← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 63

Sashe 2

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba na ne ya yi wani mummunan faɗuwa ganin fitowar Yaya Bilal daga cikin mota ya yi ƙyau sosai cikin suite ɗinsa,ƙyaunsa ya ƙara fitowa sosai kamar ka ɗaukesa ka gudu,ƙyaunsa da nutsuwarsa sun ƙara fitowa sosai.na yi wani tagumi azuciyata ina tuna ranar da zan iya barin tunanin Yaya Bilal a cikin zuciya,Yaya Bilal namiji acikin maza yana da wani ƙwarjini da cikar zati,duk wannan abinda na ke yi Yaya Bilal bai san ina yi ba don tsakani na dashi hantara da kuma kallon banza,donshi aƙwaishi da miskilanci sosai.
Cikin takunsa mai ƙyau da haiba ya ƙaraso inda Kaka take ya rungumeta yana cewa"my grand fa dafatan na sameki lafiya".da yake shiba mutum ne mai magana da yawa ba yafi yin magana kaɗan,ai kuwa nan kaka ta zage tana ta basa labarin cin kashin da aka yi mata,ina cikin satar kallonsa sai kuwa naji ta ce"kaga waccen ƴar baƙar ita ce ta fara wulaƙantani a wajen nan har kowa ya samu bakin yimin wulaƙanci,waiwayowa ya yi ya kalleni kallo ɗaya shima by mistake ya juya kansa,yaja hannun kaka suka tafi sashenta,kallonsu na yi cikin tsoro na ce"Rashida na shiga ukuna kinga wanna fitinanniyar tsohuwar zata jazamin ƙazamin duka,kinga wani banxan kallon da ya yi min kuwa?".
Dariya Rashida ta yi sannan ta ce"ai ni dai na godewa Allah da ban ma haɗa ido da wannan mugun sojan ba amman wallahi da na yarda na haɗa ido dashi da tabbas naga wulaƙanci don wallahi haɗuwarmu baza ta yi mana ƙyau ba".
Ɓata rai na yi na ce"ke kinga Rashida idan bazaki faɗi alkhairi ba to ki yi shiru don Allah don manzon Allah(S.A.W) ya ce ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru".
dariya sosai Rashida ta yi sannan ta ce"hmm so hana ganin laifi gaskiya Khairat ki rage son da ki kewa Yaya Bilal kada ya haifar miki da wata matsalar,don ni har tausayinki na ke ji kina ganin mutum kullum fuska a ɗaure ki rasa wanda zakice kina so sai shi,kuma ke kinfi kowa sanin baƘwa wani Ɗasawa dashi don shi kaf gidannan in banda wannan rigimammiyar tsohuwar babu wanda ya ke gani da gashi."tsabar haushin Rashida da na keji don ni a rayuwata babu abinda na tsana irin zagin Yaya Bilal.
Anyi sha'ani sosai ranar anyi hotuna kala2 ana cikin hotunan na ce"Rashida don Allah muje wajen Kaka itama tazo muyi hoton babu daɗi wallahi tunda babu Kaka".na faɗi hakan cikin shagwaɓar da ta zamemin jik.
"caɓɓijan wallahi idan ke zakije Khairat ga hanya nan amman ni la.la.la.don bazan kwasowa kaina masifa ba".
Kinga tunda wannan masifaffan yazo gidannan yau to wallahi mu ta ka asannu idan kuma ba haka ba mu ɓallowa kanmu ruwa".
ÆŠaure fuska na yi sannan na ce to ni dai na tafi kada Allah yasa ki taho,uwa É—aya uba É—aya amman kina yiwa yayanki shedar zur.
Dariya sosai Rashida ta yi sannan ta ce"inna ta gaida aisha don wallahi bazanje in janyowa kaina masifar da zata saka in kasa bacci ba".
