← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 63

Sashe 5

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da Ƙasim ya gaji da jiran Hajiya Kaka sai ga shi ya biyota sashenmu ya tarar ana dirama,gurin zama kawai ya nema ya zauna don yasan wannan tsayuwar da kakar ta sa ta yi sai akai dare ana abu ɗaya,don kaka bata san ta yi abu ɗaya ta yi shiru ba.

Tun ana abun tsakanin ɓangarenmu har ƴan sauran ɓangaren sashen suka fara tururuwar shugowa har ana ƴan rige rige.

Umma ce kawai bata shigoba mahaifiyar Bilal don dawowarta daga makaranta kenan,don ita ce headmaster a makarantar Æ´an matan da take.
Kowa ya baza idanu ya ji abinda zai faru,masu dariya na yi masu jin haushi suma ba a barsu a baya ba.

"Wallahi yau bazan yarda ba,bari Malik ɗin yaxo idanma shine ya ɗaure muku gindin dukan jikata yau zanji,wannan wani irin rashin imanine kamar an samu ƙato,duk cikinku wa ubanta ya taɓa duka?ku gaya min tambayarku na ke"?.

babu mai bawa Hajiya Kaka amsa,don idan kaka na abinta kowa shiru ya ke idan ba haka ba sai a dawo kansa.

Ƙasim kaka ta kalla ta ce"kai uban son gulma kirawo min ɗana Malik,yanzu duk abinda ya ke ya dawo gida don bazan yarda ba wallahi sai an karɓarwa jikata ƴanci don har hukuma yau sai munje wallahi".

ai suna jin maganar hukuma suka tsugunna har ƙasa suna ba ta haƙuri amman fir Kaka ta ce bata san zance ba".

yana ɗauka kaka ta warce wayar ta ce"kai Malik uwarka ce ke magana duk abinda ka ke ka yi hanzarin dawowa gida,don wallahi yau sai dai ka zaɓa ko ni ko ƴan iskan matanka Iklima da Xeenatu".

yana jin hakan ya ce"ganinan zuwa Umma".ƙit ta kashe wayar ta jehowa Ƙasim,ya yi saurin cafkewa don sauran ƙiris wayar tasha ƙasa.

Mintina kaɗan sai ga shi don daman ba nisa ya yi ba,suna meeting ne a gidan gomnati,tunda ya sauka a mota ya hango ɓangaren na su a cike an ɗaga labule yasan Hajiya Kaka ce da wannan aikin don in dai za ta yi faɗanta ɗaga labule take.

Yana zuwa kowa ya fita don suna matuƙar jin tsoronsa don sam bashi da wasa ko kaɗan balle wargi soja sak a haka ma idan ya juya sai ka ɗauka Bilal ne don suna matuƙar kama da Bilal ɗin.

A hankali ya zauna sannan ya gaida kaka amman ko amsawa bata yi ba ta ce"yo ta ina zan amsa maka ana neman kashe min jikata,janyo ni ta yi ta gurfanar gaban Abba gabana sai faɗuwa ya ke don muna matuƙar jin tsoronsa,duk da wataran yana sakar mana fuska.

Abba ya kalleni sosai ya kalli kuncina ya kalli kaka da mutanen wajen ya ce"waye ya yi mata wannan bin cikinku"?.

Dukkansu har Mamana sai da hankalinta ya tashi don cikin kakkausar murya ya yi maganar,idanuwansa sun kaÉ—a sunyi jawur jin babu wanda ya basa amsa sai ya ce"babu wanda zaiyi magana acikinku?tunda duk kun rainani ko?".

"yo ta yaya za'ayi suyi magana munafukan banza da wofi kawai,to idan baza ku faɗa ba ni bari in faɗa ka ga wannan ƴar me tallan ƙosan da waccen almurar ƴar fillon dajin suka haɗu suka mari Khairat a fuska ka ga yanzu sun janyo maka asara don ko babu komai ka kashe kuɗi a asibiti."

"umma babu sisin kobon dazan kashe wallahi,su dai da suka aikata abinda sukayi su zasu kaita asibiti sannan kuma daga yau zan kafa mummunan sharaÉ—i akan cin zarafin Khairat da kuke don wallahi bazan lamunta ba,khairat ta shi ku tafi Asibiti ke da Kaka dasu azzaluman."

sai Hajiya Kaka ta riƙe baki ta ce"A ah wallahi bazani asibiti ba yinin ƴar gidan gaji zanje daman Ƙasimu zai kaini alfarma ɗaya zanyi musu su shigo motar Ƙasimu ya saukesu a kan hanya amman ni baxanje ba,ai sai jikinsu ya gaya musu wallahi don har gado ya kamata a bawa Khairat don wannan zaluncin ya yi yawa,sai ka ce ja ka ni dai wallahi maganar nan ma bata mutu ba dole aje wajen hukuma don su ƙarɓawa yarinya ƴancinta ko wacce muguwa ta ƙwana a cell taji idan da daɗi mugunta."

shiru Baba ya yi sannan ya ce"kaka ki yi haƙuri abar maganar cell ni kenan bani da right agidana dole subi dokokin da zan sharɗanta musu don na isa da gidana".

