Sashe 28
Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayan sun fito daga motar kai tsaye suka nufi hanyar da zata sadaka da babban falon gidan, Sehrish sai faman bin ko'ina take da kallo aranta tana cewa"tab ! Mace ta samu wannan amatsayin gidan aurenta, ae kawai ta bi mijinta sau da ƙafa, tabi da addu'a don ni gaskiya na mallaki wannan hamshaƙin gidan amatsayin gidana, ko ƙofar gida bana leƙawa sai in ta kama,' sai faman zancan zuci take yi har suka ƙaraso wurin wani bene mai kanannaɗa, hawa junaid yayi sannan azmee tabi shi, itama sehrish tabi bayansu, sai faman jinjina kai take yi tana cewa"lallaine Aljanna ta mai rabo ce," daker take tattaka matattakalar benen saboda gajiya don yana da ɗan tsayi, bayan sun kai ƙarshensa, wata haɗaɗɗiyar ƙopa ce wadda kai tsaye in ka bi ta zata sauke ka upstairs inda main falo ɗin gidan yake, key junaid yasanya yabude ƙopar sannan suka shiga cikinsa,wurin ya haɗu an ƙawata shi ahaka ma wai ba furnitures acikinsa, to inaga ansanya mashi kujeru da sauran abubuwan ƙayatarwa, Batare da 6ata lokaci ba, sehrish ta buɗe handbag ɗinta, memo ta ciro tare da biro, junaid da azmee suka dunga dudduba falon suna karanto mata abunda za'a buƙata acikinsa, ita kuma tana rubutawa acikin memo ɗin hannunta, bayan sun gama da falon kaf sun lissafa duk wani abu da za'a sanya mashi, Sannan acikin babban falon akwai bedrooms guda biyar ƙofofinsu na acikin falon, ciki suka shiga suna dudduba ɗakunan masu girman gaske, nan ma azmee ta faɗa ma sehrish duk abunda za'a buƙata na furnitures ta rubuta, daga nan kuma suka sauko downstairs stairs shima bene ne zai biyo dakai ƙasan, Agajiye sehrish ta kalli junaid tare da cewa "dan Allah wannan wane irin gidane haka junaid? Nafa rikice wlh, mun shigo ta Upstairs yanzu kuma ga mu a downstairs yanzu ta ina zamu bi mu fita? Ba dai sai mun koma upstairs ɗin ba don wlh ƙafafuna a sanƙare suke hawa stairs ko wahala, Junaid da fuskarsa tayi jawur ya gama cika ya 6atse saboda uwar yunwar da yake ji, ga gajiya duk ta baibaye shi, daker ya iya cewa "wannan ne damuwarki, Ni ta cikina nake yi yaushe har muka kammala muka koma gida ni daga nan ma, ba abunda zan ƙara yi Allah, ku je ku ƙarasa sauran aikin in kun kammala kuyimun magana," Wuri yasamu a sitting room ɗin dake a downstairs saman wani benci ya zauna, da alama tun lokacin da akayi ginin gidan aka barsa, don akwai tarkacen kayan aikin da aka bari acikinsa, Acikin sitting room ɗin akwai ƙofofin bedrooms guda biyu, sai kitchen mai girman gaske, sunsha aiki kaf sai da suka zagaye gidan bayan sun tabbatar sun bincika ko'ina sun dudduba abunda ya dace duka kaf sehrish ta rubuta a memo ɗinta, Ana cikin kiran Sallar magrib suka bar gidan kowa agajiye, Suna ƙarasawa gida daga babban falon kowa ya wuce ɗakinsa, shaf shaf junaid ya tu6e kayan jikinsa ya faɗa toilet donyi wanka, haka itama sehrish tana shiga ɗakin nata bayan tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado tare da memo da biron duka, kai tsaye ta tu6e Jalbab ɗin dake ajikinta, ta cire rigar jikinta, cikin sauri ta faɗa toilet wanka tayo tare da Alwala, tana fito ta ɗaure da towel ta bude wardrobe ta ciro wata doguwar rigar mara nauyi ta zura, daker tasamu