← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 41

Sashe 8

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana cikin kiran sallar asuba Sehrish tafarka a hargitse tana faman dafe saitin zuciyarta dake yi mata wani irin raÉ—aÉ—i, sai faman ambaton sunan Allah take yi, tabbas ranta na bata cewa wani mummunan abu ya faru dasu Jahad, cikin hanzari ta sauko daga saman gadon tana faman zagaye É—akim kafin daga bisani ta shiga cikin toilet ta É—auro alwala,
  Fitowa tayi ta nufi wardrobe ɗinta, hijab ta ɗauko da darduma ta shimfiɗa, ta shiga jera sallah, bayan ta kammala ta zauna tare da ɗaga hannayenta sama tana addu'o'i akan su hosana da jahad da sauran al'ummar musulmai, ta jima tana addu'ar kafin ta koma saman gadon nata ta kwanta tana fuskantar sama abubuwa iri iri na zuwa mata aranta daga bisani bacci ya kwashe ta, bata sake farkawa ba sai ƙarfe 10 na safe,
Firgit ta farka har time É—in shiga kitchen ya wuce,
  Zumbur ta miƙe shaf shaf ta shirya cikin shigarta ta maza da ta saba, saboda zullumi bazai barta ta fita a matsayin mace ba, a hankali ta tura ƙopa ta fuce izuwa kitchen,
  Bin ta da kallo azmee tayi wadda ke gyara kitchen don harta kammala breakfast ɗin already tun ɗazu,
  Da mamaki tace"Sehrish ya akai naganki kuma da shigar maza?
   Shiga ciki tayi tana cewa "Aunty azmee ni tsoro nake ji Allah,"
   "Wani irin tsoro kuma,ba wani tsoro abunda nake so dake bayan mun kammala jera abinci, sai ki koma ɗaki ki cire wannan gashin bakin ki sauko da gashin kanki zan kira ki, sai ki fito a matsayin mace" 
Shiru tayi tana kallon yatsun hannun ta kafin tace "shikenan Allah yasa komai ya tafi adai dai,

Murmushi azmee tasaki tare da jinjina kai tace"Insha Allah yanzu bari na fara jera miki warmers É—in kina kaiwa dining,"

