masa,sannan na kirawo su suma duk akayi sa'a suna cikin gidan dawowarsu kenan,su dukansu ta tarasu sannan ta ce"kun gane min waɗan cen ja'iran yaran".ta nuna su Rashida da Aliyu dukansu sunkuyar da kansu sukayi don kunya sannan kaka ta ɗora da cewa to kada ku ɗoramin laifi don nima ban sani ba?sai yanzu".duk iyayen nasu su suke kallo sun kasa gane inda maganar mahaifiyartasu ya dosa.Baba Auwalu ya ce"to umma me kuma ya ƙara faruwa kin sakamu acikin duhu?".

"Duk yanzu zaku fito daga cikin baƙin gawayi ma ku ƙara tsundumawa cikin baƙin gawayin tsabar na sakaku acikin duhun?to waɗannan yara Rashidatu da Aliyu ashe soyayya suke basu taɓa barin wani ya sani ba sai yanzu ne fa ni na kama su".

ni da bama dani ake ba kunya kamar ta kasheni dukanmu mu ukun muka sunkuyar da kai,ana cikin hakan Baba ya ce"shin da gaske kuna soyayya?".da sauri kaka ta ce"ikon Allah ka jini da malik au tambayarsu ma ka ke da gaske ne ko?na sambaɗa ƙaryar dana saba muku ko?to ko ubanku kafin ya mutu bai taɓa ce min na yi masa ƙarya ba sai kai soja marnari daga ne sa".ganin mahaifiyar ta su za ta sauka daga bigeren da suke ciki ya ce"ki yi haƙuri umma ba fa nufina kenan ba kin san yaran yanxu suna iya canja ra'ayi a ko da yaushe".ya faɗi hakan yana kallon mahaifiyar ta su.

"Au to na ɗauka ƙaryata ni xaka yi ai ga Abin cikin ƙwai nan tasan komai sai ta faɗa maka,shegiya baƙar banza ai duk tare da ita aka ɓoye komai tunda sun iya munafunci".da sauri na ɗago kaina ina kallon kaka ta ce"daina kallona da idanuwanki gwala-gwala irin ns baba tunde inyamurin kakanki".da sauri na ɗauke idona don nasan kaka tana cikin fushine,arayuwarta ta tsani abinda zai taɓa mata jikoki sai kaga duk hankalinta ya tashi.
"na ce daku na ke magana".cikin tsawa Babana ya yi maganar don shi aƙwaishi da zuciya Aliyu ne ya buɗe baki da ƙer ya cire farin glass ɗinsa irin na likitoci ya ajjesa acikin ma'ajiyarsa sannan ya ce"ƙwai Baba da gaske ne muna soyayya tun 2 years da ta wuce".

"amman Aliyu anyi lusari wallahi yanzu kana son yarinya amman shine ka yi shiru har sai da aka fitar maka da mata?to yanzu yaya ka ke so muyi?so ka ke ka raba mana zumunci ko?to wallahi baka isa ba".inji Baba Auwalu wanda ya harzuƙa sosai don shi arayuwarsa baya son raini ko kaɗan.

"To ni fa bawai na tara kune anan kuyi min wani Æ´an faÉ—a ce faÉ—a ce ba,Aliyu dai ya tabbata mata 2 zai aura shikkenan sai ku tashi acigaba da shirye shirye,kuma duk shegiyar matarda ta canza muku karatun dana yi to wallahi sai ta fece garinsu".tana faÉ—ar hakan ta tashi ta shige uwar É—akinta.

