← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 41

Sashe 5

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kwance suke acikin store ɗin su biyu abunsu, kamar yadda Jahad ta saba yi musu dabara, na jera masu jarkoki su koma kamar single bed sai su kwanta suna facing ɗin junansu sam bacci yagaza ɗaukarsu zullumin su mai zai biyo ba? Wata alƙibla rayuwarsu zata fuskanta yanzu?
"Jahad idan Aunty hafsat ta zubar damu ina kuma zamu dosa"? Hosana ta tambaya tana kallon jahad wadda ta zuba mata ido,
Cikin sanyin murya tace "Nima kaina bansani ba hosana, ina tsoran hakan," ta faÉ—i zuciya a karye
Hosana tace "Dama Allah ya É—auke mu yakai mu duniyar sama ko? ko duniyar taurari inda ba mutane muyi rayuwarmu mu kaÉ—ai tare da yaya Omar tunda kowa baison mu shi kaÉ—ae ke son mu ko?
Wannan maganar ta hosana tasa jahad fashe wa da dariya daga kwancen da suke ta rinƙa 6a66aka dariya kaman kamar me,
Hosana ta É—an 6ata fuska don ita bada wasa tayi maganar ba,
Daker jahad ta jinkirta da dariyar tace "Sorry hosana dole nayi dariya mana, wa kika ta6a ganin an É—auke daga nan an kaisa sama ?
Shiru tayi tana zumbura baki, jahad taci gaba da cewa "sannan kince tare da yaya Omar kaɗai zamu tafi saboda yana son mu, Shin kin manta da Sehrish ne"? Ita kuma fa? akwai wanda yayi mana wahala ne kamarta? sehrish tana son mu fiye da kowa na duniyar nan, saboda mu tashiga duk wani hali da take ciki ayanzu duk da bansan yaya rayuwarta take ba...............wani irin kuka ne yaci ƙarfin jahad har takasa ƙarasa maganar da take yi,
Nan take jikin hosana yayi mugun sanyi tunawa da Sehrish ƴar uwarsu mai tsananin son su da ƙaunarsu, tuni itama idonta sun cicciko da hawaye murya na rawa tace "Ya Allah hada sehrish za'a ɗauke mu akai mu duniyar Taurari.....'
dakatawa da magana tayi ganin Jahad dake kuka ta fashe da dariya, wato tayi tazarce daga kukan da take Zuwa dariya ba don komai ba sai don jin abunda Hosana ke cewa, share hawayenta tashiga yi tana faɗin "Hosana wasan ya isa haka, muyi magana ta hankali, yanzu yaya za'ayi yaya Omar yasan halin da muke ciki kafin Hafsat da Momynta su sa azubar damu yakamata muyi tunanin hakan in ba haka ba zamu shiga wani mugun hannun ne ko mu ƙare rayuwarmu adaji..............' jinkirtawa tayi da maganar tana sauraron shawara daga wurin hosana,
"To ya zamuyi mu sanar mishi jahad? Bayan kullum waccen matar mai kama da samudawa mai kumatun alkubus tana tsare mu da ido duk in yazo tana hanamu kwakkwaran motsi,"
Shiru jahad tayi tabbas dole su nemi mafita in ba haka ba, zasu fuskanci tashin hankali
Can tayi wani dogon tunani tace "Hosana mai zai hana, mu samu paper da biro sai mu rubuta mishi, in yazo sai ki lalla6a kisan yarda zakiyi ki tura masa a aljihunsa? Ko da rungumesa ne sai kiyi kamar yarda kikayi a asibitin nan kin tuna"?
Murmushi hosana tasaki anzo inda keyi mata ƙaiƙayi kallon jahad tayi tace "Shawara mai kyau, amma taya zamu rubuta mishi to? Bamu da paper ba biro jahad,"
Shiru jahad tayi kafin tace "Akwai !!! Na tuna acikin wannan É—akin da Momyn hafsat takaimu acikin wannan Æ´ar lokar naga Memo da biro,"
Cike da farin ciki hosana tace "dama ƙopa a buɗe take, yau ta manta bata rufe mu ba, jahad ki lalla6a ki ɗauko ki rubuta masa,"
Miƙewa jahad tayi tana faɗin "Zan fita dan Allah hosana karki biyo ni, nasan halin ki, in kika ja asirin mu ya tonu kashin mu ya bushe mu duka,"
Murmushi hosana tasaki tana cewa "sai dai in baki daÉ—e ba, kinsan ina jin tsoro fa nikaÉ—ae anan,"
"Karki damu yanzu zan dawo,"
"To shikenan," hosana ta bata amsa,
Ficewa Jahad tayi cikin sanÉ—a take tafiya babu kowa wayam sai hasken daya gauraye ko'ina,
Wuce wa ɗakin tayi a hankali ta tura ƙopa tashige cikin hanzari ta nufi drawer ta zaro gidan farko ajikinta, anan taga memo ɗin da biron data gani,
Fiddo su tayi jiki na rawa ta aza memon asaman drawer ɗin dayake ƙaramace, daga zukunne jahad ta soma bude papers ɗin sannan ta aza biro ta soma rubutu kamar haka
_ya Omar naji ma inaso na faÉ—a maka halin da muke ciki, wlh bamu jin daÉ—in zama agidan nan, saboda basu son mu, uban aiki suke samu har bugun mu suke yi, dan Allah ya omar in kaga wannan takardar ka taimaki rayuwarmu kamar yarda kayi niya ka tafi damu inda kake rayuwa_
Kamar daga sama Jahad taji ance "Sannu da Ƙoƙari"!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!
Jin wannan maganar a bayanta yasa jahad dakatawa da rubutun da take yi, hankali a matuƙar tashe idonta sun firfirto azare, jikinta ya soma wata irin kerma, Tuni Zufa ta soma gangarowa daga fuskarta da jikinta don bala'e hatta paper ɗin da take rubutun asamanta ta jiƙe sharkaf da gumin da take fitarwa 😳😳😳

*SHIN WACECE WANNAN*‼⁉❓❓❓

Mgnr payment 300 ne amun magana direct *08103884440*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🔥The Father Of Soldiers🔥*

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤‍🔥💞💘💖

*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*

~💋BOSSLADY💋~

*Abban Sojoji part 2*

*EPISODE 3-4*

Sam jahad ta gaza yin kwakkwaran motsi saboda ta riga ta gane muryar wacece.......
Idasa shigowa tayi da wannan takun nata, jikinta na sanye da sleeping dress red colour masu zanen flowers ajikinsu, abunka ga fara ta fito 6au acikinsu, kanta ko mayafi babu ba kowa bace wannan face AUNTY BABBA,
Lokacin da ta isa inda jahad take, hannu tasa ta fisge takardar da take rubutawa, ta ɗago da ita tana karanta wa, zaro ido tayi hankali tashe tace "Keeeeee! Don ubanki ni zaki tonawa asiri!? Wato Omar kike rubutawa wasiƙa don ki faɗa mashi abunda muke yi maku ! Wlh kin shiga uku, bazan ƙyale ki ba sai kin yabawa aya zaƙinta!!!!
Chapter 5 · 0% Book details