← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 41

Sashe 29

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

yarda bazai faɗi ba, Tsayawa tayi tana faman sauke haki tare da sauke ajiyar zuciya, matsawa yayi tare da cire hannunsa ya gyara kwanciyarsa saman bedmattress ɗin sannan ya ɗan ware idonsa akan Sehrish dake atsaye, mamaki ne ya kamasa ganin ta tsaye dab da gadonsa me hakan ke nufi badai tazo bane don ta hanasa faɗuwa ba, ƙarfin halin ta yabashi mamaki shin ko ta ina zata iya ruƙoso daga faɗuwar da ya kusan yi? tabbas da ace sehrish takai hannunta da nufin ta dakatar dashi daga faɗowa daga saman gadon,ƙarshenta ya faɗa mata ajikinta ya danneta tagaza tashi don kuwa ko kusa sehrish bata da ƙarfin da zata iya taimakonsa daga faɗuwa,' Sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya sam tarasa gane ma kanta, ita dai kawai burinta karya faɗo ƙasa yaji mummunan rauni shiyasa tayi yunƙurin tarbosa, Kasalalliyar muryarsa ce ta ratsa ta da cewa"Sannu da ƙoƙari, amma kada kiyi attempting cewa zaki ruƙoni next time, if not jikinkin ki nei zai gaya maki," Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"kayi hakuri bazan ƙara ba," Shiru yayi tare da mayar da idonsa ya lumshe su, yana faman sauke ajiyar zuciya, ɗagowa ta danyi tare da kallonsa tace "dama......na kawo maka dinner ɗinka ne, yana a falo na ajiye," Kusan minti 5 da yin maganarta ta sannan yace"Shigomin da fruits tare da Coffee, su kawai nake buƙata," Juyawa tayi cikin sauri ta koma cikin falon hannu tasa ta ɗauki plate ɗin dake dauke da fruits ɗin ta shigar masa dashi saman front table ɗim gadonsa ta ajiye masa, sannan ta koma ta dauko masa hadaɗɗen Coffee din dake acikin Cup ta dawo ɗakin nasa a lokacin har ya tashi zaune ya sauko da ƙafafunsa ƙasa, a gefen plate ɗin ta ajiye masa sam yagaza buɗe idanunsa da alama ba ƙaramin bacci yake ji ba, sai faman cizon pink lips ɗinsa yake yi, Ita dai burinta ya buɗe idonsa yafara shan fruits ɗin kafin ta tafi, don batason ya kwanta bai ci komai ba acikinsa 😒 Muryarsa taji yace"What are u waiting for? Ko zaki ban abaki ne? ya faɗi a time din yaɗan ware idanunsa masu ɗauke da bacci, Cikin sauri sehrish tace "a'a sai Allah yakaimu, mu kwana lafiya," ta fadi tare da juyawa cikin sauri ta fuce daga ɗakin nasa sai da tafara tsayawa ta dauki food stuffs din dake acikin tray ɗin da ta ajiye masa sannan ta fuce dasu, a kitchen tasamu wurin ta zauna saman dining table ɗin ciki, buɗe kayan abincin tayi tazauna ta shaƙe plate tana ci, bayan ta kammala ta koma bedroom ɗinta sai da tafara yin sallar isha'e sannan tayi addu'ar yin bacci taja bargo ta lullube jikinta cikin wani irin yanayi na abunda yafaru tsakanin ta da SGR, ***************AUNTY BABBA********** Da kanta ta girka masu hosana da jahad lafiyayyen abinci ta kuma jera masu shi adining, su duka suka halarta suna ci jahad na kusa da uosana polyayin da Hafsat ke kusa da mommynta dama mai 4 seats ne, Duk sun kasa sakewa suci Abincin saboda fargabar da suke ji aransu, kwarama hussana tasamu tana shan kakkauran tea ɗin data haɗa mata tare da bread wanda yaji butter ajikinsa, ɗagowa Aunty babba tayi ta kalli jahad tare da cewa "My daughter me yake faruwa ne? Naga tun ɗazu sai fama juya cokali kike yi acikin plate, yakamata ki fara cin abincin ko saiya huce"? ta tambaya cikin nuna kulawa, murya na rawa jahad tace "babu komai Aunty zanci ne yanxu," Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa "kwara dai kici ta da zafin ta, saboda in ta huce baza tayi maki daɗin ci ba," Jahad ta amsa da toh sannan ta soma cin taiyar pasta din dake agabanta, Mayar da idonta tayi kan na hussana tace "Yawwa my daughter, ae ke na lura bakya wasa da abinci da alama, kamar ni kike, shiyasa gani nan kamar buhun masara sai uban auki," Jin abunda tace yasamu fashe wa da dariya su duka banda hafsat dake satar kallon mommyn nata, abun ɗaure mata kai yake ganin yadda lokaci guda Mommynta ta sakewa yaran aranta tana cewa "gaskiya Mommy ba ƙaramar ƙuruwa bace wurin iya tsara tuggu, ta iya shu'umanci Allah kaɗai yasan me take shirya wa, koma dai menene nidai ina nan ina zuba ido in gani......