Sim sim ni da Rashida muka bita kawunanmu a ƙasa,shima Aliyun zai tashi suka zaunar dashi sukayi masa nasiha sosai sannan suka cigaba da hirar yadda abubuwan zasu tafi na biki.to Aliyu babu laifi yana da kuɗinsa doj yana samun kuɗi na albashinsa sa sannan yana sana'ar siyarda motoci daga cotonou zuwa nigeria wannan kuma shi da yaya Bilal suke don daman a manyan gidan daga Yaya Mohd sai Yaya Bilal sai Yaya Aliyu,su biyun duk rana ɗaya aka haifesu don haka tare suka taso babu abinda suke banbantawa,ko shawara ce sai Aliyu ya tambayi Bilal sannan ya ke jin daɗi,ammanfa akan zancen son ƙanwarsa ya kasa gaya masa don kunyarsa ma yanxu ya keji don ya zama suruki.
Jin wannan maganar ba ƙaramin hargitsi ya haɗa ba,don mama mairo mahaifiyar yaya Aliyu tuburewa ta yi ita fa ɗanta bazai auri ƴar maƙiyiyarta ba,da ya ke macece tsayayyiya sai gashi tana neman canzawa Baba Aliyu tunani,ai kuwa kaka ta kirasu ta sillesu tsaf ta kuma ce"ke Mero sanda za'a aureki ba tuwo tuwo ki ke a bakin titi ba?".sai kuwa mero ta bazo idanuwa waje kunya duk ta isheta,ta sunkuyar da kai tana jerowa tsohuwar Allah ya i'sa.

"Oho ke ban hana a aureki ba sai ni zaki hana a auri jikata ko?ta haÉ—iyi zuciya ta mutu ko?to wallahi baki isa ba aure kamar an É—aurashi ne,don haka ki fita daga idanuwa na in rufe duk abubuwan da ki ke bana son yin magana ne don kada in zama uwar banza don haka kada ki yadda ki shigo gona ta don haka ki ki yaye duk sanda kika cikani sai na faÉ—awa kowa sirrinki".

da sauri mama mero ta ƙwalalo idanuwanta don tasan kaka za ta iya faɗa to tabbas ta tarwatsa mata rayuwarta shikkenan ƙarshenta yazo,da sauri ta ce"Allah yaja daran Hajiya kaka insha Allah haksn bazai ƙara faruwa ba."harararta kaka ta yi sannan ta ce to ass- ass na sallami mutum ya tashi ya bani waje don nan ba filin tuƙa tuwo ba ne ehe".

da sauri ta yi fit ta fita don ba ta son ƙara jin maganar da kaka za ta faɗa don yanzun ma ta gama faɗin abubuwa marasa ƙyau akanta.

Tana tashi kaka ta kalli Baba Auwalu ta ce"to sallamamme ni kam yanzu na sallamawa mero kai dai ka tashi ka bita don na ga jikinka har rawa ya ke ka bita".

Sunkuyar da kansa ya yi sannan ya ce"umma ki yi haƙuri daman wai ina tausayawa masa ne riƙe mata biyu a ƙananun shekarunsa".ya faɗi hakan kansa aƙasa.

"Oh ni Ramatu idan baka mutu ba zaka yi kallo wai ni Auwalu ji ka ke na manta ne yanzu fa matanka biyu kuma kana son ƙaro ta uku ita mero kana aurenta ko shekara bata yi ba ka yi mata kishiya ba?babu yadda banyi ba akan kada ka ƙara amman ka ƙara saboda ka gano shuwa duk ka gigice to ka fita idanuwa na wallahi,daman kai Auwalu duk ƴaƴana kai ne sallamamme akan mata Kamar wani zakara,to dai Allah ya tsari Aliyu da haka".

Sunkuyar da kai ya yi sannan ya ce"to umma na tuba ki yafe min insha Allah hakan ba za ta ƙara faruwa ba".da hannu ta nuna masa ƙofa ya fita a hanyar fitowarsa ne yaci karo da hajiya Inna aminiyar Hajiya kaka gaisheta ya yi cikin mutunci sannan ya tafi.
Bayan sun gaisa ne Hajiya Inna ta ce"Ramatu wai me je faruwa ne acikin gidannan na ga duk yaran suna wani É—a-ri-É—a-ri da mutum suna wani sunkuyar da kai."

"ah to ai dole ki gansu a haka tunda gidan mutuwa kika zo?wai fa akan wannan haɗa wannan alkhairin da ki ka bani shawara ne to shine fa suke ta fushi dani,yanzu haka duk basa zuwa ɓangare na Abin cikin ƙwai ce kawai take zuwa sai Bilal daman kaf jikokina yasin ba fi sonsu don basa guduna akowani hali".

"to Ramatu ai dole daman ki gansu a haka amman daga baya komai zai gyaru insha Allah suna yin auren idan suka É—an É—ana zumar aure to fa zaki bani labarin irin yadda zasu kasance".nan dai suka cigaba da hirarsu gwani sha'awa.

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
Chapter 12 · 0% Book details