← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 63

Sashe 17

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rashida tazo ta wuce ta kusa dani tana ƴar dariyar mugunta,yadda kasan in shaƙesu haka na ke ji tsabar baƙin ciki,jikina duk a mace na ƙarasa ina kallon ƙasa,na gaishe sa ya amsa sannan ya ce"sannu gimbiya mai koyon ɗinki?Khairat ban taɓa tunanin haka daga gareki ba?banyi tsammanin haka ba?nasan ke mutum ce mai gaskiya hasalima baki iya ƙarya ba?to me yasa ki ke min ƙarya ni?tabbas ko da baki faɗa ba nasan komai Khairat,bakya sona Khairat idan na fahimta kamar dole na yi miki amman ki yi haƙuri don Allah idan na takura miki,zuciyata ce bata yi min adalci akanki son da na ke miki shine ya ɓoye mode ɗin fuskarki gareni,ina son ki fito sosai straight foward ki faɗamin matsayi na agunki don Allah".

kasa ce wa komai na yi sai da yaga ƙwalla ta taru a idanuwa na alamar zanyi masa kuka sannan ya ce"sorry yi haƙuri kinji ban ɗauka wannan maganar za ta ɓata miki rai ba,amman don Allah ki yi haƙuri ki daure ki faɗamin abinda ke ranki saboda kada mu ɓatawa juna lokaci tsakanina da ke".

Cikin siririyar murya ta na ce"yaya Mk ka yi haƙuri amman wallahi bawai bana sonka bane kunyar anty khadija na ke ji shiyasa na ke ce mata ta ce na je koyon ɗinki".ɗan murmushi ya yi sannan ya cs "khairat kenan uwar kunya to shikkenan yanzu dai ayi haƙuri adinga kulani kinga duk yadda na rame saboda tunaninki ko aiki fa bana iya yi a office?sai dai inyi ta rubutu shirme".dariya ya ɗan bani rayuwa kenan shi yana sona baki ɗaya da zuciyarsa ni kuma ina son wanin sa haka.nan dai muka cigaba da hirarmu ya ɗauko wani ƙaton gift a nannaɗe na miƙomin yana murmushi don shi ma'abocin murmushi ne.

Juya abin na yi a hankali sannan na ce"na gode yaya mk Allah ya ƙara arziƙi".ɗan murmushi ya yi yana kallona sannan ya ce"ba komai matata kada kiji komai gobe Baba zai dawo daga tafiya inason in shigar da maganar aurenmu ayi komai a gama".

Ai ban san sanda na zaro idanuwa na ba cikin tsoro,kallona ya yi sosai sannan ya ce"lafiya ki ka tsorata haka?ko kuma tsoron auren ki ke"?.mayar da wani malulun da ya tokare ni na yi sannan na ce"ba komai".daga haka ban ƙara cewa komai ba har muka rabu na koma cikin gidan.har na shiga bai daina kallona ba ya shafa gashin kansa sannan ya ce"khairat ina sonki da yawa Allah ya bani ke na more mata".
Ina komawa ciki suka fara yimin dariya ba babu ma wacce tafi ban haushi irin Maryam na kai mata duka na ce"banza uwar ƙarya kawai".dariya ta yi sosai sannan ta ce"don Allah khairat ki bawa yaya mk dama mana ya fito musha biki?ki manta da wani yaya Bilal".ɗaka mata wani duka mai zafi na yi sannan na ce"aniyarki ta biki insha Allah yaya Bilal zan aura".tare suka haɗa baki wajen ce wa"to Amin tunda kin dage sai shi".

Rashida ta ce"banza shine da zaki taho ko sallama babu bayan kin tafi na ce wa baba zanzo kema kina nan gidan shine ya ce wai bazan zo ba zamu cika musu gida,to ashe ma zan yi wa yaya mk aiki mai ƙyau".duka na kai mata ta kauce muka cigaba da hirarmu anan muke ta zancen auren Su Sauran wata ɗaya yanzu muka cigaba da hirar bikin anty khadija ma tazo ta cigaba da bamu shawarar ankon da zamu fito dashi don haryanzu ruwan ido mun kasa fitarwa.