👀 Murmushi Aunty babba tasaki tana kallonsu ganin yarda tasanya su nishaɗi aranta tace "haka nake so don kutmar ubanku a hankali zan canza muku tunani har na cimma burina," a fili kuma ta washe baki tana cewa "ku hanzarta ku kammala ci dare yayi sosai yakamata ace yanzu kun kamma yi nisa a bacci, sannan jahad kada ki manta kafin ku kwanta ki tabbatar kin ba Hussana maganinta, Jahad ta amsa mata da "toh," Bayan sun kammala yin dinner ɗin nasu suka wuce bedroom din hafsat bayan hussana tasha maganinta sannan suka kwanta, bacci mai nauyi ya ɗauke su............. Kallon Hafsat aunty babba tayi a lokacin itama idonta nakan Mommyn nata, "tun ɗazu na lura da satar kallona da kike yi shiru kawai nayi," aunty babba ta fadi tana kallonta Hafsat tace "hmmmm mommy kenan ni so nake ki faɗamun abunda kike shiryawa game da twins ɗin nan yakamata na sani," Dariya aunty babba tayi kafin tace "bai da amfani koda kin sani hafsat ! ki ma daina tambayata domin kuwa bazaki ta6ajin mutuwar sarki abakina,!" Jinjina hafsat tayi tare da miƙewa daga kan dining ɗin tace "Shikenan Mommy kwarama ki ruƙe sirrinki, yarda in asiri ya tashi tonuwa ke kaɗai zakiji jiki ban dani, ni dae nayi nan," tana faɗin hakan ta wuce cikin bedroom ɗinta, Saman Sofa ta kwanta tare da jan bargo ta lullu6e jikinta, Shu'umin murmushi Aunty babba tasaki tare da cewa "Yanzu wasan ya soma, " 😳 Nikuma nace Allah yaba mai rabo SA'A ***********AFTER 1 WEEK********* BAYAN SATI ƊAYA Acikin waɗannan kwanakin Jahad da hussana ba ƙaramin kwanciyar hankali suka samu ba, sun samu ƴanci sosai acikin gidan jikinsu yayi kyau ba laifi sun ɗan murmure, gashi hafsat bata gajiya da ɗawainiya dasu har fita takeyi dasu yawan shaƙatawa, su fita shan ice cream ko kuma ziyarta gidan friends ɗinta, Aunty babba dae ta zuba ma sarautar Allah Ido burinta kawai Baba alamu ya diro Garin kaduna kafin Zuwan Omar, don tuni Baba Alamu yasanar da ita cewa suna kan hanya yau Litinin zasu sauka kaduna, 😳 A 6angaren Sehrish kuwa tana cikin farin ciki matuƙa saboda makaranta da zata fara zuwa, an riga da an kammala yi mata komai hatta Uniform ɗinta an kawo mata su kusan kala 3, ga sandals ɗinta masu kyan gaske, ga jibgegiyar school bag ɗinta da aka siya mata tare da textbooks na amfani da sauransu, abunda ya rage mata yanzu shine fara zuwa makarantar acikin satin nan, 😇 Tuni Marshal Omar yayi oder na haɗaɗdun furnitures made in dubai, kamfanin da yayi siyayyar kayan su da kansu, suka tsara mashi gidan wa'iyazubilla wurin kyau ba'a magana, komai sabo fal acikin gidan, kayan kitchen ne kayan ɗaki kayan falo komai fa wannan an zuba acikinsa ba abunda ya bari, bari in taƙaice muku zance hatta wannan kayan store na abinci yasa an jibge masu shi, duka freezer ɗin dake acikin gidan yasa an cike masu shi da Kayan marmari dana sha, komai fa Omar ya tanadar musu na jin daɗin Rayuwa, dama abunda ya hana shi zuwa kaduna kenan saboda yafi son saiya fara gyara masu gidan ya sanya musu komai na more rayuwa acikinsa sannan ya je yaɗauko su, kuɗi sosai Omar yaba Sehrish da azmee don suje yi musu siyayya, koda suka tambaye shi size dinsu na kayan da zasu siya masu gudun kar ayi kuskure, sai yace musu komi zasu siya irin na Sehrish saboda yana da tabbacin cewa tsayinsu da komai na jikinsu bazai wuce na SEHRISH ɗin ba, da sukayi masu siyayyar kaya masu yawan gaske kamar irin na sehrish amma nasu yafi yawa saboda su biyu ne, ƙarshe sai dai motar kamfanin da su kayi siyayar ta kawo musu kayan har gidan Abusufyan saboda motar junaid bazata iya kwashe su duka ba, saboda shine ke ɗawainiya dasu duk in da zasu fita, finally dae komai ya kammalu,👍
Chapter 29 · 0% Book details