← Book details Abduljabarr Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 14

Sashe 3

Abduljabarr Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bici taƙe ci, junainah turo baki tayi gama, "Dada shine kika ki jira nah muci tara"
Jan ƙujera tayi ƙusa da Dada ta zauna, ƙullan abincin ta janwo, yanda zata iya ci ta Ɗiba tafara ci bawan da ya kara yin magana
Suna gama wa junainah ta tatara pelet da kullan taƙai kitchen

dawa falon tayi Dada na zaune a kan ƙushin
"Dada zan shiga gidan su Hibba"
Toh ki gaishe min da Mom,ma É—in.

Ɗakin,ta ta shiga ta ɗauki Hijabin ta da lollipop ɓoyewa tayi a shikin hijabi kar Dada tagani.
Salaman Dada tayi "sena dawo Dada"
Kai kawai ta É—aga mata

A nese take takawa har ta i,sa ƙofan gidan tura ƙofan gidan su Hibba tayi tayi sa,a abuɗe yake
Baba me gadi yana zaune a kan ɓenci hannu sa rike da radio ya najin programm da ake gaba tarwa "Baba mun tashi lafiya"
Washe baki yayi da fara'a ya amsa
"Alhamdulila Æ´ar Dada kina lafiya ya maman naki Tana lafiya"?

"Lafiyan mu Baba"
Masha Allah, kizo duba Amini yanki Hibbatu ko?
"Eh ta amsa ta wace dan inta biyema Baba me gadi yadinga yi mata tan baya ƙenin.

Babba gida ne me É—auke da ban gare biyu É—aya yafi girma gidan ya kawatu da flowers ko ta ina a zagaye da gidan ga wajan peaking na Mota shima gon abun kallo ne, gidan ya haÉ—u iya haÉ—uwa.

Kan ta saye ta nufi cikin gidan, batare da wani far gaba ba
Tana É—ago kanta ta hango su
kirjin tane yayi wanni irin buga wa dafe kirjin tayi taji yanda yake har bawa kaman zai rabu da gangan jikin ta, "Innalilahi" kawai take ta nana tawa a ranta.

Abduljabarr ne da Abokin sa, Suna zaune a side nasa
ÆŠauke Kanta tayi ta kara sauri dan kar ya ganta, side na su Hibba ta wace ciki da sauri.

Falo ta faÉ—a ko salama bata yiba se sauki ajiyan zuciya take yi

Mom'ma da Hibba ne zaune a falon suna hira, ganin Junainah kawai sukayi kaman a jefota ciki falon.

Mom,MA ne, ta kalli ta "lafiya junainah, Naga kaman aƙwoi a bunda ya soratar da ke" .

Kanta ta Sosa "babu Mom,ma".
okay
Hibba ne tayi Dariya, ta ce, "mom,ma yazo haka karki sha Mama kin wata kila, My lion tagani shine take godu"

Mom,ma ta juyo gwon Hibba, da alaman tan baya "Toh ita kuma meya hada su teke godon sa"?
Hibba tace "lefi tayi.
Mom,ma ta waiga gon Junainah ta kafeta da ido "lefin me kika yi da kike soron haÉ—uwa da Abduljabarr?
Toro baki tayi bata bata amsa ba
Hibba ne ta amsa ma mom,ma "last week ne muna saye a kwofan gida ta rakoni, se muka É—an saya muna hira, shine ta fara sana'an ta na Sosan lollipop namata magana taki bari"
Shiku ma Ya dawo kenan, Yagan ta tana tsotson lollipop akan hanya, shine fa yayi mata faÉ—a,
Ya ce "inya kara ganita da Menti seya yanka mata baki"

Dariya mom,ma tayi "Ai kowa da mun huta da wanan jara beben son lollipop É—in nan" se kace sha zumam,
Kwoda yake Ba lefita bane, Shi ya koya mata sha, dan haka shi ze hanata"
Mekewa tayi ta wace bedroom nata .

