← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 41

Sashe 34

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bayan wasu lokutta, duka baƙin da suka zo suka tafi gidan yayi tsit ba hayani, suna cikin wannan zaman na jimamin Ga samu ga rashi, na hajjaju da suka haɗu da ita yau, sun son itace kaɗai zata faɗa masu inda Sehrish take gashi itama tace bata sani ba, hakan ba ƙaramin kashe musu zuciya yayi ba, daker suka samu bacci ya ɗauke su,
_______________________

Fitowa daga wanka general ishaq yayi jikinsa sanye da gajeran wando, Closet É—insa ya nufa tare da sa hannu ya buÉ—e ya É—auko jallabiya ya zumbula ajikin shi, Sarai yasan cewa tana É—akin Amma sai yayi tamkar bai ganta ba, sai da ya kammala kimtsa kansa sannan yace "Ya Rashin Ji"? Ya tambaya yana kallon kansa acikin Mirror, mamaki ne ya kama aunty babba jin abunda yace, tana zaune daga gefen gadonsa tace "Nifa ce ba hafsat ba," ta faÉ—i tana kallonsa
Ishaq yace"Nasani ae, dake nake magana, duk rashin jin hafsat ae bata kai ki ba, kefa tamkar 6eran gida kike wurin 6arna da rashin ji,"
ɗaure fuska tayi jin abunda yace rai a6ace tace "Alamu sun nuna cewa ba kayi kewata ba ko? shiyasa kake gayamin magana, ko da yake dama kai ae ba ka iya soyayya ba, Iya ruƙe bindiga kaɗae ka sani,"
......juyowa Ishaq yayi yaÉ—an kalle ta tare da ta6e bakinsa yace "ban iya soyayya ba, amma gashi nan har kin haifi hafsat dani ko? Naga wannan ma ae wani sashe ne na soyayya,"
ya ƙarasa maganar tare da wuto wa ya haye saman gadonsa ya kwanta yana cewa "Idan kin tashi fita daga ɗakin kada ki manta, ki kashe mun hasken inaso nayi bacci,"
a ƙule aunty babba ke kallon shi, can kuma ta miƙe fuuuuu ta nufi hanyar fita har takai bakin ƙopar ɗakin ta kuma tsaya tare da juyowa tana kallonsa, abun mamaki sai ta same shi yana ta faman tiƙar dariya,
Bakomai yasa ta tsayawa ba face tsananin son kasancewa dashi da take yi,
dakatawa da dariyar yayi sannan yace "nifa ba korarki nayi ba, zaki iya dawowa kiyi zaman ki,"
murguɗa masa baki tayi aranta tace "shashasha dama nasani ae dole ka buƙace ni,"
shi kuma aransa yace "Mayya, Jibi yarda take ta hau hawa kamar buhun harawa, duk an cinye mun abincin gidana," 😂
Kamar taji mi yace ta É—an kallesa tare da jinjina kanta tace "bari na kawo maka Tea,"
"Ok i wll be waiting for u," ya faɗi yana faman yin dariya ƙasa-ƙasa, general ishaq kenan tamkar Abbansu haka yake indai wurin iya zolaya ne,

******************************
A 6angaren sehrish kuwa, sam taƙi bari bacci ya ɗauke ta sai faman gyangyaɗi take yi tana zaune asaman kujerar dake gaban mirror burinta kawai su twins su dawo ko tasamu ta kai masu abincinsu, sune kawai suka rage mata takai mawa, domin kuwa ta jima da kaima Abbansu nashi tunda ya dawo,

Basu tashi dawo wa cikin gidan ba sai wuraren ƙarfe Sha biyu da rabi suka shigo suka shigo cikin falon kai tsaye ɗakinsu suka wuce, shaf shaf suka shiga rage kayan jikinsu, sai da ya rage daga su sai shorts ajikinsu, sannan suka shige toilet donyin wanka, sun jima aciki kafin daga bisa ni suka fito kowannansu ɗaure da towel a waist ɗinsa, closet ɗinsu suka buɗe jerin kayansu ne ajere komai iri ɗaya, kamar yadda suke tagwaye haka komai nasu yake iri ɗaya, kimtsawa su kayi cikin sleeping dress riga da wando milk colour,
Chapter 34 · 0% Book details