← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 41

Sashe 40

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran ƙarshe da jahad ta kwalama hussana kafin ta sume har cikin zuciyarta taji shi tuni ta soma ƙoƙarin buɗe idanunta wanda ke cike da bacci, a lokacin har baba alamu yashiga da ita gidan gonarsa ƙopar katako ce ke gare sa tamkar ɗan gate, bayan ya shigar da motar ya fito ya rufe ƙopar gidan gonar da kwaɗon dake ajiki,
Sannan ya koma tare da buÉ—e murfin motar inda hussana ke zaune tana faman lullumshe ido alamar bacci bai isheta, so take ta buÉ—e Idonta taga ina jahad take amma sam bacci ya hana Ta,
hannu baba alamu ya zura tare da ɗauko hussana ya sa6ata a ƙafaɗarsa ya miki hanyar wata ƙopa inda ya dosa ya buɗe ta ya shige da ita ciki sannan ya sauke ta ƙasa har tana yin tangyaɗi zata faɗi, sai da baba alamu ya datse ƙopar ɗakin gam yadda bamai shigowa sannan ya juyo yana kallon hussana tare da washe waɗannan haƙoran nasa marasa saiti,
A lokacin Hosana ta dawo cikin hayyacinta baccin yabar jikinta, bin wurin tayi da kallo É—akine mai faÉ—in gaske babu komai aciki sai jarkokin ruwa da bulo bulo, da wani ajiyayen genarator tsoho, sai sauran tarkace, wurga idonta tayi akan baba alamu dake tsaye agabanta yana washe mata baki, nan take ta buga uban tsalle taja da baya tana faÉ—in "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un nashiga uku, Ina jahad take! Wayyo Allah na Me zaka yi mun meyasa ka kawo ni nan ! tayi maganar tana ja dabaya a tsorace
Baba alamu ya kashe mata ido É—aya tare da cewa "daÉ—i zan baki, kiyi shiru da bakin ki kada wani yaji mu, indai kina son ganin Æ´ar uwarki to ki bani haÉ—in kai muyi mu gama cikin salama,'
Yayi maganar tare da kai hannu zai shafa fuskarta a firgice taja baya tana girgiza masa kai atsorace take cewa "Dan Allah kada ka cutar dani, ka ƙyale ni bani da lafiya, idan ka ta6ani mutuwa zanyi," ta faɗi tana faman zazzare ido, ga wata irin zufa dake wanko mata dakyar take haɗiyar numfashi,
"Ba zaki mutu ba, bada zafi zan miki ba kaɗan kaɗan, in dai baki bani haɗin kai ba zan ƙwata ta ƙarfi kuma naƙi nuna miki inda ƴar uwarki take,"
Cikin kuka hussana tace "a'a nidai kada ka cutar dani bana so, kadaina matsowa kusa dani, wlh Allah bazai barka ba kuma yaya Omar ma bazai ƙyale ka ba sai ya kashe ka,"
fashewa da dariya Baba alamu yayi tare da gwalo ido yana mata gwalo yace "Wanene wani Omar kuma? babu kowa anan daga ni sai ke ! Kuma yanzun nan zan kawar da sha'awata tare dake," yayi maganar tare da yin kwakkwaran taku ya fusgo mayafin jikin husana nan take ya zame ƙasa, watsa wa tayi da gudu ciki tana kuka cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da bulo ƙafarta ta harɗe ta kife ƙasa gaba ɗaya.........................

