← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 63

Sashe 58

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

•3)- Ki guji cire farce da hakori. Ko da ya zama cewa wani abu ya taba farcenki ya yi irin dagowar nan, kada ki sa hakori ki cizge shi, domin hakan zai sa ya  fita ba bisa ka’aida ba ta yadda har zai sa a tsarin farcen ya zama wani iri daban. Wato sai ki ga wani bangaren na farcen ya fi wani tsawo. A maimakon haka ki sami reza ko kuma abin yankan farce da ake kira da nail cutter ki  yanke farcen da shi.

•4)- Kada ki bari farcenki ya zama a jike koda yaushe, domin hakan zai sa ya rika kakkaryewa tun  kafin ma ki kai ga yankewa. Idan ya zama za ki yi aiki da ruwa, yana da kyau ki sami irin safar hannun nan ki sa, don ta kare miki faratanki daga lalacewa.

•5)- Kada ki yi amfani da alkamashi wajen yanke farcenki, ko da farcen ya kasance mai rauni ne, balle kuma ga wanda ba shi da wata matsala.

•6)- Bayan kin kammala da yanke faratanki za ki iya samun man farce ki shafe su da shi, wanda hakan shi zai sanya faratanki su rika walkiya da sheki, ba lallai sai kin sanya jan farce ba.

Idan har ke mai sha’awar tara farce ce to ki tabbata cewa kina kula da su ta hanyar fitar da duk wata dauda da ke shiga cikinsu ta zauna. Idan kika kula barin dauda ta zauna cikin farce ba shi da kyawun gani a ido ma, ballantana ga lafiyar jiki.

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿

[23/09, 16:31] Miss Green🍀: 97. . . . . . 98

. . . .da sauri na ƙarasa wajensu haidar cikin tsoro na kalli Ahmad wanda shima ni ya ke kallo yaron yana masifar sona akaf cikinsu.na kallesa na ce"arman ina ɗan uwanku"?.rau rau ya yi da ido kamar zai yi kuka ya ce"mamy wai ya ce ba jai jo ba.wai tunda bakyason dadynmu".

Sosai na waro ido waje abin irfan yanxu mamaki ya ke bani,wato shi yafi son babanshi ko?abin ya tsayamin arai na gashi duk wajen da mutane,shahid ma yaji komai amman da ya ke shi mutum ne me haƙuri sai ya ce"Arman kada ka damu kaji Irfan zai xo shima zanxo in ɗaukesa".ya faɗi hakan yana mimmiƙa musu sweet da ya ke sun sanshi sai suka bishi suna ta bashi labarin dadynsu kaza da kaza.

Abin ya tsayamin araina wato shi Bilal har yanzu ba zai daina son kansa ba ko?duk ya koyawa ƴaƴansa hali irin nashi,na ƙullatar mutum,na goge hawaye na waɗanda har sun fara zubowa.Anty halisa wacce tazo yanzu taji abinda ya faru ta dafa kafaɗa ta ta ce"don Allah khairat ki zama me dauriya mana.kome aka yi sai ki hau kuka?ai wataran ma sai ka nemi hawayen karasa ko?".

Handcachep ta miƙomin wai in goge hawaye na,na saka na goge a hankali,na ɗaga idanuwa na kai tsaye suka sauka akan shahid wanda duk mode ɗinsa ya canja ganin halin dana ke ciki,ɗaga min gira ya yi yana murmushi nima murmushin na mayar masa.

Anci ansha sosai walima ta yi daÉ—i sai dai fatan samun zaman lafiya.Maryam ce babu lafiya tana ta amai Shahid ya ce bari ya kira likita ya duba ta.gwajin farko ya tabbatar Maryam na da ciki har na tsahon wata uku.sosai wajen ya ruÉ—e da murna Allah kenan yau shekara uku kenan da aurenta har da É—oriya.don tare aka yi mana auren farko.

Sosai yaya Aliyu ke murna kamar zai komar da maryam ɗin cikinsa.Anty khadija ma yanzu cikinne da ita yaranta biyu yanzu da cikin na uku,bata san Maryam nada ciki ba,don sosai takewa maryam gori wai Aliyu ya auro juya shekara uku ko ɓatan wata,sai gashi yanzu Allah ya kawo lokacin wanda ita da kanta bata san ma tana da cikin ba.

Kafin yamma kowa ya watse daga ni sai Anty Halisa sai maryam wacce ke É—an hutawa kafin su tafi,sai Æ´ar uwar Ammi wacce da kaÉ—an ta fimu Æ´ar yayar ammin ce.

Anty Halisa ta sakani agaba sai da na sake wanka,da ya ke har wankan tsarki zanyo tare da wasu sirrika waÉ—anda na har haÉ—a kuma ya kamata duk wata mace wacce ta gama al'ada ta yi sa.

Ki dinga tsarki da ganyen magarya da kaninfari baysn gama al'ada yin hakan yana sakawa ki koma dai dai bayan gama haila,sannan ki samu misk ɗan asali da audiga ƴar kaɗan kina goge duk inda jinin ya taɓa.wannan yana ƙarawa mace kima sosai awajrn mijinta.kuma wannan ba sai matar aure ba hatta bazawara ko budurwa za ta iya yinsa.

Zuwa dare kowa ya watse daga ni sai halina na kimtsa cikin doguwar rigar bacci wacce ta amsa sunanta na taje gashi na wanda yasha gyara da mai na gashi masu daɗin ƙamshi,da sanyaya zuciya.