tayi sallah bayan ta kammala ta baje saman gadonta, bata ƙara sanin meke faruwa ba sam ta manta da batun jera abinci adining, gana babban yaya da zata kai mashi bacci kawai take kwasa, Azmee ce kawai tayi ƙoƙarin fitowa bayan ta canza kayan jikinta, tunda ta leƙa tasamu sehrish na jan minsharin wahala, bata tashe ta ba kitchen kawai ta wuce ta shirya masu abincin dinner ɗinsu ta dunga kaiwa a dining tana jerawa harta kammala, Daker junaid yasamu ya fito sai da yaci ka cikinshi sannan ya wuce masallaci yin sallah, Sai bayan sallar isha'i sannan sehrish tafarka tana faman zazzare ido, agogon bangon ɗakinta ta duba kusan ƙarfe goma da rabi cuf, arazane ta miƙe tana faman dafe ƙirji tuna cewa bata kaima SGR dinner ɗinsa ba, cikin sauri ta ɗauko mayafi a wardrobe tayi lagensa a kanta, sannan tafito dakin azmee tafara wuce wa don taji ko takaimasa, kwankwasawa tayi sannan ta jira ta buɗe mata, A lokacin azmee bacci takeyi jin bugun ƙofar sehrish yasanya ta, farkawa daga baccin nata, tasowa tayi ta buɗe mata ƙofa, Ganin sehrish yasa ta cewa "ashe kin tashi daga baccin? Lafiya naganki ko akwai wani abune? Sehrish tace "dama babban yaya na manta bacci yaɗauke ni ne, bankai masa ɗina ɗinsa ba, shine nazo na tambaya naji ko ankai masa," Azmee tace "Ae basu kai ga dawo cikin gidan ba Shi da Omar, pls kada ki koma bacci ko kuma ki sanya alerm na wayarki in sun dawo ki tabbatar kin kai masu abincinsu, sannan kada ki manta ki bama Omar list din da mukayi masa acikin memo dinki,' Sehrish ta amsa mata da cewa "to shikena insha Allah zan bashi, mu kwana lafiya," Tayi ma azmee sallama sannan ta fito ta wuce nata ɗakin, gefen gado tasamu ta zauna sannan ta miƙa hannu ta ɗauko handbag ɗinta, wayarta ta ciro daga ciki sannan ta shiga dannata, Tunawa tayi da maganar Azmee da tace mata in zatayi amfani da data, wi-fi kawai zata kunna, Cikin sauri tasanya yatsanta ta janyo top of the screen din wayar ta, danna wi-fi ɗin ya kunnu, tsayawa tayi tana tunanin me zata fara yi da wayar yanzu, tana cikin tunanin nan taji ƙarar shigowar motocinsu cikin gidan kusan ƙarfe 11-30 na dare, mayar da wayar tayi saman bedside drawer ɗinta ta ajiye asamanta, miƙewa tayi tana jiran su kammala shigowa sai taje ta kai masu, sai da tabari 12 tayi dai-dai a lokacin tasan sun kimtsa kowannansu na a bedroom ɗinsa, Sannan ta fito ta wuce kitchen ba ƙaramin daɗi taji ba ganin azmee ta kammala zuzzuba musu komai na dinner ɗinsu, a cikin tray guda biyu ta jera masu asaman table na kitchen ɗin, Hannu kawai tasanya ta ɗauki tray ɗaya ta wuce dashi sashen marshal Omar sallama da ƙarfi tayi saboda yaji ta da kyau, kasancewar yana acikin bedroom ɗinsa bayan tajiyo Muryarsa yana amsa mata sallamarta ta, sai ta shiga cikin falon nasa ta ajiye masa tray ɗin asaman table, sannan ta fita cikin sauri tunawa da Memo ɗin da azmee tace ta bashi, bedroom ɗinta ta shiga ta dauko memon data bari asaman gadonta, sannan ta koma part ɗin nasa a lokacin har ya fito jikinsa sanye da jallabiya ash, wuri yasamu yazauna saman sofa fuskarsa ɗauke da ɗan murmushi ganin Sehrish, Ƙarasawa tayi inda yake tare da gaishe shi "Yaya Omar barka da dare, ya gajiyar aiki," ? "Alhamdulillah miss Sehrish, ya maganar