dariyar mugunta baba alamu ya saki ganin abun yazo mashi cikin sauƙi, nan take ya shiga kwance zariyar wandonsa,
daker hussana take jan numfashi saboda buguwar da tayi wani irin ciwon kai yafar mata lokaci guda, jin motsinsa dab da ƙafafunta yasa ta dumbuzar ƙasa a hannunta, ta daddage ta tashi zaune tare da watsa mashi ita a fuska, nan take yashiga yin tsalle yana faɗin "kai ! Kai!! Kai !! Don ubanki ni kika watsa ma ƙasa a ido! aiko bazan ƙyale ki ba, saina wulaƙanta rayuwarki,
Jin hakan yasa hussana zabura tare da miƙewa tsaye zata gudu batayi wani aune ba taji yaja rigar jikinta nan take ta soma yage wa, juyowa tayi tare dasa hakoranta ta gartsa mashi Cizo, azaba da raɗaɗi suka sa shi sakin ihu, kuma hakan ya ƙara fusata shi, a fusace yabi ta tare da damƙo gashin kanta ya janyo shi da ƙarfi ta dinga sakin ihu tana kuka tana kiran Sunan Jahad,

Matse ta yayi ajikinsa tare da sa hannun shi biyu ya ƙarasa yage rigar jikin hussana gaba ɗaya, hankali a matuƙar tashe husana ta watsa mashi miyau afuskarsa biji-bijin daya daya fara gani ne yasa shi ɗan dakatawa, hannunta ta sanya tare da ingije shi da ƙarfin gaske gaba ɗaya baba alamu yayi taga² zai faɗi ƙasa,
Cikin sauri hussana ta tattare rigarta ta kare kirjinta da ita, hanyar fita daga É—akin ta nufa da gudun gaske tana kuka burinta kawai ta isa kopar ta buÉ—e ta fuce
tana cikin gudun nan baba alamu ya taso a matuƙar zuciye ya nufe ta da sauri yakai hannunsa tare da jan rigarta data rufe jikinta da ita, gaba ɗaya ya 6an6are rigar daga jikinta ya cire ta gaba ɗaya ya ruƙe a hannunsa,
Wani irin kuka hussana ta saki mai matuƙar cin rai ganin yarda ya cire mata rigarta, gashi ko brazier bata sanya ba, ƙirjinta gaba ɗaya sun fito, hannunta ta sanya ta tarbesu tana kuka kuma hakan baisa ta daina tunkarar ƙopar ba,

