← Book details Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 63

Sashe 52

Abin Cikin Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda ire iren wannan ma na ce bazan auresa ba,to shima ɗin dai bai haƙura ba,yana nan yana naci amman naƙi bada fuska.

Ƴan huɗu fa sunyi girma ga baki chaƙwai2 sun san mahaifinsu sosai,don idan yazo nigeria har ya tafi suna wajensa.

Rannan na shirya zuwa gidan Anty Halisa.na saka wata doguwar riga ta atamfa ta amshe ni sosai matuƙa don yadda yanzu na ke na zama babbar mace sosai,komai zan zan babu namiji da zai kalleni ya share fatata ta yi luwai luwai.

Ina fitowa na buɗe sabuwar motar da Babanmu ya siyomin zan shiga,sai ga shinan ya fito da ƴan huɗu,ganin zan fita yasa suka runtumo da gudu zasu bini,ganin haka yasa ni kuma na figi motata fuuuuuuuu..... .✍🏿

07068606171

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*

1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huÉ—u N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda É—aya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya👇

0810 433 5144

Masu tura katin MTN👇

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huÉ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda É—aya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨

_*Miss green ce*_🤙🏿

[23/09, 16:29] Miss Green🍀: 87. . . . . . .88

. . . .sosai abin ya bawa Bilal mamaki wato har ƴaƴanta ma bata barsu ba,ka dinga ƙin ƴaƴanka saboda kana ƙin mahaifinsu,shi kuwa zai ga ƙarshen rashin kunyarta don xai yi maganinta.

Wani super market na fara sauka me mugun kyau da tsari,na shiga na wuce ɓangarensu biskit da halawa na fara siya saboda yaran anty Halisa,ina cikin siya sai naji kamar ana kallo na na tsargu na juyo.wani kyakkyawan saurayi na gani kusa dani wanda yafi kama da balarabe don wannan ko kusa bai yi kama da hausawa ba.

Saurin janye idanuwa na na yi daga garesa don kada ya gane ina kallonsa,murmushi ya yi ya iso kusa dani na juya masa baya na cigaba da siyayyata,naga wata alawa dasu Haidar keso na saka hannu xan ɗauka,shima ya saka nashi hannun da kallon kallo muka shigayo ni da shi.naji gabana yana faɗuwa sosai na yi saurin sunkuyar da kaina ƙasa.

Cikin harshen turanci ya ce"ya ke ma'a bociyar ƙwarjini da kuma ƙuruciya,zanso ki bani dama in taya ki siyayyar."sosai kalamansa suka daki zuciyata sam bana son ƙara fuskantar wata rayuwa dana miji,sai inga kanar bani da sa'ar wannan.

Babu yadda zanyi don mutum ne shi me mugun naci don haka na biyesa ma dai har na gama siyayyar.muka jera atare yana ta kallona sosai kamar zai haɗiye ni,ni wannan mugun kyaun nasa ne ma ya ke bani mamaki kamar ba mutum ba,i'na zuwa wajen biyan kuɗi na ciro atm card ɗina na miƙa shima sai ya miƙa hannu.

Ya basu nashi ya ce su ciri kuÉ—i ko nawa ne a abinda na siya.kallonsa kawai na ke ina mamakinsa,ya kannemin ido É—aya yadda yaya Bilal ke yimin.tuni naji gabana yana faÉ—uwa tun farkon fara kallonsa dana yi.

Da sauri na fito daga cikin wajen don bana son ya ƙara takuramin kuma.don ni wannan ma tsoro ya ke bani,murmushi ya yi ganin na fita sosai yaji mugun sonta na ratsa duk jikinsa ayanzu yana da shekara 29 aduniya,amman bai taɓa jin yana son wata ƴa mace ba sai yanzu gata baƙa kuma ba wata kyakkyawa ba amman sai yaji ta yi bala'in ƙwanta masa.