Junainah juyama Hibba baya tayi
Dan taji haushin Hibba data fa É—ama mom,ma lefin ta
Hibba Masowa tayi inda junainah take zaune kamo hannun ta tayi da alaman lalashi
"habba my aunty fuci kike yi dani,dan nafaɗa ma mom,ma a bunda Husband.. to be naki yayi miki, Shine kiƙe fushi dani" kara faɗada murmushin ta tayi ta kwonta a jikinta tace "ayi hakuri kawa na kar ya ɓal'lani dan nataba masa mata".
Tana murmushi da ganin yanda Junainah ta roÉ—e a lamun soro ya baiyana a fuskan ta

Junainah juyuwa tayi da sauri har jikin ta na ɓari tana fiskan tan Hibba
"Dan Allah Hibba kibar wanan maganan ki rufa min asiri Kar kina wanan maganan ya shigo, ki jamin jarfa
Kinsan Hali sa da miskilaci sa.
kwou da kanta tayi gefe cikin tsanyin murya tace, "Matan da suka fini Class ma be kulla suba ɓare ni"

Dariya Hibba tayi "Zanso naga ranan da
My lion Ze furta miki kalman yana son ki inga yaza kiyi
Inda kike soran sa nan, ko Azara'illu albarka"

Da sauri junainah Ta rufe mata baƙin, tana jijjiga kanta gaba ki ɗaya ilahirin jikin ta rawa yaƙe yi dan ta firgita da maganan Hibba
"Hibba kina cikin hah yacin ki kowa? Kifini sanan ƙwoda mata sun kare a duniyan nan, Brother bare taba cewa yana so naba, Dan kin san wusiyan rakumi yayi nesa da kasa, sede hange daga nesa.
Dan Allah Hibba kibar wanan maganan kisan brother Abduljabarr, ba Abokin wasanmu banne,

Mikewa tayi tana kallon Hibba "Dama 2days ban ganki bane Nace bari na dubaki ko lafiya"
Tonda naga lafiyan ki
nizan koma gida

Hibba ta tamke feska tana bin Junainah da kallon tuhuma
"Nikam Junainah me yasa baƙi sakewa da my lion ne?
kode baki É—au kesa a Masayi É—an uwwan ki bane?"
Naga kwoda yaushe, da zaran kin gansa, rasa Nisuwan ki kike yi, meya sa?
Why? Kwode yana miki wani abune wanda mu bamu saniba"

Girgiza Kai junainah tayi alamun babu
Hibba ta tabe baki tana kara zuba mata idanu wanta tana neman karin bayani "Toh Mene masalan da yasa baki sakewa da shi?

Kinga tashi ki rakani, kinwani sareni da Tan bayoyi sekace a Lahira muke.
Mikewa tayi Muje tonda ko gaisawan ƙerki bamuyi ba kindage tafiya zakiyi.
Sekace gidan yau kika fara zuwa

Nide mutafi tonda naga lafiyan ki
"Bari na salame mom,ma" Shiga ciki bedroom na mom,ma tayi sukayi salama.

Hibba rike da hannun Junainah tana murmushi "ƙawa nah muje na rakaki har gida" Haraban gidan suka fito suna tafiya Hibba na sokanan ta.

Sukaji murya daga side na Abduljabarr ana faÉ—in "Hibba yau ba gaisuwa ne" muryan Faruk ta jiyo
Da murnata ta ce, "LA yaya Faruk yashe kazo ban saniba"
Hanun Junainah ta sake Karasawa tayi gwonsu tana faÉ—aÉ—a murmushin ta yaya faruk "barka da war haka"
shima murmushi ya yake yi kaman sabon ango.
Amsa wa yayi da "barkan ki de Hibba" ya gida?
"Gida lafiya yaya faruk"

Abduljabarr ne Ya É—ago yana kallon Faruk yanda yake wage hakworan sa, girgiza kai kawai Abduljabarr yayi

Hango ta yayi tana tsaye a side nasu mom,ma hannu ta a cikin hijabin ta
Murya ya buÉ—e, ba alaman wasa a fiskan sa, yace, "keee"
juyowa Junainah tayi Tana kalonsa
"zonan yace da ita, idanun sa ya zuba mata yana binta da kallo

A hankali cikin nisuwa ta fara takawa har ta i,sa gwonsa.
tamke fuska tayi ta kwouda kanta gefe tana magana "Munwuni lafiya brothe Jabarr"
Daban kiraki ba zaki gai,she nine Mara kunya.