Fara ce ƙal rigar wacce ya ƙwantamin sosai kamar daman anyi tane saboda ni,na sanya hijabina na tada sallar magrib na ɗaga hannaye na sama ina godewa Allah da wannan ni'imar da ya yimin.na aurar salihin bawa irin Shahid na roƙi Allah ya rayamin yara na da al'ummar musulmi baki ɗaya,Allah kuma ya dawo da hankalin ɗana kai na don abin ya razanani sosai a ƙananan shekaru irin na Irfan wai har yasan ya ƙullace ni.na shafa addu'ar sai naji shahid ya ce"Amin".

Da sauri na juyo ina kallonsa,yana sanye cikin pakistan irin wanda ƴan idia ke sakawa irin fari ƙal ɗinnan ya yi kyau sosai.na shagala a kallonsa sai kawai naji ya janyoni baki ɗaya na.ya ce"ni dai adaina kallona haka ƴan mata".ya faɗi hakan cikin salon yaudarata.

Wani yarrr naji tun daga ƙafata har ƙwaƙwalwata na ce"ni ba kallon ka na ke ba.to ma da wani idon kasan ina kallonka"?.sosai na burgesa yadda na yi maganar cikin yana yi shagwaɓa ya lakato gefen kumatu na ya ce"Hayatee yaya ki keji da ki ka ganmu a matsayin mata da miji"?.

Harararsa na yi nima cikin tsoka na ce"ni babu komai".ƙara janyo ni ya yi har muna jin numfashin juna daga nan fa salon ya canja.

Sam Shahid bai da takura kuma yana da matuƙar haƙuri da bi da mace yadda ya kamata.bai matsamin akan komai sai abinda na ce,sosai muka raya darenmu cikin so da ƙaunar junanmu.kuma gaskiya jarumi ne sosai don ba ƙaramin gajiya na yi ba,shi kuwa har kuka ya yi saboda wani irin mugun daɗin dana jiyar dashi.

Sai sakamin albarka ya ke,yana ganin babbar wautar da Bilal ya yi na saki na,don shi gani ya ke babbar wauta ce a saki mata iri na don na haɗu ta ko'ina,sosai Shahid ya mori kayarsa,nima sosai naji daɗin kasancewa dashi,don bashi da takura kamar yaya Bilal,shi shahid dai dai buƙata ne gashi da tausayi sai lallaɓani ya ke yana bani haƙuri kamar ya yimin laifi.ni abin nashi ma dariya ya bani.

Rayuwa da shahid ya nunamin menene daɗin aure,menene shi kansa auren,ashe daman haka aure ya ke da daɗi?ashe ni da acen baya ba aure na yi ba?haƙiƙa sai yanzu shahid ya lasamin zumar aure.bani da matsalar komai agidansa don Ammi ma mutuniyar kirki ce babu ruwanta ko kaɗan.

Na zaɓi in dinga yiwa miji na girki tare da gyara masa ɗakinsa,don ko ina na gidan ma'aikata na shiga su gyara ammanfa nan na yi musu iyaka ciki kuwa har da ɗakina.

Na yi wani irin mugun kyau da fari,ashe dai nima farar ce ba baƙa ba?to me ya hanani yin fari dacen ɗin?".sosai na ke tambayar kai na musamman ma yanzu yadda na yi wata iriyar ƙiba musamman ma hips ɗina kamar an bubbuɗa ni.

Ranar daren farko na Shahid ya yimin kyautar danƙareriyar mota,da kuɗi wanda kawai sai jin alert na yi,na duba na zaro ido alokacin shi kuma yana wajen amminsa na murza idona sannan na duba wani saƙo da ya turomin.

"Hayatee dafatan kin tashi lafiya kada kiga ban tsaya awajenki ba.Ammi ce babu lafiya tun jiya da daddare.ilove u too my wife".

Shafa saƙon na yi ina jin mugun ƙara son shahid har rai na.

Na tashi kenan xan shiga banɗaki ya turo ƙofa ya shigo gabana ya yi mugun faɗuwa.tuno abinda ya faru na sunkuyar da kaina kunya ta isheni.ya ce"ayya meye kuma na kunya?munfa zama ɗaya kenan komai nawa ya zama naki.kin zama ni na zama ke don haka ni gaskiya bana son kunyar nan tana cutar dani.

Ya faɗi hakan yana sungumata sai banɗaki,duk yadda naso wajen hanasa amman bai haƙura ba da kanshi ya ɗakkomin kayan dazan sanya wata doguwar rigace ta atamfa wacce ta yi matuƙar yimin kyau sosai.

Da ya ke shahid na mugun son atamfa sosai,atare muka tafi dashi wajen Ammi ta rungumoni ina yi mata ya jiki ta ce"kai son yanzu sai da ka gaya mata?"ta faÉ—i hakan tana harararsa.
Sosai rayuwarsu tak burgeni don su basa É—aukar rayuwa da zafi gashi dai suna da kuÉ—in amman kuma babu ruwansu da wani saka ido ko wani abu.

Ana cikin wannan ɗan yanayin ne na fara laulayi sosai,wannan karan tun watan farko ya nuna kansa,don ba kaɗan na sha wahala ba duk na yi sanyi babu yadda baiyi da muje asibiti ba naƙi,daya gaji ya kiramin likitansu yazo har gida.

Likitan yana murmushi ya ce"congrat matarka nada ciki amman ƙarami ne sosai,sai kuma an kula da ita don ulcer nason kamata saboda bata cin abinci."
Chapter 58 · 0% Book details