Da sauri ya riƙe hannun motar tawa ya ce"haba rayuwa ina kuma ki ke son zuwa ki gudu ki barni?idan ki ka tafi ina zan ƙara ganinki".?da sauri na zaro idona ina kallonsa,cikin tsoro na ce"Don Allah bawan Allah ka yi haƙuri ka kyaleni in tafi,na gode sosai da kuɗin da ka biyamin."

na faɗi hakan cikin tsoro don tsakani fa Allah ni tsoro ma ya bani.zama ya yi agaban motar tawa sannan ya ce"Ni sunana Shahid ni ba ɗan nan ƙasar bane,ni ɗan ƙasar masar ne uba na bature ne shi ɗan asalin england ne,mama na kuma masar kuma a masar ɗin aka haifeni,munzo nan gari ne ni da mamana wajen buɗe wani campany ɗina,mahaifina ya rasu tun ina shekara biyar,to yana da hannun jari sosai a ƙasashen waje ciki harda ƙasarku nigeria,to shine yanzu na buɗe wasu company a ƙasar nan,kuma ina jin daɗin zaman ƙasar ashe zan haɗu da rayuwata a garin?".

"Don Allah ki faɗamin sunanki don Allah,wallahi tun ganin farko dana yi miki naji kin masifar ƙwantamin don Allah ki yadda ki soni kamar yadda na kesonki please,Ammina za taji daɗin hakan sosai tun kafin in kai yanzu take son inyi aure wai saboda mu ƙara ahali,tasha haɗani da ƴaƴan ƴan uwanta amman haɗin bayz yiwuwa saboda sam basu ƙwantamin ba,amman ke kallon farko ki ka tafi.da rayuwata."

Da ƙer na buɗe baki na na ce"sunana Rahma amman anfi kirana da khairat.ni ba budurwa bace bazawara ce don ina da yara ma har huɗu".

Da sauri ya ce"wow nice name amman khairat baki yi kalar ƙarya ba,ta yaya zaki ce min yaranki huɗu?gaskiya ni bann yarda ko ɗaya ma kina dashi ba"?.ya faɗi hakan yana kallona yana murmushi.
Samun kai na yi a mai mayar masa da murmushin na É—akko wayata na buÉ—e hoton Æ´an huÉ—u na na nuna masa."Wow inason waÉ—annan yaran amman wannan macen tafi kama da ke?kuma yaya na gansu duk kusan kansu É—aya"?.

Murmushi na yi na ce"Æ´an huÉ—u ne yanzu shekararsu biyu da Æ´an kai."murmushi ya yi sannan ya kalleni kallon cikin ido sannan ya ce"gaskiya kin iya haihuwa Hayaty'nima haka na keson ki haifamin Æ´an 8 ma".sosai ya bani dariya,ya shagala yana kallona cikin nutsuwa na jiyo muryarsa yana ce wa"i lov u khairat".da sauri na kalles ya kalleni kallon cikin ido.

To Shahid dai sai da ya rakani har gidan Anty Halisa,da ya ke da body guad É—insa yazo don haka ya ce ya biyosa da motarsa.

Har zan fita daga motar sai naji ya ce"Hayatee".da sauri na jiyo jin maganarsa kamar sarewa.cikin shauƙi na kallesa.shima ya kalleni sannan ya miƙomin wayarsa ya ce"samin number ɗinki awayata".babu musu na amsa na saka mishi number na miƙa masa.murmushi ya yi sannan ya ce afito lafiya".nima murmushin na maida masa da sauri na shige gidan ina murmushi.

Halisa na falo tana saita agogon ƙaton falon nasu wanda ya goce,ta bayanta naje na rungume ta zata runtuma da gudu na kyel kyale da dariya sosai.ta ce"wayyo maman ƴan huɗu so ki ke in saki fitsari awando ko?"murmushi na yi na zauna ina ce wa"to yi haƙuri ina yaran nawa suna skull ko"?.