a hankali na ke takawa har na ƙaraso sashen Kaka,na jiyo dariyarsu gwanin sha'awa,ina sakawa araina Allah yasa Yaya Bilal wataran inga yana yimin dariya haka don ni sai inga kamar kaf gidan ma yafi kowa tsanata har da ƙyanƙyami na ya ke yi,Don da kansa ya taɓa cewa Kaka shi ya tsane ni saboda kaf gidannan babu mai masifar kallon mutum irina gani baƙa kamar gawayi don haka shi ko kallona bai san yi.
Ina shiga Kaka ta gimtse fuska ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'Un yanzu tsabar baƙin ciki tun kafin abani tsaraba ta kika zo salon ki cinyemin duka?to wallahi ahir ɗinki mara kunya ɗazu ba ke ce ki ka badani acikin mutane ba wai ƙwalliyata bata yi ba,tunda ta inya mura ta yi ƙyau aini ba dole bane sai na yi".
Ko É—ago kai baiyi ya kalleni ba na ce"Yaya Bilal sannu da dawowa".na faÉ—i hakan bakina yana kakkarwa kamar zuciyata zata fito haka na keji saboda tsoron yaya Bilal.
A hankali ya tashi ya fita baice min ƙala ba,na kalli Kaka inji ko zata yi magana sai kuwa ta ce"soja na don Allah ka ɓoyemin tsaraba ta da ƙyau eh ka yi ƙyaun kai da baka zauna wannan ƴar baƙar ta cinye min ba".
Ko da yazo wucewa ta kusa dani wani ƙamshin turare me mayen ƙamshi ne ya tafi da numfashina na lumshe idanuwa na ina jin ƙara son Yaya Bilal har cikin ƙoƙon zuciyata.
Kaka ta ce"to wannan kallon da ki ke bin namiji dashi fa,kin san dai ko a ƙafa aka ɗaura ki bazai kalleki ba,don matar soja ta dabance ba irinki ja'ira ba."
"haba Kaka tunda na shigo ki ke ta zagina gaskiya Kaka ki daina wannan abinda ki ke yi wallahi wannan abin ba dai dai bane,yanzu idan kina faɗar haka a kusa dashi ƙara jin haushina zaiyi kuma kinfi kowa sanin yadda ya tsaneni".
Sai na faɗi hakan kamar zanyi kuka ta ce"Haba ƴar baƙa aike mijinki ma na dabanne wallahi don ke har kin fisu ƙwari ma da kuma hazaƙa,naga ƙwanan nan ma zaki yi saukar alqur'ani kinga kuwa kina da baiwa da yawa".
ƴar dariya na yi na ƙwanta kan cinyarta ta ce"yau naga ta kaina Ni Fatima wannan ƙarfaffar yarinyar zata karyani kowa ya hutu,kinyi wa iyayenki guda 12 asara.Yar dariya na yi sannan na ce"gaskiya Kaka kin iya haihuwa yanzu har ƴaƴa 12 ki ka haifa a cikinki?gaskiya kin zazzagu".
kamar kaka na jira sai kuwa ta ce"Hmm iyayenku ai su sunƙi zazzaguwar ita wancar yellow ɗin kamar ɗorawa ita ta haifawa malik yara biyar,ita kuma waccen sadakar yallan ta haifa mishi uku,ita kuma inya mura wato uwarki ta haifa masa huɗu,to duk sayi sa gama don ni dai babu ruwana ato aura zansa ka ya yi ƙwanan nan".da mamaki na ke kallon kaka don ita daman haka zancen ta ya ke da kun fara abin arziƙi idan har bakayi da gaske ba zai kuma na tsiya.
Zumɓuro bakina na yi na tashi na tafi sai kuwa ta ce"wallahi kin zunɓurawa inyamura mai baki kamar na shantu,ato ke Allah ya dubeki da baki yi wannan shegen bakin ba kamar ƙofar gari.ta gyara zamanta tana cigaba da cin goronta.