  Ta amsa mata da "toh", tana jin ɗar axuciyarta

  Cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala jerawa, Ayaan da Jahan ne suka fara fitowa sanye cikin kakinsu gwanin kyau, Suka samu wuri suka zauna kusa da Juna, azmee ta soma saving ɗinsu, time ɗin sehrish ta shige bedroom ɗinta don ta kimtsa kamar yadda su kayi da azmee zata fito a matsayin mace,
Bayansu sai kanal yusif ya fito shima sanye da Jallabiya launin ruwan toka, wuri yasamu yazauna yana gaishe da aunty azmee, da fara'a take amsa musu, cikin girmamawa su twins suka gaishe shi shima ya amsa musu daga bisa ni kowa ya mayar da hankali kan breakfast É—insa,
Sehrish na cikin ɗaki cike da zullumin yarda za'ae ta fito a matsayin mace, tana a jikin ƙopar ɗakinta tana ruƙe da handle ɗin kopar cike da fargaba,
Gyaran murya azmee tayi ta É—an É—aga murya tare da kwaÉ—awa sehrish kira da sunanta tace "Sehrish ki fito mana,"
Jin sunan da azmee ta ambata yasa su kallonta da mamaki, sake maimaitawa tayi "Sehrish ki fito nace,"
Kallon juna Ayaan da jahan su kayi sannan suka kalle ta atare suka haɗa baki wurin cewa "Wanene Sehrish kuma? Kanal yusif shima cike da mamaki yake kallon azmee jin sai faman kwala kira take yi, zuba ido su kayi don suga wanene wannan sehrish ɗin da Azmee ke faman kira, shin baƙo su kayi ne a gidan nasu ko kuwa?
buɗe ƙopa sehrish tayi gabanta na faɗuwa ta tunkaro hanyar dining area ɗin, jikinta na kerma a tsorace take tafiya,
gaba ɗayansu suka ɗago suna kallon ta tun kafin ta idasa bayyana a area ɗin da suke, bin ƙafafunta su kayi da kallo waɗanda ke sanye da ƴan silifas ɗinta na gado, sai faman kerma yatsun ƙafarta suke yi,
Time ɗin da sehrish ta idasa fitowa a raxane jahan ya miƙe tsaye, ayaan kuwa baisan lokacin da ya saki cokalin dake hannunsa ba ya faɗa cikin plate ɗin dake agabansa, kanal yusif kuwa kallon abun yake kamar a mafarki,
Bin ta suke da kallo cikin mamaki, kamar a mafarki suke kallon lamarin, ƙarasowa tayi ido a zazzare jiki na kerma, riga da wandon nan ne ajikinta , ta cire gashin bakinta, ta kuma zuba da doguwar sumar kanta har gab da waist ɗinta, ta fito asalin macen ta Tsaleliyar budurwa ƴar matashiyya,
A rude jahan yace "Azmee who's she ? daga ina ta faÉ—o cikin gidan nan? Da iznin wa!?
Ayaan kuwa cewa yayi "Ku kuke ganin mu bamu muke ganin ku ba ! Wannan Hurool ainin fa? daga aljanna ta gudo?
Kanal yusif sam yagaza magana bayani kawai yake jira daga wurin azmee, ita kanta azmee ta É—an razana da reaction É—in da suka bayar, Sehrish kuwa a gefen azmee ta tsaya tana faman zare ido,
"Azmeee Explain !!!!' jahan ya faÉ—i azafafe harda dakar table É—in gabansa da tafin hannunsa,
Murya na rawa azmee tace " Kuyi haƙuri dan Allah...Am wannan da kuke gani ba kowa bane face Tukur mai aikin ku, nasan zakuyi mamakin hakan......
Dakatawa tayi ganin yarda Ayaan da kanal yusif suka miƙe atare, cike da ruɗu Kanal yusif yace "What ! Wai wane tukur ɗin ake magana ! Ba dai wannan yaron mai aikin namu ba, kina nufin dama mace ce ba namiji ba ....? Ya tambaya hankali atashe ,
Daga sehrish har azmee sun tsorata,
Hannu jahan yasa yasake bugun table É—in abincinsu yace "Impossible bazai ta6a yiyuwa ba ! muddin kuwa hakan ta kasance dole yarinyar nan ta fuskanci hukunci mai tsanani kuma tabar gidan nan ayau É—in nan,
Fashewa da kuka sehrish tayi saboda tsorata da maganar Jahan gashi idonsa na akanta ya zare su,
"Dan Allah ku kwantar da hankalin ku, laifi ne nasan ta aikata amma kuyi mata afwa, sam bata da niyar cutar da kowa.....' dakatar da ita Ayaan yayi da cewa "Ba wannan zancen ! Saboda ƙarfin hali irin na Yarinyar nan, tayo shigar maxa ta saje acikin mu tana mana aiki, babu sirrin mu da bata sani ba, babu irin firar da bama yi agabanta, har yawo muke yi da towel a ƙugunmu, muyi yawo da gajerun wanduna duk idonta na akai, kaf ta haddace ashe kallon mu kawai take yi,"
bil'haƙki ayaan yake kora bani, gaba ɗayansu ba komai suke ji mawa ba face yadda sehrish ta saje A cikinsu matsayin namiji na tsawon lokaci tana masu aiki, duk a tsammaninsu namiji ne ashe maca ce, tagama sanin sirrinsu saboda babu irin firar da basa yi agaban ta, sannan babu irin shigar da basa yi suna yawo duk a idonta,
Hannu Jahan yasa yana ƙoƙarin zare belt ɗin wandonsa da nufin ya jibgi sehrish saboda yafi kowa fusata, gashi dama su Mace bata agabansu balle suga kyanta ko wani abu haka don su tausaya mata,
A tsorace sehrish ta ƙanƙame kanta ta 6oye abayan aunty azmee tana faɗin "Nashiga uku ! Dan Allah aunty azmee ki basu haƙuri, kada su buge ni...zan tafi nabar musu gidan,
ture kujerar gabansa yayi gadan gadan ya tunkari sehrish zai jibge ta,
Kamar daga sama suka ji Muryar Abban su yace "Kada ka kuskura ka ta6a ta!'
Atare suka É—ago suna kallonsa kowannan su na huci,
Ruƙe yake da hannun junaid cikin nasa, yana sanye da jallabiya junaid kuma na sanye cikin riga fara da wando baki, ya tsorata da ganin halin da sehrish ke ciki gashi kuma yayi mamakin ganin ta ta bayyana kanta a matsayin mace, ga kuma jahan tsaye ruƙe da belt wato zai jibge ta,
Idasa isowa sukayi inda suke tunkan abbansu yace wani abu Ayaan yace "Daddy dama wannan yaron tukur mai aikin gidan mu mace ne ba namiji baa !!
murmushi Abbansu yasaki yana kallon su yadda duk suka zabura,
Mayar da idonsa yayi kan Yarinyar dake 6oye abayan azmee yace "Ke zonan,"
"Sehrish ki fito Abbansu na kira,"
Azmee ce ke tunasar da ita, fitowa sehrish tayi jiki na kerma ta ƙarasa inda Abbansu yake tsayawa tayi at front of him murya na rawa take faɗin "dan Allah kuyi haƙuri ku yafe mun, nasan nayi laifi wlh ni banzo da niyar na cutar da kowa ba.....'
tsawa Jahan ya daka mata da cewa "Rufe ma mutane baki kona zo nan na nakaÉ—a miki shegen duka,"
Abbansu yace "Ya isa haka Jahan, bana so kowa yasake magana," shiru su kayi gaba É—ayansu suna sauraron mai abban nasu zai ce,