"ka ga Malik ni fa na gaji da wannan muguntar idan kai abin baya damunka to ni billahil azim yana damuna,don nasan zafin mari don rabona da a mareni tun ubanka yana zafi zafinsa ya mareni ranar kuwa baiyi baccin ƙwarai ba,don sai da na azabtarsa nima,don wallahi fuska itace babbar kadara a jikin ɗan adam."

kunya ta ishi malik amman ya rasa me zaice haka dai ya lallaɓa Kaka muka tafi asibitin,ai kuwa ce wa ta yi a bani gado atake likita ya ce to aka rubuta sannan aka bani magani harda allura sannan bacci ya ƙwasheni,Kaka saboda mugunta asibiti me mugun tsada ta ce Ƙasimu ya kaimu ai kuwa dai me tsadarne don tashin farko dubu talatin aka nema kuma duk ƙwana ɗaya dubu talatin kuma ce wa ta yi ƙwana uku zanyi sai na warke tsaf sannan zan koma,kuma ta ce su zasuyi jinya ta,kuma duk abinda ya samu jikarta sune a rubuta a ajje,bayan wannan kuma idan muka dawo gida sai sun bani tarar kuɗi har na dubu hamsin.

Sosai abin ya bawa kowa mamakin jin furucin Kaka,Æ´an gulma ana ta zuwa dubani Kaka kuwa duk wanda yazo babu abin dubiya sai ta sillesa tsaf,Yaya Bilal baya nan tun ranar da abin ya faru sai yau ya dawo ake faÆŠa masa duk abinda ya faru.
Ransa ne ya yi mugun Ɓaci nan da nan ya wuce sashen kaka alokacin ta fito daga wanka kenan tana duba mudubi tana rangaƊa Ƙwallinta,sai ga shi ya taho kamar daga sama,tsabar tsoro sai da kaka ta yarda mishiyin Ƙwallin tana kallon bilal Ɗin ta ce"oh ni Ƴatsu soja me ye xaka shigomin Ɗaki babu sallama kamar wani na'adaren sarki".?

"ba gwara ba'adaran sarkin ba,kawai don an mari yarinya shikkenan sai ki ce wai sai an biyata diyya kamar waÉ—anda sukayi wani kisa,haba kaka kidanga abu mana da sense amman kawai yarinya ta yi ta haÉ—aki da jama'ah kina ci musu mutunci suma fa Æ´aÆ´ane kamar na ki Æ´aÆ´an su ma kuma iyayensu suna sonsu. . ."

Tun kafin ya ƙarasa cikin faɗa ta ce"to ita Khairat ɗin sai aka ce maka daga sama ta danno ta fito,itama ai uwarta da ubanta na sonta,wallahi soja bazan yarda suci banza ba kowacce baƙar muguwa sai ta gane kurenta don wallahi bazan yarda ba ehe idan ma sun turo kane don ka yimin rashin mutunci ni ba zan yarda ba,kaima da ka yimin rashin kunyar Ruƙayya uwarka ka yi wa ba niba,don ni ba sallamammiya ba ce".

tana faɗar hakan ta yi ficewarta tana ce wa"yanzu ma asibitin zan tafi don yau za a sallamota kuma a sibitin zasu bani kuɗin in karɓe in bawa yarinya ta yi shagalin gabanta,idan kuma aƙwai wanda zai karɓe bismillah ga ni gashi".

tafiyarta ta yi ta barshi a wajen ya ce aransa lallai tsohuwarnan yau za ta san ta taɓa soja ba dai asibiti za ta ba,mu zuba mu gani.

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

*YADDA AKE BUÆŠE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka É—akko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form É—in kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email É—inki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buÉ—e account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*miss green ce*
[23/09, 16:15] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_

📃Littafi na 1

By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*

*GAWURTATTU 5*
---------------------
*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
---------------

*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
-------------

*Sirrinmu*

manzon Allah(S.A.W)ya hanemu da saka turare idan zamu tafi don yaÉ—a xinar idone,don haka mu kiyaye.
------------------------

7🟩8

. . . .Tun ka fin ta ƙarasa bakin gate ɗin taga duk babu motocin gidan,ta ce"oh mu dai Allah ya tsaremu da mugayen mata yanzu tsabar baƙin ciku don zanje nemawa jikata ƴanci shine za a ƙwashe motocin gidan a ɓoye."

Ammar ta hango ɗan gidan Baba ƙasim me bin baba auwalu,da sauri ya fara neman wajen Ɓuya tunda yasan halin kakar ta su,da sauri ta ce"Zo nan Ammaru ko Ƙasimu ubanka bai isa ina masa magana ya ƙi zuwa ba,saboda uwarka ƴar borno tasha ruwan babur na baƙin hali shine ina magana zaka ɓoye?".

ɗan shafa kansa ya yi sannan ya ce"haba kaka wane ni na'isa kina magana in ɓuya,ai ban isa ba yanzu dai me ki ke so?".

"ayyo to na ɗauka rashin mutuncinne ta motsa tunda kasha nonon babur ƴan maiduguri".kallon kakar ta sa ya yi sannan ya ce"wai ke kaka me yasa kullum sai kin zagar mana iyaye sannan ki ke jin daɗi ne?don Allah ki daina yadda ki keson ƴaƴanki muma haka mukeson na mu".ta ɓe baki Hajiya kaka ta yi sannan ta ce"to rasai ai dole inyi zagi tunda kasha nonon rashin kunya,yanzu dai ni dai ina duka motocin ƴaƴana aka kaisu"?.
Chapter 5 · 0% Book details