Tura baki tayi idonun ta sun kawo kwola .
"Walahi kika kuskura hawaya nan suka zuba, sena koya miki hankali, mara kunya kema kina ganin kin girma ko"?
Mika mata hanu yayi, alamun tabasa .

Zaro ido tafara, jikinta yafara rawa .
"Bakomai brother Jabarr"
Zaki bani ko saina tashi. a,a ba seka tashiba, zan baka muryanta na rawa
Runse idamu tayi kaman wanda za'a zarema rai, ta Mika masa lollipop ɗin da taƙe ɓuyewa a hijjabin ta .
Nan take hawanen da Take rikewa yazubo.

Sayawa yayi yana kallon ta yanda take hawayin kaman ya ɓuge tane a buma mamaki yabasa, yanda akan lollipop tana ƙuka
Karba yayi.

Da gwodo ta bar gidan ko jiran Hibba* bata yiba tana kuka
"My lion kaga kasata kuka ko" tafaÉ—a tana turo baki itama kaman zatayi kukan.
Hararan ta yayi .And so what tayi kukan jini mana intaso.

Bata rai Hibba tayi tace "Ai ba lefita bane ƙai,ne ka koya mata sha"
mom,ma Tace "ton tana karama kaika ƙe bata,
ko an hanaka Seka bata abuye, dan kawai kasata farin ciki.
Yazu kumma kace sedai tadena sha"

Dariya Faruk yayi "Hibba kice dama faÉ—an na soyaya ne" ai kuwa abun ya kayatar.
Abduljabarr mekewa yayi a zabure ya ddaka mata sawa, Wanda ya firgita ta .
"Hibba Yaushe nafara wasa dake haka,
kodon kina ganin dariya na shine reni yafara shiga sakani mu" ?

Rasa abuyi tayi gashi ta firgita da yanayi sa dok wani zati da kiran karfi na jikin sa ya bayana dan inya rike ta sede a haifi wata, dan nata ya kare, rungome shi tayi ta fashe da ƙuka.
Cikin shesheka kuka tafara basa hakuri . "I'm sorry brother* baran sakeba" jikinta se rawa yaketayi
"Sakeni" yace.
dan Allah kayi hakuri .

Naji ki sakeni ya cikin kwoshin murya me amun sauti yayi magana .
Sakesa tayi da tsauri ta bar gon ta kwoma cikin gida
Faruk Ne Ya bata rai dan yaji zafin yanda ya ɓatama Hibba rai.
"Abduljabarr kai wani irin muton ne Meya sa kasa Hibba, nah ƙuka kai?
kanada masala walahi.
A Magana nan me abun bacin rai,
Wada har kana mata sawa da tada jijjuyoyi wiya kaman da sa,anka kake magana!
nikam baji DaÉ—in hakaba .

Kozaka rama Matane, Naga yanda kanata bude mata hakora Solon kajama kanka raini katoh da kai.

Ina ruwan ka dani ta renani mana meya shafeka da haka
Taɓe baki Abduljabarr yayi ɓece komaiba

Junainah gida ta koma tana kuka
Dada ne Ta tare ta tana tanbayan ta me yake faruwa kika shigo da kuka
"Ba wancan É—an sa idon bane"
Meya miki dan ta gane wa take kwotan ce
Shine ya Kwoce min lollipop nah yayi.
Murmushi Dada tayi tace "Allah shi kara ai gwonda daya kwoce, nida kaina zan Sashi ya zane ki inyaga Minti a Hanuki
tonda bakiji"

Shiga ÆŠaki tayi ta cigaba da kuka

Washe gari junainah da Zazabi ta tashi Sakama kun kukan da tata yi dan Abduljabarr ya ce mata mara kunya.
Dada ta bata Panadol tasha ta koma baci

Hibba taji junainah. Shuro
Yasa ta shiga gidan su ta duba ta dan tunda suka rabu jiya tana kiran wayan ta bata É—auka.
Chapter 3 · 0% Book details