Yaya Aliyu ya dawo daga tafiyar da ya yi ranar ina kitchen ya dawo anty khadija tana bacci da gudu na je na rungume yaya nawa,ya ce "kai wai ke haryanzu baki girma ba?ko da ya ke kaka ta ɓata ki wallahi".cikin shagwaɓa na amshi kayan nasa shi kuma yana tsokanata,yaya Aliyu sam bai da hayaniya don dukkanmu mamanmu mu ka yo yaya Salim ne dai mafaɗaci shi kuma abbanmu ya yo.

*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*

1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_

Guda É—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huÉ—u N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*

Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.

Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224

...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

*Miss green ce*
[23/09, 16:17] Miss Green🍀: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI🥚*

MALLAKAR
*ummu maher(miss green)*🍀🍏

*GAWURTATTU BIYAR🔥🔥*

23🟨24

... . .zaro idanuwa na na yi kamar maryam Ɗin tana kallona na ce"kai maryam ni fa bana son wasa wallahi"?.ina faƊar hakan na saka takalmi na na fito tsakar farfajiyar hajiya kaka A cen Ɓangaren maryam ta ce"ni wallahi khairat abin ma mamaki ya bani".

"ikon Allah to daman wai yaya Aliyu yana sonki ne ko kuwa?".jan numfashi maryam ta yi sannan ta ce"haba khairat idan da yaya Aliyu yana sona ai zaki sani ko?".

Nan dai muka cigaba da hirarmu ni da maryam awaya har take cewa gobe zata zo mu Ƙarasa maganar,na tsokana ta da ce wa"to matar babban yaya sai kinzo".dariya ta yi sosai sannan ta ce"hmm ni dai wallahi ki yi a hankali kada anty khadija ta jiyo ki".sosai na Ɓarke da dariya na Ce"kin san Allah ni dai koma manene naji daƊin haƊin nan don idan yaya ya aureki to tabbas ya samu mata,ga Ƙyau da ilimi ga tsafta".dariya ta yi sannan ta ce"hmm ke dai sai nazo khairat yanzu ma umma ce ta aike ni gidan anty hajara kin san ba tada lafiya laulayin ciki ya saka ta a gaba".

"kash!to Allah ya bata lafiya".ta ce amin muka kashe wayar a tare na dawo Ɗakin kaka na zauna na kalli anty khadija wacce i'tama ni take kallo ta ce"yauwa daman hajiya kaka so na ke muyi wata Ƴar magana dake".

gutsirar goronta ta yi wanda ya bada Ƙara ras,sannan ta ce"ke uwar iyawa ina jinki?Ba'a banza uwarki take a buzuwa ba saboda ƙazantar ta da kuma iya son asanta take da shegen iyayi,amman fa ni duk iyawarta kallonta na ke tsaf,don ni Ɗinnan duk iyawar mutum kallonsa kawai na ke."

ganin Hajiya kaka na Ɓaro zance anty khadija ta ce"haba hajiya kaka to me ye kuma na sako iyaye aciki?Ke fa sai ana magana ta arziƙi sai kuma ki hau zagin mutane".