Ranar ɗaurin aure da wuri muka shirya mu ƴan matan gidan duk anƙwan shadda fara mukayi,iyayenmu kuma skye blue,samari kuma arsh sukayi.
Wajen Kaka na shiga ina zuwa naga ta yi baƙi ɗakinta cike da mutane amman maza ma sunfi yawa wasu pan gidanmu wasu ba ƴan gidanmu ba.
Na gaishesu na kama hanya zan fita sai naji kaka na ce wa"ƙwaji shasha Salisu ba yanzu ka gama yimin ƙwatancenta ba?ka ce inya maka iso kana sonta kuma tazo kabarta ta fita,to wallahi ni babu ruwana gwara ma ku sasanta tun yanzu don wallahi na gaji da kallon ƴan matan gidannan yara sunkai talatin duk ƴan mata,wannan ma idan kana da hawan ruwa ai sai ya tashi".

ni dai ranar kunya ta isheni azuciyata na ce kaka kenan É—azu ta gama faÉ—ar munyi kaÉ—an yanzu kuma ta ce wai munyi yawa,kaka kenan babu mai iya mata sai ita.
Shima wanda ta kira da Salisu É—in kunya sosai ce ta kama sa,ya kama rufe fuska,ni kuwa É—an satar kallonsa na yi sam wallahi baiyi min ba ni wallahi ko da ma ace ya yi min ni yaya Bilal na ke so.
Da sauri na yi hanyar sashensu Rashida sai ga Salisu ya biyo ni a baya yana yimin magana,ban iya wulaƙanta ɗan adam arayuwata don haka na juyo muna cikin gaisawa sai ga Yaya Bilal ya fito daga cikin sashensu ya yi bala'in yin ƙyau cikin shaddarsa ruwan arsh,ta zauna sosai a murɗaɗɗan jikinsa mai ƙyau da tsari,kaf gidanmu babu wanda ya yi fari da kuma ƙyau irin na Yaya Bilal shine ya yo asalin kakanmu,kuma Yaya Bilal yana kama da babanmu wato alhaji abdulmalik.
Ayanzu yaya Bilal soja ne yana a matsayin Admiral ana ce masa Admiral Bilal Mohd.in kiyarsa Admiral B.
Gaba ki ɗaya hankalina da nutsuwata duk yana kan Yaya Bilal,Salisu yana ta zuba surutunsa dai daga baya ya gane ce wa hankali na yana wani wajen ba wajensa,mamaki sosai ya ke ganin wanda na ke kalla tabbas idan baiyi ƙarya ba yasan wannan yaya na ne kuma yasan ɗa ne ga yayan mahaifina amman ya aka yi haka na ke ta kallonsa lallai aƙwai lauje cikin naɗi a wannan lamarin,don ruwa baya tsami banza sosai Salisu yaji haushin wannan lamarin ya juya ya tafi don shi tunda ya ke bai taɓa buɗe bakinsa bama ya ce,yana son wata ƴa mace ba sai akan Khairat amman ta wulaƙanta sa haka.
Anyi bidiri sosai aka saki kiɗa amman iya mata ne kawai ƴan uwan Mama suma sunyi na su al'adun na inyamurai,ashe abin ya zaunawa Kaka a ƙoƙon zuciya ta shige ɗaki ta fara kuka wiwi,ashe lokacin Kishiyar mama na ta ganta wato Hajiya Iklima ta biyo kaka don salon gulma tana tambayar kaka abinda ya faru,haba daman kaka na jiran ƙiris ta ƙara volume ɗin kukanta tana tirje tirje kamar ƴar yarinya ƙarama,ta ce wa mama iklima ta je ta kirawo mata malik da sauran ƳaƳanta.
Duka iyayenmu maza suna babban farlon gidan ana hira ta zumunci,sosai hankalinsu ya tashi maxa goma ɗinnan duk suka taho daman biyu ne mata ƴaƴan kaka goma maza,nan fa kaka ta shiga gaya musu wai tana ji lokacinda aka ce a ƙara volume tunda masifaffiya ta iso.

*Miss green ce*
[23/09, 16:15] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_

📃Littafi na 1

By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*

*GAWURTATTU 5*
-----------------------
*wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
---------------

*Arewa book user*

https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
--------------------

*Sirrinmu* manzon Allah (s.A.W) ya hanemu da gujewa mazajenmu a shimfiÉ—a yin hakan babban laifi ne kuma tsinuwar mala'iku za ta tabbata akanki. --------------------------------

3🟪4

.. .Dukansu suka haɗa baki wajen ce wa "umma lafiya me ya faru?".kukan ta ƙara fasawa tana ce wa"yanzu har lokacin wulaƙanta ni agidannan ya yi?gaskiya zan bar muku gidannan ku zauna ku da matanku tunda haka kuka zaɓa".

dukansu shiru suka yi sai malik ne ya ce"Umma ki faÉ—a mana abinda ya faru,don mun shiga cikin duhu wallahi".
Chapter 2 · 0% Book details