Shin ina haroon duk wannan abun dake faruwa yana a tsaye fitowarsa kenan, gaba ɗaya ransa ya gama jagulewa mamakinsa yarda akai yarinyar ta bayyana kanta A matsayin mace bayan bai idasa cimma burinsa ba, na tsoratar da ita, Amma ganin yadda su Jahan suka fusata yasa shi jin daɗi aransa burinsa karsu amince su tada 6alli sai anyi mata horo sannan a koreta shi kuma zaiyi amfani da wannan damar wurin ƙuntata mata,

tsayawa yayi da murmushin mugunta a fuskarsa don yaga ya ƙarshen bada'ƙalar zata kaya,
Daga shi sai gajeran wando fari ajikinsa tsaye ruƙe da ƙugu, ɗayan hannunsa na ruƙe da Brush da alama ma daga toilet ya fito,

burinsa yaji mai Abban nasu zai ce,
gyaran murya Abbansu yayi sannan ya soma cewa "Na riga da nasan komai game da yarinyar! Domin junaid ya jima da sanarmun komai agame da ita, duk abunda junaid ya nuna yana so aduniyar nan koma menene shi zan amince dashi, Junaid ya nuna cewar yana son Zaman yarinyar nan agidan nan, don Haka Na AMINCE masa,!"
Cikin mamaki suke kallon abban nasu, Haroon kuwa tuni yayi wata irin raxana har Brush ɗin dake hannunsa ya faɗi ƙasa sbd jin abunda Abbansu yace,
Murmushi kawai junaid ke saki, kallonta Abban su yayi tare da cewa "Ya Sunan Ki"? Sehrish dake tsaye agabansa idonta cike tab da kwalla duk ta tsorata murya na rawa tace "SEHRISH"
Jinjina kai Abbansu yayi tare da sa hannun shi ya shafa gefen fuskar sehrish yace "Daga yau Ba sunanki Sehrish ba,"
cikin mamaki suke kallon Abban nasu, itama sehrish É—in kallonsa take tana jira taji sunan daya canza mata, azmee kuwa Alhamdulillah kawai take faÉ—i aranta,
"Kinsan menene sunan ki daga Yau"? abban nasu ya faÉ—i yana kallonta,
Cikin sanyin murya Reesh tace "a'a".
murmushi Abban nasu yayi sannan yace "daga Yau sunanki *SEHRISH SALAHUDDEEN HUSSEIN ABBAN SOJOJI*"
😇😇😇

Sakin baki su kayi suna kallon Abban nasu
Chapter 8 · 0% Book details