aikin dana saku? Ina fata komai ya tafi dai-dai, sannan ya gajiya nasan kun kwaso ta ko? Murmushi tasaki tare da miƙa masa memo ɗin hannunta tace"Gashi nan, mun dudduba gidan duka kuma mun rubuta duk wani abu na furnitures da za'a buƙata acikinsa," Jinjina kai Omar yayi bayan yasanya hannu ya kar6a yana duddubawa yace "Very good, naji daɗi sosai gaskiya kunyi ƙoƙari, insha Allah zuwa gobe zanyi oder na duk wannan abubuwan da kuka lissafa ana buƙata acikin gidan, zuwa dai next week zan sake tuntu6arku," Sehrish tace "toh Allah ya kaimu lafiya," Har ta juya zata tafi ya kuma cewa "kina zuwa school ne? Ko baki fara ba? Sehrish tace"a'a ban fara ba, amma aunty azmee tace zan fara cikin kwanan nan," Omar yace "Owk, inaso ne suma yaran da nakeson kawo wa cikin gidan can, su fara zuwa school amma zan jira naga wadda zaki fara zuwa, in yaso suma saina sanya su amakaranta ɗaya dake," Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "mata ne suma? ta tambaya tana kallonsa a lokacin harya fara cin abincinsa yace "Eh ƴan mata ne, kyawawan gaske inason yaran sosai tun dana ganki sai na ga fuskarki tana koma mun irin tasu, nasan saboda son da nake masu ne da kuma kewarsu da nake yi,......' ya ƙarasa maganar asanyaye, Hakanan sehrish taji gabanta ya ɗan faɗi raaasss! amma batasan dalilin faɗuwar gaban nata ba, taso ta tambaye shi sunayen su amma tunawa da cewa ba ta kaima babban yaya abincinsa ba yasa ta saurin cewa "Allah sarki yaya Omar Allah yabaka ikon Kula dasu, yasa su zama alkhairi agare ka,' Ya amsa mata da "Amin," Sannan cikin sauri ta fuce ta koma kitchen sai da tafara haɗa masa yankakkun fruits acikin madai-daicin plate ta azashi asaman tray ɗin sannan ta fuce hannunta dauke da tray ɗin acikin babban falon suka ci karo da haroon wanda fitowarsa kenan daga part dinsu, night dress ne ajikinsa riga dai-dai guiwa, kawar da kanta tayi tare da miƙar hanya tana jiyo shi yana cewa "a rinƙa haɗawa da sallar dare ko an samu adace asamu shiga," Murmushi sehrish tasaki batare da tace komai ba bayan ta isa part ɗinsa da sallama tashiga, baya acikin falon nasa ƙarasawa tayi ta ajiye masa asaman table dinsa, sannan ta tattaka izuwa bedroom ɗinsa tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin nasa, sallama tayi masa amma shiru babu amsa hakan na nufin yana cikin toilet ko kuma bacci ya ɗauke sa ne, aranta tace "Allah yasa baiyi bacci ba," ɗan sa ƙafarta tayi cikin ɗakin nasa ta shiga ciki sai uban ƙamshi ke daker hancinta kamar wadda tashiga gonar turare, samun shi tayi baje a saman gadonsa daga shi sai Short ajikinsa, ji tayi gabanta ya faɗi rass saboda yadda surar shi ke ɗaukar idonta, sam tarasa me zatayi ta tashe shi don tasan dole akwai yunwa atattare dashi, kuma in ya tashi da safe yaga ba'akai masa abinci ba zai iya tuhumarta, Shawara ta rage ma mai shiga Rijiya, tana cikin wannan tsayuwar abakin ƙopan ɗaki nasa ƙafarta har ta soma rawa saboda gajiya da tsayuwa, Wani irin Juyi taga yayi daga saman gadon nasa gaba ɗaya ya tafi dukansa zai faɗo daga saman gadon, agigice sehrish ta watsa ciki da gudun gaske ta ƙarasa tare da kai hannu zata tarbesa sai gashi ya buɗe blue eyes ɗinsa kuma nan take yasanya hannusa ɗaya ya dafe ƙasan