← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 41

Sashe 10

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babu wasa a fuskar shi yayi maganar, shiru su kayi don baza suyi mashi musu ba, Abban nasu yaci gaba da cewa "Yusuf kai zaka biya kuɗin siyayyar kayan sawanta, Jahan kuma shi zai ɗauki nauyin kayan ado na mata da za'a siya mata, sannan Ayaan shi kuma zai ɗauki nauyin na gyaran jiki hada takalma da bags ɗin da za'a siya mata ina fata duk kunji," sam takaici ya hana twins yin magana bawai kuɗin bane damuwarsu ba sam basu da matsalar kuɗi saboda bada albashinsu suka dogara ba, Mahaifiyarsu duk ƙarshen wata tana tura masu makudan kuɗi dollars wannan ba tare da sanin Abbansu ba ko Babban yayansu ba, haushin su yarinyar da aka ƙaƙaba musu wadda basu san daga ina aka tsinto ta ba, gashi kuma har ana ɗaura musu responsibilities ɗinta,

"Naji kunyi shiru"? Abbansu ya tambaya yana kallo su,
Kanal yusif yace "Atm É—in yana a cikin side drawer É—ina, junaid yaje ya É—auko in zasu tafi,"
  Jinjina kai Abbansu yayi tare da cewa "Haka nake son ji ku fa"?
  har suna haɗa baki wurin cewa "akwai kuɗi cash a ɗakin mu junaid yaje ya ɗibi yarda zai ishe su,in kuma Atm suke so shima yana anan saman mirror muka barshi...." suna magana suna yatsina fuska irin an musu dolen nan,

Kanal yusif yace "A'a Abba ba sai sun bada nasu ba, kawai suyi using da Atm É—ina zasu ishe su har ma su rage," acewar kanal yusif,
   Abban su yace "a'a ni nafison su sauke nauyin dake akansu na ƙanwarsu yakamata tun yanzu su son yadda zasu ɗauki ɗawainiyar mace kafin Allah yasa lokacin auransu yazo,"
. atare suka haÉ—a baki wurin cewa"Aure kuma Abba,"
  "Eh mana" ya amsa musu,
Kallon Ayaan jahan yayi tare da cewa "tashi mu tafi lokacin aiki yayi " miƙewa Ayaan yayi yana cirar tissue yace "Abba mu mun wuce,"
  Murmushi Abbansu ya saki tare da cewa "adawo lafiya, aure dae ba fashi in lokacinsa yayi mutun ko bai so saina ɗaura masa in yaso ya haɗiyi zuciya ya mutu, zan zauna in ta zuba muku ido ne,"
   fashewa da dariya junaid yayi bashi kadae bama hada su azmee da sehrish, kanal yusif dae murmushi kawai yayi,

Na wani lokaci kowa yabar dining É—in cikin zumuÉ—i sehrish ta wuce don ta shirya zasu tafi Shopping mall É—oki har ba'ayi, shima junaid bedroom É—insa ya wuce don ya kimtsa yau zasu yi fita ta musamman da sehrish don ya tsara har ice cream sai sunje sha, haka itama azmee kimtsawar take yi don su fice,

Haroon sam yagaza fitowa saboda kunyar haɗuwarsa da sehrish baisan martanin da zata yi mashi ba, dama jiya ta yarda masa magana a cikin toilet ina ga yau da tasamu ƴanci Allah kaɗai yasan Zagin da zaisha, ga yunwa yana ji amma sai faman zarya yake aransa yana faɗin "Ke ma bazan ƙyale ki ba Yarinya saina ƙasƙantar dake kuma bazan fasa abunda nayi niyya ba akan Ki,*YANZU WASAN YA FARA* 🙆