Bin ta baba alamu yayi da gudun gaske saboda ya ruƙo ta jikinsa don ya idasa nufinsa,
Sai dae ina kafin yayi wani kwakkwan yunƙuri tuni anyi ma ƙopar ɗakin wani irin kwakkwaran Naushi nan take katakon jikinta ya farfashe gaba ɗaya ta buɗe,
A tsorace baba alamu ya dakata yana faman zazzare ido don son ganin wanene wannan ya faÉ—o masa cikin gidan gonarsa !!!!!!!!!!!!
Ita kanta hussana ta firgita tsayawa tayi jikinta na wani irin kerma ga zazza6i daya lullu6e ta, har lokacin hannunta na tarbe da ƙirjinta,
Duro ƙafarsa yayi cikin ɗakin tamkar damusa wani irin kakkarfa ne mai ban tsoro, jikinsa na sanye da Jacket baƙa daga ciki kuma farar t*shirt ce wadda ta bayyana ƙirar ƙarfinsa, Sai dogon wando baƙi,
bai bamu damar muga fuskarsa ba domin kuwa tana sanye cikin face mask baƙi, idonsa kuma na sanye da baƙin glass,
gaban hussana ba ƙaramin faɗuwa yayi ba duk ta gama tsorata, baba alamu kuwa murya na rawa yashiga cewa "kai...Wai Wanene kai ! daga ina kake? Mai ya kawoka gidan gonata ! ya tambaya yana tada jijiyoyin wuya,
Har lokacin bai da alamar yin magana, a hankali ya sanya hannunsa tare da ruƙo jaket ɗin dake ajikinsa ya cire ta gaba ɗaya yayi wurgi da ita, sannan ya mayar da hannun nasa ya tu6e t-shirt ɗin dake ajikinsa ya rage babu riga ajikinsa,
Hankalin baba alamu ba ƙaramin tashi yayi ba ganin irin damtsen hannunsa a murmuɗe ga ƙirjinsa dake motsi abun gwanin ban tsoro,
tuni zuciyar hussana tayi wani irin bugu nan take ta tafi zata sulale ƙasa, da Hanzari ya tarbota jikinsa gaba ɗaya tafaɗa a faffaɗan ƙirjinsa,
hakan ya bashi damar zura mata t-shirt É—insa ajikinta donya rufe mata jikinta, bayan ya kammala sanya mata rigar,
ya buÉ—e bakinsa ta cikin face mask É—in yayi fito mai sautin gaske har saida baba alamu ya firgita yana faman kwalala ido,
Da gudun gaske wani Saurayi ya shigo ya tunkare sa, batare da yace komi ba ya miƙe masa Hussana, cikin sauri yasa hannu ya ɗauketa tare da azata a kafaɗarsa ya fuce da ita,
sai lokacin Yasa hannu ya cire glass ɗin fuskarsa tare da yin wurgi dashi, Azazafe ya sanya kyawawan idanuwansa waɗanda suka Canza Launi izuwa ja saboda tsananin 6acin rai, gadan gadan ya tunkari Baba alamu wanda ke shirin guduwa, hannunsa yakai tare da damƙar wuyan rigarsa ya ɗaga shi sama, ya dawo dashi ƙasa ya buga kansa jikin bulo nan take haƙora biyu daga bakin sa suka fito Jaga-jaga da Jini, saboda tsananin azaba da raɗaɗi ya sanya Baba alamun sakin futsari a wando yana cewa "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un na bani na 6atare na lalace nashiga uku, Dan Allah ka ƙyale ni wlh nabi Allah nabi manzonsa .,...........
tsawa mutumin ya daka masa tare da cewa "Kasan da Allah kake ƙoƙarin aikata ma ƙaramar yarinya faɗe tsofe tsofe dakai!! mutun mara imani da tausayi irinka wanda baisan darajar ƴa' mace ba Sam bai cancanta daya cigaba da rayuwa ba,'
ɗagowa baba alamu yayi yana ja da baya da baya idonsa jawur, jini na kwaranyowa daga bakinsa yana cewa "Dan Allah kada ka kashe ni ! Kabarni a haka naji jiki sosai, ina da ƴa'ƴa da mata in ka kashe ni zasu shiga wani hali.....' bai bari ya ƙarasa maganar ba, yakai masa wata irin mahangul6a da hanunsa nan take yasake fasa ihu,
"Karka kuskura ka sake buɗe wannan ƙazamin bakin naka da sunan zakayi mun bayani ! Bani da lokacin sauraron jawabin Ka, har kana da bakin da zakace mun kana da ƴa'ƴa da mata, don ubanka su yaran daka ɗauko donka lalata ma rayuwa daga sama suka faɗo? Ko su basu da dangi ne da zasuyi kuka in sun rasa su? Idan ka lalata masu rayuwa kana da tabbacin zasu ƙara numfashi ne ko baza suyi ba ? Ka yi tunanin hakan? ! idan wani ya lalata rayuwar ƴarka yaya zaka ji? Ka ƙiyasta yaya raɗaɗin yake azuciya............yana faɗin hakan yasa hannu ya rarumesa tare da wujijjiga shi ya sake buga kanshi ajikin bulo ɗin nan take kansa ya fashe jini ya soma kwaranya, ko shurawa baiyi ba nan take ya mutu a mace............
(Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar? Ka mutu kana aikata irin wannan mummunan zunubin batare da ka shiryu ba? Shin mai zaka ce ma Ubangiji? mutum baison lokacin mutuwarsa ba, shiyasa ake so koda yaushe mutun ya kansance cikin shiri kuma ya kasance yana aikata abun kirkiri, sam baba alamu baisan cewa yau wa'adinsa zai cika ba, Ga yarda ƙarshem shi takasance Ya Allah kasa muyi kyakkyawan ƙarshe, kuma ka kare mu daga aikata aikin dana sani 🙏😥
Chapter 40 · 0% Book details