← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 63

Sashe 55

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga nesa ya sakani agaba da kallo kamar zai cinye ni,kunya duk ta ishe ni Iman ta biyo ni da gudu wai zata bini,maimakon tazo inda na ke sai naga ta canja ƙwana tana ce wa"Baba oyoyo". Da sauri na ɗaga kai na ina kallon wanda take kira da baban Bilal na hango yana sanye cikin kayan sojinsa ya haɗe rai kamar bai taɓa wata dariya ba.. ... .✍🏿

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿

[23/09, 16:30] Miss Green🍀: 91. . . . . . .92

. . . . . . .nunawa na yi kamar bansan abinda suke ba,na yi wuce wata gaba zuwa wajsn masoyi na,fuskata Ɗauke da murmushi,wani irin kallo me cike da soyayya ya ke yimin yadda yaga na komar kamar Ƴar shekara goma yarinta na ta Ƙara fitowa sosai,ga wani irin mugun Ƙamshin dana ke fitarwa me gigita namiji,ai kuwa shahid ya gigice Ɗin sosai amman duk da haka hankalinsa na kan Bilal wanda ya Ɗaga iman sama yana yi mata wasa.

Ya ce"hayatee wannan shine baban lovely children ÆŠina"?.sosai gabana ya faÆŠi ahankali na ce"eh shine na manta ban faÆŠa maka ba,yaya ya ke gare ni".sai naga fuskarsa ta haÆŠe nan da nan,na lura shahid shima namijin kishi ne sosai,daman kuma ance larabawa sunfi kowa kishi.

Ya ce"ayya kada ki damu don na tambaye ki ki yi haƘuri,amman wannan yayan na ki wata macece za ta ce bata sonshi?babu abinda Allah bai yi Masa ba,amman na yi mamakin rabuwarku,kuma kema khairat nasan ba zai so rabuwa da ke ba,sai dai Ƙaddara amman duk namijin daya sakeki khairat wallahi ya yi asara gaskiya".

Murmushi kawai Na yi don bani da amsar da zan bashi,don kada yabi inda muke sai ya Ɗauki Ƴarsa suka yi gaba abinsu.Ina jinsa yana tambayarta Ƴan uwanta,sai kuwa iman ta ce"dady mamanmu ta Ƙara yi mana wani dadyn ka ganchi cen ma".ta fara nuno inda Muke.Bilal bai san lokacin da wasu hawaye masu zafi suka fara zubo masa ba ya yi saurin gogewa ya wuce.

to ranar dai da Ƙer shahid ya barni na wuce gida na lura bai gajiya da kallona,idan na biye masa kuma sai muyi ta tsayuwa awajen,don haka na ce"habibee ni zan tafi gida fa mun daƊe".na faƊi hakan cikin shagwaƁa,sosai na burgesa ya ce"ah lallai baki so kije gida yanzu,ni wannan shagwaƁar taki tafi komai tafiya dani",yauwa khairat ki yi haƘuri ni dinner bata cikin tsarina sam,duk kuwa kuƊin da na ke dashi,amman mu al'adarmu a musulunce shine bayan anyi aure ana walima washe gari,to ni dai hakan yafi Ƙwantamin".

murmushi na yi sannan na ce"kada Ka damu nima duk wannan bidi'ar bata gabana albarkar auren shi na keso".sosai na burgesa amman fa muna cikin zancen naji alert Ɗin kuƊi awayata na ce"habibee naga ka turomin kuƊi me zanyi dasu haka"?.murmushi ya yi sannan ya ce"ki yi wani abin dasu,amarya ta me sirrin kyau".ya faƊi hakan yana murmushi,bai bani damar Ƙara magana ba ya yi shigewarsa cikin mota ya yi gaba.

Sosai na keson shahid,ba don kuƊinsa ko kyau ba,a'ah sai don tsare mutuncinsa,sam bai taƁa koda taƁa hannuna da sunan wasa ba,balle kuma wata maganar banza,muna mutunta kanmu mu duka,anan na ke jan hankalin Ƴan mata da zawarawa adinga riƘe mutunci da kyau,saboda ke mace duk abinda ki ka yi bai Ɓoyuwa namiji kuwa ko zai yi sau Ɗari ba'a Ganewa,kuma a musulunce ma hakan sam ba shida kyau kuma ma ba tarbiyya bace.kuma matuƘar ki ka sadaukar da mutuncinki ga wani to fa wannan mijin koda tare ku ka yi lalatar bazai taƁa ganin darajarki ba,balle kuma akaiga zancen mutuntawa,don shi aure anfison ayisa da ganin mutuncin juna.

da kai na na ware kuƊi masu yawa aka sakewa hajiya kaka sabbin kayan Ɗaki aka yi mata sabon fenti,mama na itama aka sake yi mata furnitures duk da basu daƊe ba,sannan mama ta faƊawa babana duk kuƊin da shahid ya ke bani,baiyi mamaki ba ko kaƊan don yaron yasan tarihinsa tun farko har zuwa yanzu,mahaifiyarsa da mahaifinsa suna da kuƊi sosai kuƊi kuma masu mugun yawa,shi da kansa shahid a iya nigeria ma yana da company's sunfi ashirin,ga kuma na Ƙasashen waje,uwa uba kuma likita ne me zaman kansa me kuma lasisin kowacce Ƙasa,likitan zuciya ne shi,mahaifiyarshi kuma unguwar xoma ce.kuma ba Ƙaramin kuƊi suke samu ba.