Fitowa azmee tayi jikinta na sanye da doguwar riga ta atampha ta kashe ɗaurin kallabi, sai ƙamshi take cikin hanzari ta wuce kitchen saboda tunawa da Marshal Omar wanda bai fito yin breakfast ba kuma ba'a kai masa ba, shaf shaf ta shirya masa a tray ta wuce part ɗinsa ta shiga da Sallama babu kowa a falonsa hakan na nufin koma bacci bai tashi ba, ajiye masa tayi asaman ƙayataccen table ɗinsa sannan ta fuce,

Tana saukowa down stairs taci karo da haroon wanda ke tafiya cikin sanÉ—a zai shige kitchen wai don karya ci karo da Sehrish
  girgiza kai azmee tayi aranta tace "Shi ko haroon ko lafiya yake faman tafiya cikin sanɗa haka kamar mara gaskiya, Ni wlh nama manta dashi ashe yana nan,'
  Gyaran murya tayi tare da cewa "barka da fitowa mlm haroon," firgit yayi tare da juyowa ya kalle ta, ajiyar zuciya yasaki ganin azmee ce "Aunty azmee barka dae fatan an tashi lafiya, shine aka manta dani ina ta fama da yunwa yanzu da ban fito ba da shikenan sai dae yunwa ta kashe ni ko? Ya tambaya hada ruƙe qugu dama ransa a 6ace yake.........
  Azmee tace "Kayi haƙuri wlh ni sam na manta ban lura da baka fito ba ba,"
  ta6e baki yayi tare da cewa "koda yake dama ae ni ba'a sona na lura, bama kallon mutun ake mun ba acikin gidan nan kowa ya raina ni,"

Murmushi azmee tasaki tana kallonsa tace "kadaina cewa haka bana jin daÉ—i, koda kowa zai guje ka amma kasan ina tare da kai ko? Ka ta6a ganin inda UWA ta Guji ÆŠANTA?" tayi maganar ne don ta kwantar masa da hankali ganin ya É—an fusata,
  Sakin fuska haroon yayi sannan yace "Shikenan nadaina aunty azmee tunda baki so, yanzu dai a haɗa mun breakfast ɗina wlh yunwa nake ji har wani jiri nake gani,
   Wuce sa azmee tayi tana cewa "a ina za'a kaima abincin anan ko a ɗakin ka," cikin sauri yace "Ki haɗamun kawai natafi da abuna ɗakina naci,Zai fiye mun kwanciyar hankali na" 
  Kitchen ɗin tashiga ta haɗa masa a tray sannan ta miƙa masa jikinsa na rawa ya kar6a ya wuce ɗakinsa,
  Gefen gadonsa ya zuna hannunsa har kerma yake yi yana cusa abincin abakinsa, kamar daga sama yaga sehrish ta bayyana agabansa jikinta sanye da Kayan Sadaukai na Yaƙi, hannunta ruƙe da Zungureriyar wuƙa kanta na ɗauke da Kambun Sarauta, hankali atashe haroon ya fesar da donuts ɗin daya cunkusa abakinsa yana kallonta cike da tashin hankali, fashewa da dariya sehrish tayi tare da cewa "Kai Haroon! Ƙaryarka taƙare ! ka jima kana ƙuntatamun gashi yanzu Allah ya ɗaukakani, babu wata sauran barazana daga gare ka ta ƙare, nazo ne don na ɗauki fansa akan ka, yanzun nan zan fille kanka da wannan wuƙar ta hannu na,
  Da ƙarfi sehrish ta ɗaga wuƙar zata fille ma haroon kai, aikuwa a firgice ya miƙe tsaye yana dafe saitin zuciyarshi a tsorace

Lokaci guda Sehrish ta 6ace masa 6aaat hakan na nufin ba ita bace idonsa ne ke masa gizau,amma shi tabbas ita yagani kodai yarinyar Aljana ce ? Ya tambayi kansa,.wannan ba kowa bace face Hafsat Bature Aljanar sehrish 👿
Koma wa yayi ya zauna yana ci gaba da cin breakfast ɗinsa anatse, yayin da ransa ke saƙa mashi abubuwa da dama game da mummunan ƙudirinsa