"Au kinji tsoro kenan?a'i wallahi ni dai jika na ya shiga ukunsa da fitinanniyar Ƙazanta,daman Ɗana yana fama da ƙazanta,babu yadda banyi ba akan inga ta daina Ƙazantar nan amman babu yadda zanyi,Allah ya haƊa Ɗana da Ƙarfen Ƙafa shiyasa ma na sallama mata shi kawai,to yaya zanyi a'i dole ma in sallama tunda anfi Ƙarfina".ta faƊi hakan kamar za ta yi kuka.

sosai abin ya bawa anty khadija haushi fuuu ta fice daga Ɗakin duk ranta a Ɓace,duk wani Ɗan tattalin farin cikinka da ka ke idan kazo wajen kaka sai ta Ɓa ta maka rai musamman ma idan baƘwa shiri da i'ta don ita daman kaf gidan mutum biyu ne mutanenta Bilal da kuma khairat.
tana fita na kalli kaka cikin sanyi na ce"haba hajiya kaka?i'tama fa anty khadija naga jikar kice kuma meye na yi mata haka?".sheƘeƘe hajiya kaka ta kalleni sannan ta ce"to dukana za ki yi uwata?saboda matar yayanki ce shiyasa zaki ce haka ko?wannan Ƙazamar ai ko jika ta ce wallahi sai na faƊi gaskiya,yo aƘwai mai duka na ne?da sauri na ce"a'ah hajiya kaka Allah ya baki haƘuri".

kuƊi naga ta fito dasu masu yawa na ce"Hajiya kaka waƊannan kuƊin fa?au daman su ki ke Ɓoyewa?".da sauri ta ce"ah haba khairat aike nasan bazaki faƊawa kowa ina da kuƊi ba?damanan wannan kuƊin Soja ne ke bani su duk wata dubu talatin ya ke bani duk wata to shine yanzu na Ɗebosu a bankin bankin ya cika shiyasa zan ajje su saboda ga buki ga kuma saukarku tazo shine zan bayar ayimin dubulan da cin-cin ko?".

Dariya sosai na yi sannan na ce"ah lallao hajiya kaka ki ce zamuci daÆŠi".na faÆŠi hakan gabana yana dukan uku-uku saboda aduk sanda aka ambaci sunan yaya Bilal sai inji zuciyata tana bugawa sosai.
***

"Kai Captain Ahmad gaskiya ban cika son shiga geton nan na ku ba,saboda wallahi duk motata Ɓaci take".daga cen Ɓangaren aminin Bilal wato Ahmad ya ce"ai kuwa mutumina dolenka kazo tunda dai yau dubiya zakaxo,Gauro kawai kasani ma ko ka sami mata a geton na mu".?

"kau haba captain ta ina kuma ?A haba a wannan geton gaskiya never for ever".dariya Ahmad ya yi sannan ya ce"to magani a Ƙasa dai nan da wasu Ƴan watanni musha biki".

wannan maganar da ya yi kansa ne yaji har ya fara sara masa ya shafa goshinsa yana ajiyar zuciya ciwon marar da ya ke ne yaji yana tsarga masa ya riƘe cikin yana kiran sunan Allah har ya fara jin dai dai.

wata zazzaƘar murya yaji tana ce wa"hmm aisha ni fa wallahi na matsu ranar saukar nan ta yi,don wallahi so na ke kawai in ganni da allon sauka na".

bai san ya aka yi ba ya dawo baya kaƊan,wata kyakkyawar yarinya ya hango fara ce sosai tana da siririn hanci da Ɗan Ƙaramin baki,pink lips ne da ita fuskarta rawn face ne da ita,ga wani kyakkyawan dimple shigen irin na khairat wanda ya Ƙara mata Ƙyau sosai,idanuwanta kamar na mage irin tana jin bacci.

tsayawa ya yi cak da motarsa yaji zuciyarsa ta wani harba masa,sam bai san wani so ba amman ya tabbata yanzu ciwon so ne ya kamasa daga kallo Ɗaya,da sauri jidda taja baya don Ƙur'anin da ta rungume yana son faƊuwa cikin fushi ta Ɗago tana kallon motar Bilal.

A hankali Bilal ya fito daga cikin motarsa idanuwansa na kan jidda Ƙur wacce take sanye cikin green Ɗin hijabinta wanda ya yi matuƘar haska ta.
Chapter 17 · 0% Book details