ranar daya rage saura Ƙwana biyu gidanmu ya cika Ɓam kamar auren budurwa,son hatta ankon biki,sai da shahid ya turomin kuƊi wai abawa kowa,wai su haka suke yi naƘi amsa sai gashi ya lallaƁa yaje wajen hajiya kaka,itama da farko taƘi amsa amman da taga ransa ya Ɓaci sai ta amsa,ai kuwa kowa sai daya samu ankon biki,ranar Ne kuma amminsa tazo gidanmu mata mai mutunci da sanin darajar mutane,ta Ɗakko wata mata wai za ta yimin gyaran jiki na larabawa.

daga ganin matar ma balarabiya ce wataƘil Ɗakkota aka yi,,harda Ƙanwarta tazo ita ammin,duk suna da mutunci sosai naƘi fitowa wai ina jin kunyarsu ta ce"a'ah khairat mufa bama jin wannan kunyar gwarama tun yanzu ki saba don shahid ba shida kunya wallahi".murmushi kawai na yi ai kuwa aranar aka fara yimin gyaran jikin,wowo hmm wai ko tsagar gida ma hanani fita matar ta yi sai dai ina Ɗaki ina shan a/c,Mutanen gidanmu suka dinga zuwa ganin ammin shahid,shima tun daga ranar ammin ta hanashi xuwa saboda gudun saƁawa Allah don taga yadda Ƙirar khairat Ɗin take,ba kowani namiji ne xai iya kallonta ya kyale ba,duk da ta yarda da Ɗanta mutum ne me kana kansa sosai,da tsantsae tsoron Allah,,shiyasa a kullum take godewa Allah da kyautar da ya yi mata na samun Ɗa kamar shahid,daman kuma ba yawan yara akeso ba albarkarsu ake nema.

kullum muna maƘale awaya ni da shahid ana zuba soyayya na lura su larabawa mayun soyayya ne,kamar laila majnun.

Baba na ya saka aka kirawo masa Bilal ya ce"Bilal kasan me yasa nasa ka aka kirawomin kai?".girgiza kawai ya yi,idanuwansa sunyi ciki duk ya rame abin tausayi ya ce"ina son ka yarda da Ƙaddara me kyau ko mara kyau,ka cire komai aranka kamar ma ba'ayi ba,kai Ɗinnan dai yayan khairat ne kuma uban ƳaƳanta har huƊu,to kaga aƘwau akaƘa me Ƙarfi a tsakaninku,don haka yanzu ma na kiraka ne don ka zamo waliyyin khairat,don ance babban wa uba koda ace yanzu mu faƊi mu mutu kai ne babansu su duka".

sosai wata zufa ta shiga tsattsafo masa,ya goge ta cikin dauriya da Ƙarfin hali ya ce"ba bu komai baba na gode da bani shawara da ka yi."baba yaji daƊi sosai suka cigaba da hirarsu amman can cikin zuciyarsa yana jin wani abu yana yi masa yawo sosai,ranar dai Bilal kusan Ƙwanan zaune ya yi,saboda tsananin tashin hankali,gobe khairat Ɗinsa xa ta Ɗaura aure?da wani ba shi ba?za ta tafi gidan wani?yanzu shikkenan sun rabu har abadan?tuni ya dinga kuka kamar ba shi ba,tabbas yanzu yaga illar rashin yin bincike kafin Ɗaukar mataki,kuma yanzu yaga illar yin saki har uku,da Ɗaya ya yi mata ko biyu da yanzu suna nan zamansu gwanin sha'awa.

Anan nake jan hankalin maza akan mu kula mu daina yanke hukunci cikin fushi,an sani kuma an yarda ita rayuwar aure tana zuwa da Ƙalubale daban daban kuma sai anyi haƘuri sannan ake samun abinda ake so,don haka mu kasance masu haƘuri ako ina kuma aduk halin da muka tsinci kanmu.

to nima anawa Ɓangaren hakan ta kasance amman tsaƁanin tunaninmu ba Ɗaya bane da Bilal ni da Shahid ci ke muke da zumuƊi da son kasancewa da juna,na tuna gobe iyanzu ina rungume jikin mijina abin alfaharina,ina matuƘar son shahid son da bai ko na yaya Bilal ba,don sai yanzu na gane ashe lokacin ban san ma wani so ba,sai yanzu nasan so don shahid ya shayar dani madarar soyayya.

******

Washe gari na chaƁa adona cikin wata doguwar riga wadda shahid ya kawomin me shegen kyau,kalar skye blue ta tasha kwalliya har ya gaji,kowa sai bina da kallo ya ke kamar wata acikin zarah,gidanmu ya cika Ɓam,Ƴan huƊu ma sunsha Ƙwalliya sosai da skye blue Ɗin shadda aka dinga yi mana hotuna dasu,don tun sassafe ya aiko da wani me hoto wanda ya Ƙware yasan kuma aikinsa,kuma baƘar fata ne amman ya iya hoto sosai yasan kuma aikinsa,don duk wanda aka yiwa hoton sai ya yi murna saboda hotunan suna fita tarwal sosai.

iyaye na guda 12 duk anyi mana hotuna dasu gwanin sha'awa ga Ƴan huƊu agaba suma sunyi kyau.

Ɗaki na ya cika da Ƙawaye sosai,Mukaji shigowar angwaye bayan an Ɗaura aure,da sauri nadiya ta ce"khairat tashi ki leƘa kiga angonki sai jin kunya ya ke".

Ai banji kunyar ba kuwa na tashi ta saman bene ina hangosa,don daman baba na ya bamu mukulli muka haye saman,babu hayaniya babu komai...... .✍🏿

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿
[23/09, 16:30] Miss Green🍀: *🏮ABIN CIKIN ƘWAI🏮*

littafi na 3

*by✍🏿*
Ummu maher(miss green)🍀

Wattpad user name
Rabiatu333

Arewabooks
rabiattu0444

*SIRRINKI👂🏻*
Chapter 55 · 0% Book details