__________    💪    ______________

OMAR a hankali ya soma buɗe idanunsa bakinsa na ambaton addu'ar tashi daga bacci, yayin da zuciyarsa ke cike fal da son ganin Tagwayensa, tun da asuba daya sha maganin mura bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi sai yanzu Allah yayi mashi ikon Farkawa daga bacci, a hankali yasa hannun sa ya janye blanket ɗin daya lullu6a dashi jikinsa na sanye da Night dress riga ce dai dai guiwa mara nauyi, fararen idanuwansa yafara kaiwa ya kalli agogon dake manne jikin bango ƙarfe 12 na safe yayi mamakin yadda lokaci ke gudu har haka, ko don yayi overdose na maganin muran daya sha ne yasa shi yin dogon bacci har haka,
  Cikin sauri ya yunƙura ya miƙe direct toilet ya wuce , brush yafara yi yana tsaye agaban wash basin amma idonsa Fuskar Jahad da Hosana take hasko masa ta cikin mirro ɗin gabansa, shaf shaf yayo wanka ya fito jikinsa sanye da Bathrobe(rigar wanka) fara, wadda ta tsaya masa adai-dai guiwarsa, Marshal Omar kenan Son kowa ƙin wadda tarasa 😉
  kai tsaye wuce wa yayi ya ɗauki wayarsa dake a saman gadonsa, sak irin ta sgr ce, Company ɗaya ce waya ce ta musamman domin Manyan jami'an sojoji irinsu kirar Companyn Iphone Ce, hamshaƙiyar waya haɗaɗɗiyar gaske wadda kuɗinta sun haura 30millions, ba kuɗinta bane abun mamaki ba a'a amfaninta shine abun dubawa, ƴar bala'en wayace bakowa ma zai iya Controlling ɗinta ba sai mamallakinta.
  dannata ya soma yi Contact ɗinsa ya shiga kai tsaye numbar aunty BABBA ya laluba, ya buga mata Calling ta shiga ringing, burinsa tayi picking yasanar da ita cewa Zai shigo kaduna don ya duba su Hosana da Jahad, almost 3 times ba'a ɗaga kiran ba, domin kuwa wayar tabar ta agida, canza ra'ayi yayi ya dannawa Wayar Hafsat kira,

Suna a asibitin nan zaune saman waiting seats, bacci duk ya kwashe su daga zaune don daren jiya ba wanda ya runtsa sai da sassafe wurin ƙarfe 10 suka samu baccin wahala shima saboda likita yasanar dasu cewa Yarinyar da ranta bata mutu ba, farkawa ne kawai batayi ba doguwar suma tayi, shine suka ɗan samu natsuwa suka baje suna bacci kamar wasu shanaye ga uwar yunwa na cinsu, kiran Omar ne yashigo da ƙarfin gaske a wayr hafsat dake acikin purse ɗinta data aza saman cinyarta, a firgice suka farka su duka wuri wuri da ido, cikin hanzari hafsat ta zura hannunta cikin purse ɗinta ta duba me kira sunan MARSHAL OMAR ne ya bayyana, dafe ƙirjin tayi hankali atashe tace "MUNSHI GA UKU ! MOMMY YA OMAR NE KE KIRA"😳

   Mu haɗu ranar monday Insha Allah🙏

Kar amanta da paymemt wanda suka shirya sumin magana 08103884440, 300 ne VIP kuma 700 ga wanda basa ra'ayi a grp*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🔥The Father Of Soldiers🔥*

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ❤‍🔥💞💘💖

*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*

~💋BOSSLADY💋~

*Abban Sojoji part 2*

*EPISODE 7-8*

*AYAAN* arab name ne for boys means God's Gift (kyautar Allah) ❤️
Chapter 10 · 0% Book details