Murmushi ta yi sannan ta ce"eh duk suna skull me sunanki dai kin san tana gidan hajiya inpact ma ta koma cen da zama".dariya na yi sannan na ce"ai kuwa har can sai na bi taƙwara ta".sai kuwa Anty Halisa ta ce"a gaskiya khairat banji daɗin abinda ki ka yiwa mijina ba,don ya ce yana sonki sai kuma ki wulaƙanta min shi"?.

Murmushi na yi sannan na ce"mijin naki ne bai yi min ba".na faɗi hakan cikin zolaya dana ga taji haushi sai na ce"Anty Halisa bazan iya auren mijin ki ba ki yi haƙuri,ban cancanci in auresa ba sam,kinga na farko mijinki ne.na biyu abokin babansu haidar amini ma.ta yaya ki ke zatan zan auresa in lalata wannan zumuncin".?

"Haba khairat wannan fa ba uxuri bane,ai aure babu ruwanshi da wannan tunda dai sunna ce,amman ni banji daÉ—i ba gaskiya,yanzu ba gwara akawo maka wadda kasan halinta ba,?kina tunanin don haka ya faru ba zai nemi wata ba?to su maza ba haka suke ba,muddin suna son yin aurensu to babu shakka sai sunyi,khairat ina tsoron wataran a kawomin wadda zata tarwatsamin ahalina.khairat ina tsoron matan yanzu,don Allah ki amince masa".

Dafa kafaɗarta na yi na dinga batz haƙuri sannan na ce ta dage da addu'ah don ita kaɗai ce mafita.

Anan ma na ke bata labarin shahid ta saka dariya ta ce"inye wato balarabe shine ya yiwa mijina ƙafa ko?sosai taban dariya na ce"Anty halisa gaskiya inason shahid wallahi,ammanfa ni ina tsoronsa saboda kyaunsa ya yi yawa fa".murmushi ta yi sannsn ta ce"babu komai khairat tunda dai kina sonsa ki bashi dama ki gani,ai kinga ba zai yiwu ki yi ta zama babu aure ba ko"?.

Murmushi na yi na ce"haka ne insha Allah zan bashi dama,nan dai muka cigaba da hirarmu.

Tun daga ranar sai Bilal ya ƙwashe ƴaƴansa daga waje na suka koma wajen hajiya Ruƙayya,naso inyi magana mama ta hanani ta ce ai duk ɗaya ne,kuma nemsn magana ya je dani in kyalesa.itama maman na yi mata maganar Shahid ta yimin fatan alkhairi.

Na wuce sashen hajiya kaka mero ma na nan don yanzu ta ƙara haihuwar mace ƴaƴanta biyu kenan,na farkon namiji ne yanzu kuma mace.

Hajiya kaka ta kalleni sannan ta ce"yanxu khairat kin ƙwammace ki yita zama haka babu aure hakan kuwa xai yiwu?.ni wallahi idan gaji zan yi wa malik magana kawai anemo wani a ƙauye a haɗaku nima in huta."

Da sauri na kalleta na ce"haba kaka har yanzu fa shekara ta 23 ko da biyar ban kai ba,sannan sai awani fara yimin zancen aure,auren ma da ɗan ƙauye?ai kuwa ba zai yiwu ba".mero ta ce"maman ƴan huɗu yasin kada ki yarda haka kawai."

Muka saka Hajiya kaka agaba da tsokana.da ta gaji ta saka radionta akunne ta barmu muna ta hirarmu da mero,sai ga yaya Salim bayan mun gaisa na tashi zan tafi sai naji hajiya kaka na ce wa"ah lallai Salim ka samu dama yau fa ina kallonka ka shigo wajen nan yafi sau biyar,me ka ke nufi?to ni dai ba dani ba wallahi ka É—auketa ku tafi daman.ba zai yiwu kuzo ku sakani gaba ba kuje cen kuyi shaiÉ—ancinku."

Dariya na yi na fita Yaya Mukhtar na gani yasha mur ya wuce,ni dariya ma ya bani don tun bayan mutuwar aure na ya takuramin akan na aures na ƙi to shine fa yanzu har da gaba.
Chapter 52 · 0% Book details